AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Ta bangaran momcy kuwa itama ta dage tana mika kukanta ga Allah akan lamarin diyar tata duk batasan halin da ake ciki ba amma tasan sadeeq baya son khairat kawai biyayya xaiyi.

Ta bangaran sadeeq kuwa bashi da wata damuwa shirye shiryan sa kawai yakeyi yana nunawa su dady cewar tana mutuwar son khairat domin bayaso asamu matsala idan ya tashi gabatar da shirin sa.

Anyi kamu sosai lrin namasu hannu da shuni inda amarya tayi matukar kyau aka cashe sosai Sannan amarya tasha nasiha mai ratsa jiki awajan kamun nata daya samu halartar manya malamai mata.

Lokacin da kowa ya watse daki khairat tashiga kawai ta fashe da kuka kamar ranta xai fita domin tasan kwana 2 ya rage tashiga wata sabuwar rayuwa mai wuyar fassarawa domin batasan mai xataje ta tadda a gidan masoyin nata ba wanda ita takasance abar kyama a gareshi.

Rahama ce ta shigo dakin da tadda aunty nata nata kuka, karasawa kusa da ita tayi tace

Aunty waya dakeki kikeyin kuka?

Sai a lokacin tasan da shigowar rahama dakin tayi saurin goge hawayenta tana fadin

Bb komai auta kinji gashin idon danasa ne ya shige min ido yake xafi amma karki fadawa momcy tunda kinga bataso amma naje na sanya.

Toh aunty baxan fada mata ba amma kema kicireshi toh tunda yana saki kuka.

Shikenan tashi kije autar mom yanxu xan cire kinji.

Tashi tayi ta fita itakuma khairat tashiga toilet ta gyara face dinta domin bataso Aisha da maryam su fahimci tayi kuka sbd yanxu sun dawo gidan da xama xuwa lokacin gama bikin.

Washe garin ne yakama ranar party tun la’asar aka farawa amarya kwalliya saida suka dau sama da 2hrs ana kwalliya saida khairat tayi kamar ba itaba duk wanda yaganta saiya yaba domin khairat badai kyau ba ita kanta data kalli kanta a mudubi godiya kawai take mikawa ga ubangiji domin it’s kanta tasan ita kyakkyawa ce.

Iya kodawa maryam da Aisha sun kodata domin suma ba’a barsu a bayaba kaya iri daya suka sanya da maryam da Aisha sai rahama da sukayi iri daya da ita Sannan suka Hana kowa tafiya da ita tana makale dasu.

Saida kowa ya tafi Sannan sadeeq ya turo da mota a dauko su khairat, momcy na ganinsu tace masha Allah gsky diyata kinyi kyau murmushi kawai tayi sai rahama datace

Mom nifa bakice nayi kyauba

Ah ai dukanku kunyi kyau auta kuje ana jiranku na tsai daku.

Suna isa wajan su maryam suka fito da khairat suka kaita wajan xamanta aka fara gabatar da abinda ya kaisu.

Saida akadau wajan 30mins Sannan sadeeq da abokinsa Abdul suka iso tunda yaxo wajan yake kallon khairat aransa yana cewa

Dama haka yarinyar nan takeda kyau gsky Allah yayi halitta awajannan.

Tana kula da yadda yake satar kallon ta murmushi kawai tayi aranta tace koh bb komai yau nayi abunda ya burgeka.

Sai wajan 11:00 suka dawo gida duk sun gaji sallah kawai sukayi sukaci abinci suka kwanta domin gobe su tashi da wuri domin shirin daurin aure.

 

 

*More comments More typing……….domin ta comments dinku xan gane amsuwar book din gareku????????‍♀*

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:26 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

*Page 6*

 

 

Washe gare kowane bangare suka tashi da shirye shirye daurin aure inda yan uwan momcy dake gombe suma sun samu damar isowa.

Hajiyar su maryam ma tun safe ta shigo ake hidimar da ita.

Amarya kuwa da manyan aminan nata ansha kwalliya kamar basuba can sasan dady momcy ta kaisu saboda nan jama’a sunyi yawa domin sugama shirye shiryensu.

