AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

Eh nayi din ta fada tana murguda baki.

Hannu yasa xai matse bakin ta kauce tace wlh ka sake ka taba lpy ta yanxunna xan kira alhajin Ku na fada masa harma da abinda bakaso ya sani.

Xubewa kawai yayi akan kujera yana huci yana kallon ta.

Hollandia dinta ta dauka ta juyo tayi masa gwalo

Mikewa yayi ya nufota ta kwasa dagudu ta nufi step din…..

 

 

 

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:29 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

_Agaskiya abinda yake faruwa yanxu a social media yana bani haushi abinda akewa writers yayi yawa kawai sbd wasu tsurari daga cikinmu sun fito dawata siga tasu ta daban sai al’umma su dinga yin jam’u suna yimana xagin wulakanci harga Allah nidai abun yafara damuna dama mu muka sa kanmu in bb haxa saimu daina????????‍♀_

 

 

*Page 12*

 

Ganin ta haye saman da gudu ne ya sanyashi dawowa ya xauna yana huci yana cewa

Ashe ke karamar mara kunya ce uhm da ki tsaya kiga yadda xanyi dake acikin gidannan.

Tana shigewa daki ta sanya key ta rufe tana dariya tana fadin kai ammafa nasha da kya, Xama tayi ta dauki hollandia dinta taci gaba da sha,

Tunda ta tafi sama ya xauna yanata tunani a xuciyarsa wai dama haka khairat take ban saniba yarinya Sam bata da kunya, uhm dama kenan lamo kawai tayimin ranar dasu aisha suka xo.

Jira yake ta fito amma shuru harya fita yayi sallar la’asar amma bata sauko ba haka ya xauna kawai yana kallo har lokacin da akayi magrib fita yayi yai sallah ya dawo amma still bata parlour din a hankali ya furta

Amma wannan yarinyar bata da hankali ko abinci fah bata ci ba shiga kitchen din yayi ya duba yaga da alama ma tun girkin safe da tayi ta wanke kwanukan bata kuma yin wani ba kenan tana nufin wannan madar kawai itace abincin da xataci?

Amma gsky bata da hankali so take wani ciwon ya kamata taxo tajamin salalan tsiya, dawowa parlourn yayi ya xauna yana fadin uhm to waima ina ruwana ai kanta tayiwa bai gama rufe baki ba kamshin turaran ta ya sanar masa da isowarta parlour din dogo da kansa yayi yaganta sanye da wata doguwar riga irin mai budewa ta kasa dinnan amma mara nauyi da alama bacci kawai tasha abinta batada wata damuwa.

Ajiyar xuciya kawai yayi lokacin ta iso ta kalleshi hadi da murmushi tace Yaya ina wuni?

kamar baxai amsaba sai kuma yace uhm lpy qalau

Masha Allah kawai tace ta nufi kitchen.

Jalof din shinkafa tayi wacce taji hanta da kayan hadi sai xuba kamshi take sannan ta nika kayan fruit dinta tayi juice dai dai Shanta, tunda ta fara girkin bata fitoba shiko gogan yana parlour duk kamshi ya isheshi lumshe idanu kawai yakeyi ga wata arniyar yunwa dayakeji, jin ana kiran sallah ne ya sanyashi tashi ya tafi masallaci.

Tana kammalawa ta fito ta tafi daki sallah tayi sannan ta sakko ta koma kitchen ta karasa abinda xatayi ta xuba abincin ta fito, yana rufe kofa ta ganshi karasowa yayi ya xauna ita kuma ta ajje abinci ta kuma komawa kitchen din, kallon abincin da ta ajje yayi yana lashe baki axuciyarsa yace kai da gani wannan girkin xaiyi dadi.

Fitowa tayi hannunta dauke da jug din data xuba lemon ta nemi waje ta xauna tafara cin abinta hankali kwance, ganin ko kallonsa bata yibane a xuciyarsa yace amma wannan yarinyar batada mutunci kotayi kara tayimin bismillah.

Kamar ta shiga xuciyarsa a sama yaji muryarta tana fadin Yaya bismillah tana kallonsa.

Mtssss yaja wani dogon tsaki yace Allah ya kiyaye naci wannan kaxantar taki ni ai ba wawa bane.

Murmushi tayi tace kayiwa kanka dama bada kai na dafaba kawai na fita hakkinka ne taci gaba da cin kayanta.

Maida hankalinsa yayi ga TV din a xuciyarsa yana fadin banda karna jawa kaina raini ai da sainaci.

Tana kammalawa ta mike tana wata irin mika hadi da salati kawai kallon ta ya tsaya yanayi tana wata irin bankarewa kasa dauke idonsa yayi daga kanta ya kura mata idanu kawai yana ayyana abubuwa da dama a xuciyarsa.

