AURAN WATA DAYA

Karar bude kofar sadeeq xai tafi masallaci ne ya tasheta ta bude idonta taji ana kiraye kirayen sallah mikewa tayi tana salati tanufi toilet tayi alwala sannan tayi sallah tana laximi taji shigowarsa ya wuce dakinsa hawaye takumji sunbiyo fuskarta ta sanya hannunta ta goge.
Tana kammalawa ta tashi ta koma gadon ta kita bata jimaba bacci ya dauketa.
Misalin karfe 10:00 dai dai ta farka tana salati dataga rana ta hasketa mikewa tayi ta nufi toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin atamfar ta wacce akayiwa dikin riga da xani ta daura dan kwali batayi wani kwalliyaba powder kawai ta shafa sai white lipsticks ta dubu madubi taga tayi kyau sosai domin khairat irin kyawawan nan ne ga diri gashi Allah yabata gashi domin tabiyo mahaifiyar tane wato Fulani.
Idonta ta kalla taga sun sauya alamar tasha kuka daran jiya kwalli ta dauka ta sanya ta sauko parlour n kasa.
Yana xaune akan kujera ya lumshe idanunsa amma ba bacci yakeba ga TV ya kunna amma kuma ba kallo yakeba alamun tafiya yaji ya bude idanunsa a hankali yana ganinta yayi saurin maida kansa gefe.
Ras taji gabanta ya fadi datayi taxali dashi a parlour domin batayi tunanin yana gidan bama, karasawa tayi kusa da shi ta tsugunna tace
Yaya ina kwana?
Sai da yayi kamar baixai amsaba sannan ya bude idanunsa ya xuba mata ido tayi saurin kauda kanta sannan yace
Lpy qalau
Tashi tayi ta nufi inda take tunanin nanne kitchen.
Ina xaki ya fada yanabin inda ta nufa da idanu?
Kitchen xan shiga nayimana breakfast
Kallonta yayi up nd down yace ni bana bukata kawai ki dafa ke kadai.
Toh kawai tace ta wuce abinta.
Tea ta fara tafasawa sannan ta soya kwai ta dauki bride data gani acikin kitchen din ta fito parlourn da nufin komawa dakinta taci acan.
Ina xaki taji ya fada amma ko kallonta baiyiba?
Xanje daki naci abinci ne ta fada kamar xatayi kuka
Tsaki kawai yayi yace dawo nan kici inaso xamuyi magana.
Dawowa tayi ta xauna tana goge hawayen daya fara xubo mata.
Tsaki yakuma yi yace aikin banxa ko mai mutum xai da raguwar macema oho daga magana sai kuka wai ita yar shagwaba.
Ko kallonsa batayba ta cigaba da kallon kasa kawai.
Au baxakici abin cin ba saikin batamin lokaci ina jiranki.
Bb musu tasanya hannu tafara ci tana kammalawa ta miki taje kitchen ta wanke kayan ta maidasu ma’ajiyarsu sannan tadawo parlour ta xauna.
Sai da takai kusan 15mins sannan yace khairat
Na’am race tana kallon kasa
Cigaba da magana kawai yayi batareda y kalleta ba
Inaso ki sani nan gudan ba gidan xama bane awajanki inaso ki fara kirgawa daga yau kwanakinki xasu fara kwana 30 ne tsakanina dake wanda xamu xauna a inuwa daya.
Kuma inaso ki sani banason raini kuma muddin kikayi wani Abu wanda vaiminba a kwanakin daxakiyi tabbas saina hukuntaki, sannan kisani ni ban dora miki nauyina ko guda daya a kankiba ke dai dai da girkima kiringa yin kayanki ke daya bana bukata na yafe.
Toh kawai tace masa tana kuma sauraronsa
Hmmm saura kuma kaikayin bakinki ya kaiki fadawa wani irin xamanda muke a gidan nan tabbas ranar saina gasaki acikin gudannan.
Daga haka bai kuma cewa komai ba har xuwa wani lokacin itakuma har lokacin bata tashiba tunda bai bata ixini ba.
Kitashi kibani waje kinwani xauna kin kafeni da ido ya fada watsa mata harara.
Mikewa tayi da sauri tanufi dakinta kai tsaye…..
*More comments more typing????????*
*Neenat saif????????*
[12/18, 7:27 PM] +234 701 918 7780: ????????????????????????????????????????????????????????????????
*AURAN WATA DAYA*
????????????????????????????????????????????????????????????????
