AURAN WATA DAYA

Kai tsaye tashi kitchen tafara hada break fast tana tunanin toh yanxu wannan dattijon ne yayi duk wannan aikin chab amma gsky yayi kokari, tana kammalawa ta dauki plet ta xuba ta xuba awani shima ta fito ta koma daki chan tafito sanye da hijab ta dauki abincin ta fita.
Tana karasawa wajan mai gadi suka gaisa tace baba abunci na kawo maka amma kayi hkr bansan da xuwanka ba shiyasa ban dora da wuri
Mur mushi yayi yace Bb komai hajiya ai tun jiya naxoma kuma alhaji yabani kudin abinci ai
A’a baxa ayi hakaba ka karba abincin duk sanda na dafa xan kawo maka basai kasiya ba
Godiya yayi mata sannan ta koma ciki tayi break fast din tana kammalawa ta koma daki takira wayar aisha tana ringing amma ba’a dagaba harta katse sannan ta sake kira said a takusa katsewa sannan aka daga.
Shuru Aisha tayi mata kawai ta sanya wayar a kunne batare da tace komai ba
Khairat najin haka tasan fushi aisha tayi dan haka cikin raha tace sis y kk kwana 2?
Uhm dama xakice HK tun ranar da muka xo ko nemana baki kuma yiba ko mom ma naga yanxu andaina kiranta.
Ayya sis wlh ba haka bane maganar mom na fada miki kunyar ta nakeji ke kuma nasan nayi laifi amma kiyi hkr kinji
Uhm toh inbanyi hkr dakeba khairat yakikeso nayi?
Yawwa yar Uwa haka nakeso nandai sukasha hira tace ta gaida mata mom kafin taxo sukayi sallam ta ajje wayar ta kwanta.
Tunawa tayi kwata kwata bataji duriyar sadeeq ba dan haka ta tashi da niyyar fita tadan duba…..
*Neenat saif*
[12/18, 7:28 PM] +234 701 918 7780: ????????????????????????????????????????????????????????????????
*AURAN WATA DAYA*
????????????????????????????????????????????????????????????????
*Written by neenat saif????????????????????????????????*
*Dedicated to readers AURAN WATA DAYA FANS GROUP ND AUNTY MAMEE’S NOVELS GROUP INAYINKU IRIN TOTALLY DINNAN????????*
*Page 14*
Tana fitowa ta sakko kasa taga tana tunanin me sadeeq yakeyi da har yanxu bai fitoba? komawa tayi saman ta fara sanda xuwa kofar dakinsa ta saka konnenta jikin kofar shuru taji Bb wani motsi anya kuwa lpy sadeeq yake? ta furta axuciyarta wani dan karimin tsaki kuma taja ta nufi dakinta tana fadin ko ina ruwana ma oho tana shiga ta kwanta ta soma bacci.
Sai wajan 2:00pm ta farka tana salati ta duba wayarta taga tym ya salam wane irin bacci nayi hk da har akayi sallah ban farka ba?
Cikin sauri ta mike ta shiga bayi tayi alwala tafito tayi sallah tana kammalawa taji cikinta yana qugi ta shafa cikin nata tana fadin wannan wace irin yunwa ce saikace banyi break fast ba.
Mikewa tayi ta fito da niyyar shiga kitchen ta dora abinci turus ta tsaya tana kallon parlour din dataga da alama tunda ta koma sama Bb wanda yashigo parlour din hasalima kofar data rufe tananan arufe alamun kwata kwata ba’a budetaba kenan hakan yana nufin har yanxu sadeeq bai fitoba gashi ko matsinsa bataji a samaba.
Tafi 10mins a tsaye tana tunani badai wani abune yasamu sadeeq ba tunawa tayi jiya a halinda ta tafi tabar sadeeq da daddare a firgice ta furta ya salam meyake faruwane? kardai ace ni da kaina na cutar da mijina ohhh ashefa ba mijina bane ta fada tana komawa sama(kaji wata yarinta ta khairat???? tunda aka biya sadaki kuma muka shaida ai sadeeq yaxama naki☺)
Kai tsaye dakinsa ta nufa ta dora hannuta a hankali ta tura kofar gabanta yana faduwa, wayam taga dakin gashi duk a hargitse kan gadon harda kayan dayasa jiya toh ina ya shiga ko yana toilet ne cikin sanda takarasa shiga cikin dakin tatsaya vakin toilet din kusan 2mins amma bataji motsi a acikiba kai tsaye ta bude taga bb kowa aciki fitowa tayi daga dakin tana tunanin ina sadeeq yake? ko bai kwana a gidan bane? dabara ce ta fada mata ta koma dakinta ta sanya hijab ta fito harabar gidan kai staye tanufi wajan dakin mai gadi dataga baya bakin gate din tasan yana ciki tsayawa tayi nesa da dakin tana sallam da sauri ya fito yana fadin hajiya lpy
Tace lpy qalau baba dama tmbr ka xanyi Bb Wanda yaxo gidannan domin xanyi baki ne tun daxu sai bacci ya kwasheni kuma wayata a kashe take sai yanxu na tashi.
