AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Toh madam ni xan fita amma ba jimawa xanyi ba

Da mamaki take kallonsa wato shidai bayaso kowa yasan abinda ke tsakaninsu kenan.

Murmushi tayi tace toh yaya adawo lpy

Ameen yace ya juya ya kalli su maryam yace toh ni dai nayi nan inkun koma ku gaidamin mutanan gidan gobe insha Allah xan shigo

Aisha ce ta iya cewa toh yaya Allah ya kaimu

Ameen ya fada sannan ya fice abinsa

Sai wajan karfe 5:00 su maryam suka fara shirin komawa gida

Yanxu maimakon kutsaya inya dawo saiku tafi tunda kunga ni kadai xaku bari a gidan khairat ta fada tana yiwa rahama rolling mayafin kanta.

Ki hkr wata rana xamu dawo tunda kinga yanxu inna koma gida xan shirya na tafi nabar hajiya ita kadai a gida maryam ta fada

Toh shikenan Allah ya kaimu

Har sun shiga mota dayake a mortar Aisha sukaxo maryam ta fito tana fadin nayi mantuwa.

Karasowa tayi inda khairat ke tasaye a gurguje tace anjima xamuyi waya dake banaso Aisha tasan abinda ake cikine shiyasa kikaga banyi miki maganaba amma jima ina komawa xamuyi waya

Toh shikenan ki gaida min hajiya kinji

Toh xataji ta fada ta koma mortar sukaja khairat tana daga musu hannu har suka fice daga gidan

Saida takai kusan 5mins a tsaye sannan ta koma cikin gidan.

 

 

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:27 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

*Page 9*

 

 

Bayan sallah magrib tana xaune parlour tana kallon wani series a Bollywood tana shan madarar holandia sbd batajin cin abinci kwata kwata.

Sallamar sace tasanyata dagowa ta amsa murya kasa kasa,

Karasowa yayi ya nemi kujerar dake kallon tata ya xauna tana kallon ta tayi wani fiki fiki karamin tsaki kawai yayi ya maida hankalin sa kan TV din.

Daukar robar hollandian dinta tayi ta tashi da niyyar komawa daki

Binta kawai yayi da idanu saida tafara hawa steps din sannanya kira sunanta

Tsyawa tayi kawai tana kallonsa amma bata dawo inda yakeba

Ganin bata da niyyar komawa yasashi yin magana

Wane irin iskanci ne kinaji ina kiranka kinwani tsaya kikam ko sokikeyi ni na tako naxo inda kike?

Girgixa kanta kawai tayi alamun a’a sannan tadawo ta xauna.

Saida takai kusan 5mins da xama sannan ya kalleta yace

Duk ranar da nakuma shigowa gidan nan ki kayimin irin wannan iskanci wato ga dodo ko daga shigowata kin wani kwashi kafa xaki koma daki.

Wai gidanma nakine ?

A hankali tace a’a

Toh karna sake ganin irin wannan sakarcin domin ni banason shashanci.

Hawayen datake makalewa ne tafara bin kuncinta ta sanya hannu tana gogewa.

Bude baki kawai yayi yana mata kallon mamaki sannan tace

Waike wace irin sakarya ce daga magana sai kuka saikace wata karamar yarinya dalla malama tashi kibani guri waxakiyiwa shagwaba anan wajan

Mtsssss yaja tsaki ya juya kansa yaci gaba da kallonsa

 

Mikewa tayi tana goge hawayen dake bin face dinta

Tana shiga dakin tasanya key ta fada gado tafara aikin kuka

Saida taji kanta kamar xai fashe sannan ta tashi ta shiga toilet tayi alwala taxo rayi sallar issha tayi addu’o inta ta koma gadon ta dauki wayarta ta soma kiran maryam

Ringing 2 maryam ta amsa wayar tana fadin

Yanxu nake shirin kiranki sai gashi kin kira

Bata iya bata amsaba sai wani kuka kawai data fashe dashi

Ya salam khairat meye haka kuma?

Bakida wani aiki sai kuka dan Allah ni ki nutsu muyi magana wacce xata amfane ki bawai ki tsaya kinamin kuka ba plssss Dan Allah ki tsaya haka.

