AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

    Da kaɗan-kaɗan aka fara watse wa, Arɗo da Baffa Mandi da Baffa ne suka fara tafiya, Baffa Mandi ya ce
“Amma na rasa me yasa Magaji kake yawan maganar Banju” Baffa ya ce
“Sabida ni kaɗai nake ganin abunda nake gani a gidana” yana gama faɗin haka bai jira amsarsu ba ya yi gaba, Arɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce
“Mandi, akwai abunda yake damun Magaji” Baffa Mandi ya ce
“Nima haka nake gani, amma anya baya da nasaba da yaransa da ake yawo dasu ake zarginsu kuwa? A gaskiya Magaji ya yiwa yankin kwana hidima bai kamata a dinga masa haka ba”
“Gaskiya kam hakane” tafiya sukeyi a hankali suna tattaunawa, Baffa kuma hanyar gida ya ɗauka.

     ????????????????

Zaune ta sameta a rafin jimulo, ita ma zama ta yi kusa da ita ta ce
“Azima tambayarki na zo yi”
“Wai ni Aziza me yasa kika rainani ne? Ba nice gaba da ke ba?” murmushi Aziza ta yi ta ce
“Au haba dai da gaske? Rainin babu dadi ne? To haka iyayenmu suke ji a ransu idan kika musu, balle ni da ba ki bani ko da kwana daya bane, kawai iskar duniya kika rigani shaƙa” Azima ta kyalkyale da dariya ta ce
“Macijiya Aziza me ya kawo ki wajena?”

Kallonta Aziza ta yi ta ce
” ZAREN SAƘAR DANA! WA ZA KI KASHE DA SHI!?” sake kyalkyalewa da dariya Azima ta yi ta ce
“Idan naki faɗi fa me zakiyi?”

     “Sai na gwada ta wata hanyar!” Aziza ta faɗa tana mikewa tsaye, da sauri Azima ta mike ta ce
“Muje zuwa” tana gama faɗi ta hau ajijiya, Aziza na tsaye tana kallonta.

      ????????????????

COMMENT AND SHARE

BY
MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

IDAN AKA CE ƘAWANCE ANA NUFIN AMINTAKA! WANDA WANNAN AMINTAKAR WATA DANƘO CE MAI MANNUWA,ANA SAMUNSA NE IDAN AKA SAMU YARDA DA AMANA! IDAN NA KIRAKI DA SUNAN ƘAWATA BAI KAI INDA ZAN NUNA YADDA NAKE YINKI A CIKIN RAINA BA, HAKIKA MU DIN BA IYAKAR KAWANCE BANE,INAJINKI TAMKAR WACCE MUKA FITO CIKI DAYA,INA MIKI SON SO SABIDA ALLAH! ALLAH YA BAR MINKE ƘAWALLITA RASHEEDAT USMAN UMMU NASMA&NASREEN ALLAH YA ALBARKACI ZURI’ARMU ALLAHUMMA AMIN, INA KU KE MAKARANTA? UWAR NASMA TA YUNƘURO FA A BOOK DINTA MAI SUNA GELLE ‘BINGEL WANDA ZAKU SAME SHI CIKIN FARASHI MAI SAUKI, KU NE ME NI TA LAMBATA DAN ISA GA FASIHIYAR MARUBUCIYAR KAI TSAYE, KARKU BARI A BAKU LABARI, SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

FREE..
????️==1️⃣7️⃣↪️1️⃣8️⃣

A wani ƙasurgumin jeji Aziza ta tsinci kanta, jeji mai cike da wani mugun duhu da abubuwan tsoro tare da wasu mugayen halittu marasa kyawun gani da ban tsoro, haƙiƙa ganin wa innan abubuwa sun tsorata Aziza, amma tunowa da maganar Inno Fandi da cewa kar ta tsorata yasa ta takure tare da tattaro jarumta, ta hau tafiya, tare da furta kalman “makarin zaren saƙar dana!” wani sowa ne taji na tashi ta tsakiyar kanta da wani irin mugun jijjiga nan wasu halittu suka yi sama da ita, saura qiris Aziza ta saki ihu amma kuma ta daure tana karanto dukkan adduar da ya zo zuciyarta, nan halittu suka dauketa suka kara yin sama da ita suka hau tafiya da ita a cikin duhu,amma duk wannan duhu ba shi ya hanata ganin mugayen halittu marasa kyau da ban tsoro ba.