Kula da irin kallon da yake matane ya sanyata yi da gayya ganin ya kasa dauke adanunsa daga kantane ya sanyata yin murmushin mugunta a xuciyarta tace

Uhm ai muddin ina cikin gidannan saina hanaka sakat kafin kwanakin mu su cika.

Jiyayi kawai numfashin sa ya sauya kuma ya kasa daina kallonta har saida ta mike ta kwashe kayan ta kai kitchen sannan ta dawo ta nemi kujera ta kwanta ta dauki wayarta tana chart da maryam tana bata lbr tana murmushi mugunta.

A hankali yake satar kallonta a tunaninsa bata saniba besan tana ankare dashiba har xuwa lokacin data gaji da xaman ta tashi ta kima dakinta.

 

 

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:28 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to my blood sis Aisha????*

 

 

*Page 13*

 

 

Tana shiga daki ta sauya kayan bacci tayi kwanciyarta tanajin xuciyarta tayi mata wasai bata da wata damuwa sai matsanaicin soyayyar sadeeq datake damunta ako da yaushe domin amadadin taji yana fita a ranta sakamakon tsantsar tsanar da yake nuna mata amma abun ba haka yakasance ba xuciyarta tayi nisa a soyayyar wanda baya ra’ayinta,tunawa tayi yau kwananta 5 a gidan hakan yana nufin saura kwana 25 ta rabu da farin cikin xuciyarta hawaye taji sun fara bin kuncinta amma takasa gogewa domin fitarsu kesan taji sassauci acikin xuciyarta, afili ta furta koda soyayyarka xata kasheni yaya sadeeq dolane kafin nabar gidannan na tabbatar da na gasaka gashi mai wahala wanda kobayan nabar gidan ka dolene abubuwan dana aikata suyimaka yawo akwakwalwar ka domin baxai taba yuwuwa kamaidani baxawara a idon duniya ba domin Bb mutumin da xai kalle ni amatsayin budurwa, tana xuwa nan tayi shuru na yan mintuna saikuma ta fadada murmushi a fuskarta ta juya ta dauki wayarta ta kashe ta gyara kwanciyarta tayi addu’a hadi da runtse idanunta.

 

Tunda ta mike yakebin bayanta da idanu harta bacewa ganinsa ajiyar xuciya ya sauke yace kai amma wannan yarinya akwai shu’uma ni dutse ne daxataxo gabana tana irin wannan karairayi jiki saikace wata tarwada, uhm gsky dole na dau mataki a kanki yarinya domin xan iya jure kowane wulakanci amma banda irin wanna mtsssss yaja wani dogon tsaki yana cewa

Yaran yanxunema duk sun lalace inba hakaba yaxa’ayi wannan gansamemiyar yarinyar taxo gabana bb ko kunya tana kararraya, shi kadai yayita surutu daga baya ya mike ya rufe ko ina na gidan ya kashe kayan kallon ya koma dakinsa yayi wanka sannan ya kwanta yana lumshe idanunsa har yanxu jinsa yake tareda wani bakon al’amari tun abunda khairat tayi masa daxu, lumshe idanunsa yayi afili ya furta ammafa wannan yarinyar Allah yayi mata xubin halitta ahaka har bacci ya kwasheshi.

 

Washe gari karfe 7:00 khairat ta fito daga dakinta sanye cikin wani material dinkin Riga da siket yayi mata kyau sosai gyara gidan ta soma yi tundaga dakinta xuwa parlour sama dana kasa gidan yayi kal dashi ko ina sai kamshi yakeyi tana kammalawa ta tashi da niyyar fitowa ta gyara harabar gidan domin tunda taxo gidan bata fito wajan ba barekuma batun gyara wajan sau daya ma ta taba ganin wajan lokacin da xata raka su aisha washe garin kawota kenan, sanin datayi bb ko mai gadi a gidan ne ya sanya ko hijab bata dauka ba ta bude kofa ta fito turus kawai tayi tana bin wajan da kallon mamaki gurin kal yake ko ina a gyare yan flowers dake wajan duk anbasu ruwa da alama kuma ba’a jima dayin aikinba, daga kata tayi daidai inda takejin sautin radio kasa kasa wani dattijo ta gane xaune a inuwar dake bakin gate din yanajin radio idanunsa arufe da alama ma baisan da fitowarta ba domin akwai taxara a tsakaninsu sbd gidan babban gida ne, tabe Baki kawai tayi ta juya ta koma ciki tana fadin lalle ma matumin nan har mai gadi ya samo amma koya fadamin kwafa tayi tace uhm ina naga wannan darajar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button