*Written by neenat saif????????????????????????????????*
*Dedicated to my blood sis Aisha????*
*Page 8*
Tana shiga dskin tarufe kofa ta fada gado ta fashe da matsa naicin kuka tana fadin
Ya ilahi me nayiwa wannan bawan naka da baya kaunata?
Ya Allah ka sassauta min yanda nakejinsa a xuciyata
Ya Allah kasan ni mai rauni ce ina rokonka ka bani hkr da juriyar da xan jure dabi’ar wannan bawan naka ya Allah nasan kai ka sanyamin soyayyar wannan bawa naka Allah ka sassauta min abinda nakeji????
Wani sabon kukan takuma fashewa dashi kamar ranta xai fita.
Yaxo giftawa ta kofar dakinta yaji alamun sautin kuka, yanaji tasan abinda yayimata ne yasanya ta kuka tabbas yasan cewar bai kyauta mataba ko babu komai taci darajar soyayyar da takemasa.
Harya taba kofar da niyyar shiga komai yatuna kuma sai kawai yayi tsaki ya wuce dakinsa ya kwanta yanata tunani.
Tana xaune har xuwa wani lokaci banda kuka bb abinda takeyi wayarta ce ta fara ruri
Dauka tayi ta duba taga momcy ce ke kira saida ta tsaya ta sai saita kanta domin bataso kwananta daya a gida mom tafara fahimtar cewar akwai matsala.
Saida wayar ta katse wani kiran ya shigo sannan ta amsa hadi da sallama.
Sun gaisa da momcy ta tambaye ta bb wata Marsala a gidan
Bb komai momcy tabata amsa tana murmushi.
Anan momcy ta sanar mata su maryam suna hanya sun kirata bata shigaba sai yanxu mom din ta sameta.
Shikenan toh mom sai sun iso
Yawwa khairat sai anjima amma ki ringa hakuri da duk wani Abu daxaki fuskanta domin shi aure dan hakuri ne kinji.
Toh bb damuwa mom xanyi kokarin yin hakan ki gaishemin da dady anjima xan kirashi.
Sunayin sallama ta tashi ta shiga toilet ta wanke face dinta tadan shafa powder ta sauko parlourn kasa ta xauna.
Bata jima da xama ba taji ana taba belt din kofar tashi tayi ta bude kofar rahama ce a gaba ta taho da gudu ta rungume ta.
Dau karta tayi tana fadin auta nayi missing naku sosai.
Ku shigo naga kuntsaya anan khairat ta fada tana kollon su Aisha dasu tsaya kawai suna kollonta
Shigowa sukayi suka xaxxauna khairat na fadin shine baku bari sageer ya biyoku ba?
Aisha ce tace wlh munce yaxo mu tafi momcy tace a’a aishi namiji ne kawai ya xauna a gida.
Ayya amma banji dadiba khairat ta fada tana mikewa ta nufi kitchen.
Jallof din taliya tafara kokarin dorawa maryam ta shigo tana fadin sis me xakiyi a kitchen kuma?
Wlh girki xan dora mana ta bata amsa tana greeting din kayan miya.
Ayya bashshi kawai na dora mana tunda naga kamar taliya xakiyi ai?
Eh ita xanyi domin itace xatayi sauki.
Toh kawo na karasa hada kayan miyan owk gashi ta mika mata tafara kokarin tsai da sanwa.
Suna kammalawa khairat ta xuba ta mikawa maryam tace mika mana parlour barina xubawa rahama nata.
Harta juya xata tafi tadawo tace banga kin xubawa mai gidanba.
Hawaye ne kawai suka fara xubo mata maryam ta kalleta race
Uhm na fahimta share hawayen naki karki bari Aisha ta fahimci komai xata iya fadawa hajiyar su daga haka dady xai sane share hawayen kawai ki fito muci abincin anjima xamuyi magana.
Toh kawai tace taci gaba da abinda takeyi.
Suna kammalawa Aisha tashiga ta wanke kayan da aka bata suka xauna suka fara fira.
Lokacin sallah nayi suka tashi suka yi sallah Aisha ce tace sis wai yaya baya nan ne?
Yanan bacci ya koma tabata amsa
Owk shiyasa najishi shuru……. bata gama rufe bakinta ba tajiyoshi yana saukowa daga steps din.
Murmushi yake yana fadin Aisha yaushe kukaxo gidan?
Wlh tun daxu mukaxo kanata bacci
Murmushi yayi ya matsa kusada khairat yanawa rahama wasa
Sai a lokacin maryam ta gaisheshi itama Aisha haka itako khairat kasa kallonsa ma tayi
Cikin sakin fuska ya amsa musu ya dubi inda khairat take yace