     Wa inda suka dauketa basu ajiyeta a ko ina ba sai a gaban wani katon halitta wanda bata san dame zata fasalta halittarsa ba sabida tsananin muni da girmarsa, ana ajiyeta muryar wannan katon abun ya ce
“Keeeee! Me ya kawoki jejin lore!!!” a yadda muryarsa take ɗan adam idan ya jita ya ci ace ya mutu tsananin amo marar daɗi da kaifi, cikin dakiya Aziza ta ce
“Makarin zaren saƙar dana, shi nake so” shewa wannan halittar ya yi,sannan ya ce
“Ya matsayinki yake a halittu!?” 

      ” NI MACIJIYA CE!” Aziza ta bada amsa, wannan halittar ya ce
“Ke ba iyakar macijiya ba ce, akwai wani sirri a tattare dake, dan haka ko ba mu baki makarin zaren saƙar dana ba,kaifin gubar dake jikinki zai iya ƙonasa! Amma kasancewar sau daya tak! Muke bada alfarma zamu baki taimako guda daya, zamu ƙara miki karfi, da kinje ki hurawa zaren wuta ta idon ki zai ƙone ƙurmuss! Ga wannan” ya faɗa yana daukar wata kyakkyawar dutse mai cike da hasken gaske ya hura mata shi ya shige ta goshinta, abun na shiga jikin Aziza sai da ta girgiza ta yi kamar zata faɗi amma ta yi iyakar iyawarta bata faɗi ba,dama tana tsaye ne ita ba a sama ba ita ba a kasa ba, abun na shiga jikin Aziza nan ta kalli fatar jikinta ta ga yana sab’ulewa har yana komawa wata fari-fari, kafin ta gama dawowa hayyacinta tuni ta fara rikiɗewa tana komawa macijiya, nan ta zama wata shirgiɗeɗiyar macijiya mai cike da abun tsoro, nan aka hau guɗa wanda yasa duk jejin lore ya dauka, kafin wannan katon halittan ya ce a maidata gida lafiya, nan suka fizgi Aziza,wacce tunda suka fizgeta bata kara sanin ina kanta yake ba, sanyin asuba ne ya farkar da ita,tana buɗe ido ta ganta a kofar gida, saurin tashi ta yi tana karkaɗe jikinta, nan abunda ya faru a daren jiya ya hau dawo mata, lallai kam jejin lore ba jejin mutane bane, da kyar ta saita kanta jin yadda jikinta ke mata ciwo, da sanɗa ta shiga cikin gida, tana shiga Baffa na fitowa daga kewaye ya yi alwala zai je masallaci, ya ce
“Aziza har kin farka? To shiga ki tada Hajjarku sannan ki tashi Azima su yi sallah”
“To Baffa” Aziza ta faɗa ta shiga ta tada Hajja sannan ta fito ta shige bukkarsu, ko da ta shiga bata gan Azima ba, a ranta ta ce ko ina taje oho mata, kayanta ta ajiye sannan ta fito ta yi alwala ta yi sallah ta jima tana addua sannan ta tashi.

    Abu na gaba da zata yi shine daukar zaren saƙar dana taje ta kona shi, to amma abun tambayar a nan shine a ina Azima ta ajiyesa? “zaki iya dubawa ki gani ta tafin hannunki ai an baki karfi a daren jiya a jejin lore” wata zuciyar ta bata amsa da haka, da sauri ta buɗe tafin hannunta na dama tasa hannun hagunta tana shafe tafin hannun daman tare da lumshe ido, nan ta ga ashe ma a cikin kayanta Azima ta ajiye zaren saƙar danar, tasan tabbas Aziza sai ta binciko,kuma duk bincikenta ba zata duba kayanta ba tunda ba zata yi tunanin zata saka a ciki ba, da sauri Aziza ta buɗe ido tana fadin “lallai Azima ke shaiɗaniya ce! A cikin kayana kika ma ajiye?” da sauri ta wargaza kayanta ta dauki zaren wanda Azima ta saƙa shi ya yi tsayi, lullubi ta yi ta boyesa a cikin mayafinta ta fito a hankali dan gari ya yi haske, har ta kai bakin kofa zata fita ta ji Hajja na kwala mata kira da gudu ta fice dan bata son ta rasa wannan damar, jejin kwana taje ta ajiye zaren bayan ta duba babu kowa a wajan, da ido ta kalli zaren yayinda idon nata ya koma jajur kamar garwashin wuta,nan wani jar wuta ya fito daga idonta ya kama zaren,nan zaren ya kama da wuta har yana wani irin ƙara passpasspass! Da sauri Aziza ta ja da baya, nan zaren ya ƙone ƙurmuss! tokar Aziza tasa hannu ta shafe shi ya b’ace nan ta sauke ajiyar zuciya mai karfin gaske tare da fashewa da kuka tana zubewa a kan guiwowinta tasa goshinta a kasa ta yi sujjadar shukur,  ta yi tsammanin ta kashe wannan bala’in bata san wanda yake shirin ci ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button