AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin kuka Aziza ke faɗin
“Me yasa! Me yasa! Me yasa!” da kyar Baffa ya shawo kan Aziza ta yi shuru ta daina kuka, Baffa ya ce
“Aziza meke faruwa ki gaya min gaskiya karki boye min komai, ni mahaifinki ne” saita natsuwarta Aziza ta yi ta ce
“Baffa, haihuwarmu ta yi muku rana?”
“Subhanallahi! Wannan wace irin magana ce kike faɗi Aziza?”
“Baffa kukan da Hajja ta yi a kan Azima dazu bazan sake bari hakan ta faru ba, ba zan sake bari ba!” ajiyar zuciya Baffa ya sauke,ita kuwa Aziza ta yi hakane dan kawar da shakku a zuciyar Baffa, shuru na ɗan wani lokaci ne ya ratsa wajan kafin Aziza ta ce
“Amm Baffa? Taya za a lalata zaren saƙar danar da yake hannu Azima?”
“Wannan ba shi bane abunda nake tunani Aziza, yadda aka yi Azima ta samu zaren nake tunani”
“Amm amma Baffa ta ce inda ake samu ta samu! Ya matsayin hatsarin jejin lore yake?”
“Aziza faɗin hatsarin jejin lore ba zai yu ba, dan yafi karfin ki fasalta shi da komai, taya har Azima zata shiga wannan ƙasurgumin jejin ta fito tana yar adam? Wannan shine tambayar da nake yiwa zuciyata amma na kasa samun amsa, ban san meke shirin faruwa da mahaifana ba”
“Baffa ka rabu da maganar Azima, kasan wani lokaci ba hankali gareta ba, yawwa kuma Baffa na mance ne ban gaya maka ba, Azima kamar tana da aljanu! Dan cikin dare sai na dinga ji kamar tana ta buge-buge da sambatu ita dayanta, Baffa na tabbata su ne suke saka ta rashin kunya,kuma ba mamaki karya take yi ba ita taje jejin lore ba, sai dai idan aljanun ne suka je suka kawo mata, ka yarda dani Baffa gaskiya nake gaya maka” Aziza ta karasa maganarta tana riƙo hannun Baffa, jinjina kai Baffa ya yi ya ce
“Kenan wani irin aljanu Azima ke da shi? Wanda har zasu iya kawo mata zaren saƙar dana? Me zata yi da shi? Kuma har tasan yadda ake saƙata?” zare ido Aziza ta yi ta hau rawar murya tare da in’ina
“Amm….eh…..umm….ohh…Baff….Baffa ….kar…ka…da..mu…da…Azima…ni nan zanji da ita, zan mata hayaƙin aljanu zata warke da yardan Allah na san ka yarda dani ko Baffa?” murmushi Baffa ya yi yana jin kaunar Aziza a cikin ransa, hakika ba zai ce baya son Azima ba tunda ita ma ƴarsa ce, amma aka ce mai kyautata maka shi ne wanda yake rayuwa a cikin zuciyarka,
“Na Yarda da ke Aziza, Allah ya miki albarka” murmushi Aziza ta yi ta miƙe tsaya tare da fadin “Amin Baffana” fita ta zo yi a bukkan har ta duƙa sai kuma ta ɗago tare da juyowa ta ce
“Amm Baffa? Baka faɗa mini abunda zai iya lalata zaren saƙar dana ba?”
“Aziza sanin wannan ba sauki garesa ba, har sai an koma jejin lore, jejin da mutane ba su shiga”
“To amma Baffa kai a garin yaya ka shiga ka fito?”
“Tsoron tarihi ne Aziza, kun dai sannin a matsayin mahaifinku! Amma har kwanan gobe baku da tarihin mahaifinku, na sha miki alƙawari zan baki tahirin jarumtar mahaifinki! Abunda yasa bana son faɗi yanzu sabida jarumtar bata jawo min komai ba sai babban kuskure”
Da sauri Aziza ta dawo ta zauna ta ce
“Baffa kamar ya? Dan Allah ka gaya min”
“A’a Aziza dama kin tashi kin tafi ne da ya fi miki alkairi, dan ba zaki ji komai ba a yanzu” ganin yadda Baffa ya yi maganar yasa Aziza miƙewa a hankali ta fice, tana fita ta koma bukkansu tana tsaye tana ta saƙa da warwara, a fili ta ce
“Kenan domin dakatar da Azima nima sai naje jejin lore? Idan kuwa hakane! *yau din nan zanje domin dakatar dake, amma kafin nan sai kin gaya min wanda kike hari da zaren sakar Azima!” Aziza ta faɗa tana harɗe hannuwanta.
????????????????????
