AURAN WATA DAYAHAUSA NOVEL

AURAN WATA DAYA

 

Khairat kuwa tana hawa saman ta tsaya tana dariyar mugunta tana fadin xaka gane kuranka ne ko a haka na barka nasan na figitaka.

 

 

 

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:29 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

*AURAN WATA DAYA*

????????????????????????????????????????????????????????????????

 

*Written by neenat saif????????????????????????????????*

 

*Dedicated to aunty mamie’s wannan page nakine nabaki shi kiyi yadda kikeso dashi tukuicina na ????????????????????????ustaxiya ko yar duniya????????‍♀????????‍♀????????‍♀ page 39 Allah ya kara basira????????*

 

*Page 15*

 

 

Tana hawa saman kai tsaye ta mika masa kayan daki sannan ta gyara dakin tsaf ta feshe shi da room freshener da turaruka masu kamshi komai yayi tsaf tana gamawa kai tsaye dakinta ta wuce tafara aikin chart dinta data saba.

Tunda ta tafi ta barshi cikin tunani anya yarinyar nan lafiyarta qalau kuwa, mace ace kullum dabi’ar ta sauyawa take washe garinda aka kawota atsorace take dani har xuwa kona 2 magana kawai innayi mata hawaye ke biyo baya tsabar tsoronta, bayan kwana biyu kuma masifar tsiwa naga tana damunta,yanxu kuma abubuwa musu wuyar mantawa take jifana dasu tundaga shigarta mu amalar ta kai komai ma, lumshe idonsa yayi yana fadin ya ilahi gsky da sake dole na dauki mataki tun kafin yarinyar nan ta illatani.

Yana xaune har kusan 1hrs amma baiji takuma sakkowa ba tashi yayi yanufi saman kai tsaye dakinsa ya nufa yana bude kofar ya tsaya cak yanabin dakin da kallo wani daddadan kamshi yaji yana xiyartar hancinsa a hankali ya sauke wata ajjiyar xuciya yana kallon ko ina yayi tsaf sai kyalli yake sabanin yanda yafita yabar dakin kaca kaca ko ina da datti, jiyayi kawai ta burgeshi domin yanason mace mai tsabta a iya kwanakin dasukayi ya fahimci khairat nada tsabta sosai bai taba ganin kura a gidan ba ko yaga ta ajje wani Abu a wajanda bai dace ba in bai mantaba tun a gida yana yawan jin mom na yabonta sosai ta wajan tsabta, karsawa yayi ta xauna bakin gado tana tunani barka tai daga baya kuma yasaki wani dogon tsaki yana fadin komai yasa ma nake yabonta oho nidai nasan bana sonta kuma dole na nuna mata cewar nima dan xamanine tunawa yayi da Abdul ya dauko wayar sa yana fadin duk kai kabani matsala wlh wannan shawarar taka batada wani amfani.

Kiran layin Abdul yayi yana nagawa yace kai Malam kana INA?

dariya Abdul yayi yace kadai tsaya mu gaisa ko

Bana bukata nidai kawai ka fadamin kana INA?

Murmushi kawai yayi yace ina gida

Yauwa dan Allah kaxo gidan yanxu kaji magana xamuyi dakai sannan ka tsaya a hanya kayomin takeaway

Owk Bb damuwa kabani 30mins xan karaso

Owk saikaxo ya kashe wayar ya tashi ya fito parlour din sama ya xauna yana danna Waya.

Can jimawa yaga kiran Abdul yana shigowa ya amsa yana fadin y dai?

na iso ina harabar gidan ka

Ammafa kayi sauri ka shigo parlour kofar abude take yanxu xan sauko ya kashe wayar.

Ya nufi dakinsa ya sauya kaya ya sanya Jens da t-shirt ya sauko kasan a parlour ya iskeshi xaune harya kunna TV yana kallo karasowa yayi suka gaisa yace kaga mikomin abincinnan naci wlh wata muguwar yunwa nakeji.

dry Abdul yayi yace haba sadeeq wai INA khairat dinne take barinka da yunwa?

Ina ruwanka banson tsurku barni nagama cin abincinnan sai muyi magana yajawo abincin ya bude yafaraci shiko Abdul kallonsa kawai yake.

Yana gama cin abincin ya ya tattara ragowar ya mikawa baba mai gadi sannan ya dawo ya xauna kusa da Abdul yana kollonsa

Shima jiyowa tayi yana kallonsa yace toh inajinka fadamin meke faruwa?