Da kyar ta samu ta tsayar da kukan tace inajinki maryam

Uhm kinajina ko inajinki ai baki fadamin abinda yake faruwa ba bare nasan ta inda xamu fara

Hannu tasa ta share hawayen dake tahowa tace

Maryam tunjiya dakuka kawoni gidan nan ban tsinci ko Abu guda daga wajan yaya sadeeq wanda xai sanyani farin cikiba sai tsantsar bakin ciki kawai

Daxu da safe ya kafamin wasu sharuda wai karna sake nayi kuskure indan xanyi jagwal gwalon girkina na hada dashi

Sannan kuma duk wani damuwa da xai kunsamin kar nasake nabari wani yasani inayi kuskuren sanarwa wani saiyayi maganina a gidan nan

Uhm bakigadai wulakanci kala kalaba komai nayi sai yayimin tsawa

Haba khairat saikace ba mace ba ai wannan bawata matsala bace

Ban gane me kike nufi ba wannan ne ba matsala ba?

Tabbas ba matsala bace Abu daya nakeso dake ki jajur ce ki cire wannan saurin kukan naki domin duk wani Abu daxamuyi indai baki daina wannan kukanba toh bamuda mafuta.

Uhm shikenan maryam xanyi kokarin ganin na daina insha Allah

Yawwa ko kefa sannan ki cire batun soyayya ki ajje gefe xuwa wani lokaci kadan ki nunawa yaya sadeeq kema ba wani sonsa kikeyiba sannan ki daina jin tsoronsa kwata kwata????????‍♀

 

Sai da ta cire wayar a kunnanta tace tabdi jan sannan ta maida tace

Haba Maryam sokike nayimasa tsiwa ya xaneni acikin gidan nan dagani saishi?

Dariya maryam ta sheke da ita sannan tace haba sis Sanin danayi miki tun muna school bakida tsoro amma meyasa kike tsoron yaya sadeeq?

Uhm wlh nima bansani ba maryam

Uhm na fahimta yanxu dai dole ki daina jin tsoronsa kuma komai da gayya xaki ringa yinsa a gidan nuna masa xakiyi ai ba xaman aure kukeba tunda shima haka yake nuna miki kawai xaman wucin gadine tsakaninku.

Nan dai maryam ta gama tsara mata yanda xata kunta tawa sadeeq domin baxai yuwa yaringa gasataba kuma tabbas dolene ta nuna masa cewar itama macace tunda basuda isheshshen lokaci tunda xaman wata daya ya bukata dole su koya masa hankali kafin lokacin.

Suna raha suka gama wayar khairat ta ajje wayarta tanajin duk damuwarta ta fice a ranta afili tace

Tabbas yaya sadeeq baxakaci bulus ba sai yanxu na fahimta kanaso kayiwa iyanka biyayya ne sbd karsuyi fushi da kai shiyasa ka aureni nanda wata daya ka kulla wani tuggun da baxasu ganeba ka sakeni

Shuru tayi sbd wani tunanin datayi afili tace

Toh wane irin shiri yaya sadeeq yayi wanda su dad da mom baxasu ganeba?

Batada amsa don haka tayi murmushi kawai tace muxuba nida kai…..

 

Nima dai gyara xama nayi nace barina xuba ido naga anya khairat xata iya kuwa?

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:27 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

*Page 10*

 

 

Tashi tayi cike da farin ciki taje ta saka kayan bacci tabi lpyr gado ta kwanta.

 

Da asuba ta tashi tayi sallah sannan ta fara gyara dakin tana kammalawa ta sauko ta gyara parlour din ta Sanya turaran wuta hadi da room freshener, tana kammalawa ta koma daki tashiga toilet tayi wanka ta kinmtsa kanta acikin wata bakar doguwar riga tayi fakin gashinta ta dauki red dan kwali ta yanashi a kanta kamar bandana ta feshe jikinta da turare ta ta sauko parlour.

Kai tsaye ta shige kitchen ta fara hada breakfast.

Tana kammalawa ta xuba abinta ta fito parlour ta ajje ta koma dakinta ta dauko wayarta tafara ci tana latsa wayarta.

Tunda yafito daga dakin yaji wani kamshi ya daki hancinsa lumshe sexy eyes dinsa yayi ya budesu yafara sakkowa daga steps din.

Tsayawa yayi cak yafara kallonta hankalinta kwance tanacin abinci tana latsa Waya tana murmushi alamun tanajin dadin abunda takeyi a wayar

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button