Zaune suke a fadar sarki Chubaɗo, da sauri Maga Isar da saƙon kwana ya zo ya zube a gaban sarki ya ce
“Ranka ya daɗe! Sako ce daga yankin ja’i” da sauri wa inda suke zaune a wajan suka mai do da kallonsu kan Maga Isar da Sako, wazirin kwana ya ce
“Maga Isar da sako, buɗe ka karanto mana abunda yankin ja’i suka rubuta” jiki na rawa Maga Isar da saƙo ya zo zai buɗe sakon sarki Chubaɗo ya dakatar da shi da cewa
“Dakata! Maga Isar da Saƙo, wannan saƙo ba na iyakar mu na nan kawai za a karanta ma wa ba, a’a yanzu maza kuyi aike a tara mutane,kuje ku sanar da Mai unguwa Ori, ku kira Arɗo tare da Baffa Mandi, da Magaji Bawa duk a hallara yanzu” Maga Isar da sako ya amsa da to, sannan ya mike da sauri dan isar da saƙon sarki chubaɗo.
A cikin yan mintuna ƙalilan kowa ya hallara a fadar sarki Chubaɗo , kowa yana fargaban kar yankin ja’i ace sun rubuta ba zasu taimake su ba.
Bayan kowa ya bada hankalinsa sarki Chubaɗo ya ce
“Maga Isar da sako karanto mana abunda yankin ja’i suka rubuto” Maga Isar da sako ya amsa da to, sannan ya buɗe wasikar yankin ja’i ya fara karantowa kowa naji.
” Wa’alaikumussalam, da fatan yankin kwana su na lafiya? Ya kuma fargaban iftila’in da ku ke ciki? Kashh! Ayya! Allah Sarki! Wasikarku ta iso garemu na neman taimako! Tunda har yankinku ya duƙawa tamu yankin,mun yarda zamu taimaka muku da Innu Maciji! Zai zo gobe, amma abun mamaki ace kuna da mutum a yankinku kamar Magaji Bawa har sai kunzo yankinmu neman taimako? Koma miye daukakarmu ce, tunda yankuna yanzu zasu shaida kun watsar da makamanku wa yankinmu, saƙo daga yankin ja’i, mun karb’i ƙudirinku!“
Maga Isar da sako yana gama karantawa Baffa ya miƙe cikin fushi ya ce
“Sadda muka tura wasika yankin jimo dan su taimaka mana da jarman macizai magana mai dadi suka mana sannan suka jajanta mana suka amince da bukatarmu, amma yanzu wannan wasika na yankin ja’i har da izgilanci a ciki” Arɗo ya mike shi ma ransa a b’ace ya ce
“Duk abunda aka gaya mana laifin waye Magaji? Na ce laifin waye!?” tsohon Sarkin fulanin kwana Baffa Mandi ya ce
“Yanzu ba lokacin nuna fushi bane sabida halin da muke ciki, tunda sun amince zasu taimaka mana shikena!” Garkuwan fulanin kwana ya ce
“Amma abunda Arɗo ya faɗa gaskiya ne, Magaji da ace ka yi wani abu a kai da yanzu wannan bala’in an gama shi, me yasa ba zaka dawo yadda kake da ba? Idan ka manta da takenka sai a tuna maka….!”
“Ya isa haka Garkuwa!” Baffa ya dakatar da shi idonsa jajur, Ori ya ce
“Garkuwa yana da gaskiya Magaji, da ace kayi wani abu a kai da yanzu yankin ja’i basu gaya mana magana ba” Wazirin kwana ya ce
“Tabbas hakane Magaji, da ace kayi wani abu a kai da har yaushe zamu duƙawa yankin ja’i balle su mana izgili kamar mu muka ɗorawa kanmu masifar!” haka kowa yasa Baffa a gaba ana cewa duk abunda yankin ja’i suka faɗi har da laifinsa, jikin Baffa ne ya hau rawa ya daka tsawa da faɗin
“NA CE YA ISAAAAA!!” ya juyo yana kallon mutanen da suke wajan ya ce
“Wai ku baku duba gagarumin bala’in da nake hangowa ne? Na koma na haƙo kayayyakina da na binne tamkar haƙo maƙabarta ne wa yankin nan! Dan karku manta da aljanun da mayun da na rufe! Duk abuna ban cika kisa ba sai inta kama dolen- dole! Tunda na kashe Banju nayi sallama da kwanciyar hankali, wanda a yau duk faɗin yankin kwana babu yaran da ake zargi kamar yarana AZIMA DA AZIZA! duk da ba zan hanaku zarginsu ba, amma ko da sau daya ne zaku min uzuri! na rayu ne wa yankina inda nayi aikin tuƙuru da jinina da lafiyata! naje na haƙo abunda na binne duk aljanu da mayun da na ɗaure tass zasu kunce, me ku ke tunani zai faru da iyalin da nake da shi a halin yanzu?” Baffa ya faɗi yana fashewa da kuka yana dukawa, jikinsu ne ya yi sanyi sosai, yayinda Arɗo ya dago Baffa yana rarrashinsa inda sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori suka hau ba shi hakuri tare da nadaman ganin laifinsa, Arɗo ya ce
“Kayi hakuri Magaji, yanzu abunda za ayi a rufe wannan maganar, Allah ya kaimu gobe Innu Maciji ya zo ya warware mana wannan sarƙaƙiyar” Sarki Chubaɗo ya ce
“Kowa zai iya kama gabansa”