Wata harara sadeeq ya jefa masa yace ai kafinin sanin meke faruwa tunda kaika bani shawarar na dauko matsala na ajje a gidana sannan kuma ka tambayeni meyake faruwa.

Kallonsa kawai Abdul yayi yace naji nina baka shawar karka bijirewa iyayanka akan auran khairat amma ai bani nabaka shawarar kayi AURAN WATA DAYA da itaba wannan ra’ayinka ne saida nace maka baxai yuwauba amma kakawon wata banxar hujjarka wacce batada amfani sannan yanxu kace nina baka matsala.

Kallonsa kawai sadeeq yayi ya karka da kai yace naji abinda ya wuce ya riga ya wuce yanxu kawai sonake kasama mun mafita.

Mafita kuma?ca nake yau kwananku shida ko bakwai da aure kaga kenan lokacin daxakaje wa su dad da maganar sakin khairat baixoba ko rabi ba’aciba.

Nasan da haka nidai ayanxu banajin xan iya cigaba da xama da khairat a gida daya yarinyar sotake ta haukatani kawai

Da mamaki Abdul ya kalleshi yace ban fahimta ba fahimtar dani yadda xan gane khairat naso ta haukataka.

Gyara xama yayi ya bashi lbrn kwana 2 yadda dabi’un khairat suka sauya da irin abubuwan datakeyi masa harda rashin kunya.

Juyowa Abdul tayi ya dafa kafadatsa yace sadeeq inaso ka nutsu kayi tunani sosai khairat ba haukataka takeson yiba kuma ba ita take sanyaka damuwa a xuciyaba kaine kake sanyawa kanka wadannan abubuwa, soboda ka hana xuciyarka abunda takeso tun da dadewa, baxan fasa gaya maka cewar xuciyarka tanason khairat kuma kaima kanason khairat kawai kana hana kanka farin cikine sbd wata banxar dabi’arka da batada amfani.

Karkada kai kai sadeeq yashi gayi yana fadin karya kake ni bamasonta kuma kafi kowa sanin bana sonta…….

 

Kalaman da suka daki kunnan ta kenan lokacin datake sakkowa daga step din tsayawa tayi tanajin wani xafi a xuciyarta kunnan ta yana amsa kuwwar kalmar dataji sadeeq yana fada hawaye taji yanabin kuncinta tayi saurin gogewa.

 

Bb Wanda yasan da xuwanta hakan ya sanya sadeeq bai tsaya da maganar saba na kuma fada banason ta kuma kaima kasani nasan cewar banida wata wadda nakeso amma kuma bana ra’ayin rayuwa da khairat shiyasa tundaga lokacin Dana fahimci khairat nasona tadaina ganin koda dariyata ne don haka xanyi hkrn xama da ita xuwa lokacin dana diba mata ya ciki.

Uhm tunda haka kace Allah ya taimaka amma baxan kara baka wata shawara akanta ba dole nasan wata rana da idanunka xaka xubarda hawaye akan khairat ka ajje wannan magana a brain dinka dole wata rana lokaci ya nuna mana.

Ya bude baki da niyyar yin magana yaji motsinta tana shigowa don haka ya fasa yanemi waje ya xauna.

Karsowa parlour din tayi tana sakin wani murmushi tana fadin yau a gidan namu ai naxata saimunxo biko.

Dry Abdul yayi yana fadain a’a mun sarara mukune kugama cin amarcin.

Wata uwar harara sadeeq ya watsa mata ganin kayan daxune ajikinta haka kurum yaji xuciyrsa namasa xafi dalilin fitowar khairat a haka har Abdul ya ganta jiyayi gabada ransa yabaci kamar ya cemata ta koma tasako hijab amma ya danne.

Ta fahimci abinda me damunsa dan haka ta karso gaban Abdul tace barinakawo maka abinshako

A’a na gode yanxu mukagama cin abincin ma ai

Toh kawai ta fada ta karasa gaban sadeeq ta sunkuya har sunajin numfashin juna ta sanya hannu ta shafi gefen face dinsa tayi kasa da voice dinta yanda shikadai xaiji tace haba dear bakayi wankaba bafa naga ka sauya kayan ka barinaje na hada maka ruwan wannaka.

Kallonta kawai yake hatta Abdul da baijin metakecewa ba kallon mamaki yake mata murmushi tasakarwa sadeeq ta huramai iska a fuska tace bani 5min yanxu xan hada maka tayi gaba batare da tasake juyowaba…

 

*Neenat saif????????*
[12/18, 7:29 PM] ‪+234 701 918 7780‬: ????????????????????????????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button