AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

      ????????????????

COMMENTS AND SHARE

BY MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

NA GAISHEKI SIS NA???? SURRY BABY, ALLAH YA BAR MIN KE.

AZIMA DA AZIZA GRP NA GAISHEKU???? MASU MAFARKAI DA TSORATA NA JINJINA MUKU, A CI GABA DA CHAPTAWA.????????

FREE..
????️==1️⃣3️⃣↪️1️⃣4️⃣

“Zaran saƙar dana kuma?” Hajja ta faɗa tana kallon hannun Baffa da ya riƙe zaren yana kalla, Aziza ce ta matso kusa da  Baffa ta duƙa ta ce
“Baffa me zaran ya ƙunsa?” shuru Baffa ya yi na wasu lukota kafin ya ce
“Ba ƙaramin hatsari wannan zaren yake da shi ba, ana amfani da shi wajan yaƙi! Ko kuma a ɗaure takwabi da shi, duk wanda aka sara ko aka yanka da takwabin da aka d’aure da shi to sunansa gawa! Walau mutum ko aljan! ” a firgice Aziza ta ce
“Kenan mutum mutuwa zai yi?”
“E Aziza, wa ya kawo zaran nan gidan nan? Sannan ta ya aka samo shi? Dan nasan ba a samunsa nan kusa sai an je can cikin jejin lore, wanda wannan jeji tun kafuwarsa shekaru aru-aru  babu wani ɗan adam din da ya taba zuwa idan ba ni ba”  Hajja ta ce
“Ai kuwa dai Azima ce na ganta da shi dan tun safe take zaune a inda ka tashin nan take saƙa shi,bayan ta gama ta shige ciki, bata jima da shiga ba ka shigo” da sauri Baffa ya miƙe tsaye ya ce
“Azima! Azima! Azima!?” ya kwala kiran sunanta da karfi, Aziza ta ce
“Bari na kirata Baffa” cikin faɗa Baffa ya ce
“Nan da bukka ta ce bata jin kiran da na mata?” Hajja ta ce
“Ayye Baffan yan biyu ka bi a hankali mana, watakila bacci ne ya kwasheta Aziza kirawota”  Baffa ya ce
“Ke da kika ce ina shigowa bata jima da shiga ciki ba shine har bacci zai kwasheta?”
“Ai Azima bata da wuyan bacci” cewar Hajja, shi dai Baffa shuru ya yi tare da gyara tsayuwarsa ya maida hannunsa baya yana jiran fitowar Azima.

    Tana kwance a gadon kara, rabin jikinta macijiya sai juyi take yi kanta a hargitse, Aziza ta shigo da sallama ko amsawa Azima bata yi ba, Aziza ta ce
“Ba ki jin Baffa na kiranki ne?”

        “Mtswwwww! Na ji mana, tunda dai ni ba kurma ba ce! Je ki ce ba zan zo ba!” a fusace Aziza ta sa hannnu ta janyo wuyar Azima ta ce
“Wallahi! Wallahi! Wallahi! Kinji na rantse miki ko? To sai kinje, kuma dole ki ba wa Baffa amsar tambayoyin da zai miki, za ki tashi ne ko sai na b’ace dake a dakin nan na wujijjigaki!?” Aziza ta karasa maganar idonta da fatar jikinta suna canza kala, ganin haka yasa Azima miƙewa fuuuu ta fice, rufe ido Aziza ta yi ta dawo dai-dai sannan ta bi bayan Azima, a tsaye ta sameta Baffa na tuhumarta inda ta samo zaren sakar dana, cike da rashin tsoro da rashin kunya ta ce
“A inda ake samu na samo!”

      “AZIMA!!!” Aziza ta faɗa a tsawance ta yi kanta dan ta kai mata mari, da sauri Hajja ta ja hannun Aziza sannan ta fashe da kuka, murguɗa baki Azima ta yi ta fice a gidan ma gabadaya, Baffa kuwa suman tsaye ya yi, Aziza kuma tana lallashin Hajja dake kuka.