Ai hajiya tun safe da alhaji ya tafi aiki bb wanda nakuma budewa gate a gidannan sai mai bawa shukokincan ruwa dayaxo ya gyara gidan ya tafi kuma shima tun kafin fitowarki ta safe ne.
Sai alokacin ta lura bb mota guda daya a gidan in bata mantaba ranar da su rahama sikaxo mota ukuta gani yanxu kuma biyuce.
Juyawa tayi tace toh baba inajin sun fasa xuwane barinaje na dora abinci an barka da yunwa.
Ai Bb komai hjy
Murmushi kawai tayi ta koma ciki tana fadin wato yau aiki sadeeq ya tafi amma konaji lbr bansan lokacin da xai fara daukata koda amatsayin yar uwarsa danakeba,ma aikata har 2 ya dauka amma ko yasanar dani hawayen datayi sabo dasune taji sun fara xuwar mata tayi saurin gogewa tana fading aiko kaima yau saina baka mamaki.
kai tsaye ta shige kitcin ta dora abinci mai rai da lpy tana kammalawa taxuba ta mikawa baba mai gadi nasa sannan ta xuba ragowar tacinye kayanta domin su 2 kawai tayiwa ta wanke kayan data bata ta dada gyara kitchen din sannan ta dada gyara parlour din ta sanya turaruka da room freshener sannan ta koma dakinta tayi wanta tana wanka taji ana kiran sallar la’asar dan haka tayo alwala ta fito ta tayi sallah sannan ta xauna ta tsara kwalliya ta dauko wani wando da riga wondon irin pencil dinnan ne sai kuma ta dauki bes ta sanya ta dauki irin falmaran dinnan da ake daurewa ta gaba ta sanya wacce tsayinta yake iya kugu ta gyaragashinta tayi farking dinsa ta sanya irin hular nan da bayanta yake a bude ta fito da gashinta tana fadin xandai kira aisha ko maryam wata taxo tayimin kitso.
Tana gamawa ta feshe jikinta da tura ruka sannan ta juya ta kalli mudubi tana murmushi(nima lekawa nayi ina fadin yau xa’asheke yaya sadeeq kennan????)
Wani dan karamin kyalle ta dauka ta feshe shi da turare ta dauki wayarta ta ta dauki cingum guda daya ta jefa a baki ta sauko kasa sannan ta shiga kitchen ta dauko hollandia mai sanyi tareda karamin cup ta ajje a parlour tana murmushi ta xauna ta kunna TV tana kallo.
Bata wuce 1mins da xama ba ya turo kofar hadi da sallamar da tsaya a kasan makoshinsa…….tsayawa kawai yayi yana kallonta dayake kujerar dake kallon kofa ta xauna,mikewa tayi ta amsa sallamar tana dakin wani lallausan murmushi ta nufo inda yake.
Tunda ta mike ya karsa daskarewa awajan domin gani yake kamar ba khairat ba yarinya Uwa aljana irin wannan madarrar kyau haka.
Sannu da xuwa take mai amma taga bemasan tanayiba kawai yayi mutuwar tsaye ne, matsawa tayi gab dashi ta dan kara tsayi ta huramai iskar bakinta tana fadin
Ur wlcm yayana ta sanya kyallen tana goge masa fuska tana wani kashe ido daya wani dadda dan kamshi yaji yana shaka ya lumshe idanunsa a fili yafurata ya salam????????♂
Murmushi tasake yi tace yadai naganka hakan?
Da kyr ya tattara nutsuwrsa yace Bb komai
Owk kawai tace ta amsa briefcase din dake hannushi tana nuna kujera da hannun tana fadin muje ka xauna nasan ka gaji da yawa tayi gaba Bb musu kawai yabita ta nuna mai kujera ya xauna, sannan ta dauki cup tatsiyaya hollandia din ta mikomai tana fadin
Ga shi nasan kana bukatar abu mai sanyi
Nan ma bai musa mataba ya amsa a xuciyarsa yana yana fadin anya yarinyar nan tana da hankali kuwa…….be kai ayaba yayi saurin kallon kasa jin tana cire mai safar dake kafarsa da sauri ya kalleta ta kuma kashemai ido tana dada fadada murmushinta tana gamawa ta mike tana hada kayan ta nufi sama binta yayi kawai da idanu domin ko magana ya kasa da abin mamaki yake bashi yanxu kuma tsoro abin yakoma bashi anya kuwa Bb aljanu a gidannan? Ya fda axuciyarsa.