Karfe 11:00am dai dai Dubin al’umma suka shaida auran *ABUBAKAR MUKTHAR (sadeeq) DA KHADEEJH KABEER(khairat)*
Daurin auren daya samu halartar manyan mutane daga wurare da dama.

Khairat najiyo gudar mutane awaje sun nufo sashen dady taji gabanta yafar faduwa hawaye ne kawai suka fara bin kuncinta Aisha ce ta kula da hakan tayi hanxarin sanya hannu tana goge mata tana fadin sis karki bani kunya kinga mutane sun fara tahowa nan ki daure ki hadiye duk abinda kikeji.

Toh kawai tace ta sanya hannu tafara goge hawayen nata.

Kanwar momcy ce dasukaxo daga gombe mai suna hajara ta shigo tana fadin ina amaryar take musa mata Albarka?

Boye fuskata tafara yi hajara tace Ashe dai diyar tawa akwai kunya ina fatan dai kunci abinci?

Aisha ce ta bata amsa da basuci ba, tace bari tasa akawo musu.

Karfe 5:00 dai aka mika Aisha wajan dadi yayi mata nasiha sosai mai ratsa xuciya tunda yafara khairat ke kuka bb kakkautawa shi kanshi dady daurewa yayi ji yake kamar shima yayi kukan saboda yana matukar son khairat.

Ana fito da ita daga gidan dady aka wuce da ita bangaran momcy itama nasiha tayi mata sosai harda hawaye da kyar hajara ta lallashesu sukayi shiru Sannan hajara tace ya kamata a fara kaita wajan su hajiya xainab (mahaifiyar sadeeq) dakuma dady saboda suma iyaye ne.

Haka kuwa akayi saida aka fara kaita nan suka yimata nasiha Sannan aka wuce da ita gidan ta dake nasarawa.

A hankali kowa ya watse daga maryam sai Aisha suna xaune bb wanda ke iya furta komai a tsakaninsu kusan 30mins kenan duna xaune haka sukaji alamun tsayiwar motar su sadeeq bayan kamar minti 5 sukaji motsinsu a parlourn dake kasa.

Maryam ce tafara tashi tadau Jakarta da mayafinta sai Aisha itama ta tashi bude idanu khairat tayi tace

Me kuke nufi?

Aisha ce tayi kokarin bata amsa tafiya xamuyi mana

Haba sis karkuyimin haka dan Allah kuxauna karku tafi kunji

Hawaye kawai maryam taji yafara xubo mata tayi saurin juyawa tana fadin sis mun wuce mudai sai da safe xamu leko miki takarasa ficewa tana xubarda hawaye domin sun shaku da khairat sosai.

Kuka tafarayi tana fadin sis ki tsaidata dan Allah karku tafi khairat tafiya taxama dole kiyi hkr kinji da safe xamu dawo da kyar ta lallabata tasamu ta sakko.

A parlour ta riske Aisha da sadeeq da abokinsa Abdul suna sallama tare suka fita da Abdul xai saukesu a gida.

Suna fita sadeeq ya rufe ko ina na gidan ya nufi steps din……..

 

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:26 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

 

*Page 7*

 

 

Yana hawa saman koh kofar dakin khairat bai kallaba ya wuce dakinsa yasaka key ya rufe yanufi toilet.

Tanajin wucewarsa da rufe kofar takuma fashewa da wani sabon kukan tana nadamar auran sadeeq tana ayyana abubuwa da dama a ranta.

Yanxu da ace wanda yakesonta ta aura da yanxu yanan yanata rawar kafa akanta amma gashi wai itace aka kawota gidan miji a daransu na farko ko waiwayata baiyiba kuka taci gaba dayi bb kakkautawa saida taji kanta kamar xai fashe Sannan ta tashi tajawo wayarta ta duba agogo karfe 12:30 abin yabata mamaki shabi yanxu harda rabi gsky ta dade a xaune awajan, bb shiri ta sauko daga kan gadon taje ta cire kayanta ta nufi toilet wanka tayi sannan tai alwala.

Tana fitowa taje ta daukarfe guwar riga ta sanya ta sanya hijab ko mai bata shafaba ta shin fida dadduma tafara sallah.

Ita kanta batasan adadin raka’a nawa tayiba ta xauna tana hawaye tana mika kukan ra ga Allah ahaka har bacci ya kwasheta a kan daddumar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button