Cikin kuka Hajja ta ce
“Wai ni meke shirin faruwa dani ne kam? Me yasa Azima ta zama haka? Kwata-kwata yanzu bata shakkar gaya mana magana! Aziza dame ku ke so naji? Idan ba ki taimakawa yar uwarki ki gyara mata halinta wa zai iya yin hakan?” Hajja ta ci gaba da kuka, Baffa kuma bukka ya shige ya zube a bakin gadon kara jikinsa na rawa, hakika jejin lore ɗan adam baya shiganta ya fito lafiya, duk ɗan adam din da ya shiga jejin lore to sunansa gawa! Shi ma sanadiyyar shigarsa jejin lore ya yanko zaren saƙar dana sadda zasu gwabza da Banju ne, rass! rass! rass! gaban Baffa ya bada nan zufa ta shiga tsatstsafo masa ta ko wace kusurwar gashi dake gangar jikinsa, a fili ya ce
“AZIMA BA MUTUM BA CE! TAYA ZAN GWADATA NA GANE HAKAN DAN NA WARKARWA ZUCIYATA TANTAMA DA ZARGI!? INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN! YA ALLAH KASA KAR ABUN DA NAKE KWANA NAKE TASHI DA SHI YA ZAMA GASKIYA!” Baffa ya karasa maganarsa hannunsa a sama hawaye na gangarowa.

       Da kyar Aziza ta ɗaga Hajja ta shigar da ita bukkarta tana lallashinta amma ina Hajja ta kasa tsaida hawayenta, kasa juran kukan nata Aziza ta yi ta miƙe a hankali ta fita zuwa randar kasar dake tsakar gidansu ta ɗibo ruwa a kwarya ta bude bakinta ta zuba abu a ciki sannan ta koma ta ba wa Hajja, ƙin karba Hajja ta yi ta ci gaba da kuka, Aziza ta ce
“Dan Allah Hajja kiyi shuru ki daina kuka, kin ga gidan nan bamu da sauran ganyen magunguna balle na haɗa miki ki sha idan kanki ya fara ciwo, zan yiwa Azima magana ga ruwan nan ki sha zuciyarki ta yi sanyi” da kyar Hajja tasa hannu ta karbi ruwan ta sha, tana shan ruwa ko minti uku bata yi ba, ta zube a jikin Aziza, hawaye ne masu zafi sosai suka zubowa Aziza a fuskarta a fili ta ce
“Kiyi hakuri Hajja ki yafe min ba zan iya ci gaba da kallon kukanki ba, baccinki shine mafi alkhairi, tun a yau da ba ki san su waye mu ba kina irin wannan kukan ran da kika sani za ki hadiyi zuciya ne Hajja? Ina ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan iya rasaki ke da Baffana ba! Zan ci gaba da boyewa tare da dakatar da yar uwata, ko da kuwa zamu kashe juna” Aziza ta karasa maganarta tana sake rungume Hajja, ta sha kuka sosai kafin ta gyarawa Hajja kwanciya ta fita.

         sallama ta yi a bukkan Baffa, da sauri Baffa ya share hawayensa ya ce
“Shigo Aziza” cikin natsuwa ta shigo,zama ta yi kusa da kafarsa ta ce
“Baffa kuka kake yi?” girgiza kai Baffa ya yi ya ce
“A’a ba kuka nake yi ba Aziza” shuru Aziza ta ɗan yi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Baffa
ina so na san meke ƙunshe da wannan zaren da Azima ta saƙa”

     “Me kuma kike so ki sani bayan wanda na gaya miki Aziza? Hatsarin da ke cikin wannan zaren ba zai faɗu a baki ba tsananin yawanta, da ace za a dauki kwaya ɗaya tak! A jefata a cikin rafin jimulo, ina mai tabbatar miki duk wanda ya sha ruwan wannan rafi zai mutu!”  dam! dam! dam! gaban Aziza ya bada nan ta shiga saƙe-saƙe a ranta tare da tunane-tunane, shin wa Azima take son kashewa da wannan zaren? “BAFFA” wata zuciyar ta bata amsa da sauri ta miƙe tsaye a firgice tana zare ido tare girgiza kai gami da fadin
“A’a karya ne! Ba zai yu ba! Ba zan bari hakan ta faru ba!” ganin yadda ta ruɗe lokaci ɗaya ne yasa Baffa tashi da sassarfa ya kama  hannunta ya zaunar da ita ya ce
“Aziza natsu mana! Tsaya…kina ji? Menene? Gaya mini? Miye ba za ki bari ya faru ba?” kuka Aziza ta fashe da shi mai tsanani tana kwanciya a jikin Baffa, sosai  hankalin Baffa ya tashi yana tambayar Aziza meke faruwa!.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button