AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????
AZIMA.
tun fitarta a gida tana kwance a kan bishiya a macijiya tana jiran isowar Innu maciji, sai bayan da garin Allah ya fara wayewa ta ga wasu yan matasan samari biyu sun zo sun tsaya a jikin bishiyar da take kwance, dayan ya ce
“To ma ban da abun Mai Unguwa taya zamu iya kare Innu Maciji da za a wani turo mu dan mu tarbesa”
“Nima dai abun da na gani kenan” saurin zare ido Azima ta yi ta kallesu da kyau sannan ta yi murmushi
“Ohhho kenan yan fadar mai unguwa ne! Aiko su ya yi, shin na bar ma su bada labari ne? Idan kuma suka tona min asiri fa?” nan ta haɗe rai tare da sulalowa daga bishiyar ta zama mutum, hannu ta miƙa sama sai ga kwaryan nono, murmushi ta yi ta buɗe kwaryan wanda yake cike da nono kindirmo fari sol abun sha’awa ta watsa dafi a ciki sannan ta gyara mayafinta tayi lullubi ta rufe fuskarta ta nufi inda suke, cikin karairaya ta musu sallama, su kuwa sun ga ƴar budurwa har rige-rigen amsawa suke yi,cikin harshen fulatanci suke magana ta ce musu
“Ga fa nono, daga ina ku ke da sassafen nan haka ku ka zo ku ka zaune a tsakanin yanki?”.
“Wlh mai unguwa ne ya aiko mu, kin san ai masifar da ake fama da shi a yankin nan na macizai, to yau Innu Maciji zai zo wanda yake yankin ja’i shine mai unguwa ya aiko mu dan mu tarbesa,kin san kwanaki da Jarman macizai ya zo gawarsa kawai muka gani, kai duk wannan macijin da yake kisan nan ko take kisan nan ko humm idan Innu Maciji ya zo zan ce ya bani dama na kashesa da hannuna” cije baki Azima ta yi ta ce “da gaske?”
“Aradun Allah kuwa! Sanda zan sha na dinga roɗewa macijin kai har sai ya koma ga Allah” damƙe hannu Azima ta yi jin yadda ranta ya b’aci zuciyarta na tafasa amma ta daure tare ta k’wak’ulo murmushin mugunta ta ce
“Ai kuwa nima ina da wasu sirrika a kan macizai, kafin na gaya muku ga wannan nonon ku sha” ta fada tana tura musu kwaryan, dayan ya ce
“Allah sarki! Ashe kin san yau da yunwa muka tashi, ga shi kafin mu karya karin kumallo aka turomu yanki” murmushi kawai Azima ta yi ba tare da ta sake magana ba, nan suka buɗe nonon nan suka hau sha, sai da suka shanye tass har suna mata godiya, Azima ta kyalkyale da dariya tare da yaye mayafin fuskarta nan blue eyes dinta ya bayyana, tare da rikiɗewa ta hau komawa macijiya, tsananin tsoro da firgici yasa suka kasa motsi illa junansu da suka rungume gagam!, bayan Azima ta zama macijiya sannan ta koma ta zama mutum ta matso kusa dasu ta duka ta ce
“NI CE AZIMA MACIJIYA! WACCE DUK KASHE-KASHEN DA AKE YI NI NA KE YI! NI! NI! NI CEEEE! SANNAN KU TAKU TA KARE DAN DAGA NAN BABU WANDA ZAI MOTSA A CIKINKU, DAN KUN SHA GUBANA” tana gama faɗi kuwa suka hau aman jini, su na riƙe wuyarsu tsananin azaba, jini na fita ta baki da hanci, suna birgiman fitar rai Azima na ta sheƙa dariya, da haka har suka daina motsi, bayan sun mutu ta kwashesu ta maida su gefe ta ajiye sannan ta ci gaba da tsumayin jiran isowar Innu Maciji, ba jimawa sai ga shi nan kuwa ya yanko a kan dokinsa, daka gansa ka ga basamudan bafulatani mai ji da kansa, wuyarsa rataye da maciji, Azima na ganinsa ta hau murmushi tare da gyara lullubinta ta zo ta tsaya a kan hanya, (ga Azima ga Innu Maciji, ya zata kaya?).
Kamar yadda ta yiwa jarman macizai haka ta yiwa Innu Maciji, shi ma kalar tambayar da jarman macizai ya mata shi ya mata
“Mutum ko aljan?” murmushi ta yi tare da fadin
” RUWA BIYU!” sannan ta juyo gami da yaye mayafinta, Innu Maciji na ganin kwayar idonta nan ya sauƙo da sauri tare da zare takwabinsa yana fadin
“Keeeee!” haɗe rai ta yi ta ce
“Ajali ya kiraka!”
Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce
“Kina tunanin zan mutu a hannunki ne?”
“Ashe dai baka cika ba! Tunda har ba zaka iya bambance wacece ni ba, amma ina so ka sani ba zaka shiga yankin nan ba,kamar yadda ba zaka koma yankinku ba” tana gama fadi ta yi kansa tare da komawa macijiya,ganin haka yasa Innu Maciji saurin b’acewa dan ya ga da karfinta ta nufosa, Azima gani ta yi Innu Maciji ya b’ace yasa ta koma mutum tana ta kalle-kalle,ji tayi an tokareta ta baya nan ta fadi kasa ta bugu tukunna Innu Maciji ya bayyana yana dariya yana kallonta ya ce
“Ba mamaki baki da labarin waye Innu Maciji ko? Humm ni ne nan mai fada da aljanu da mayu, sabida shaharata yasa sadda aka raba kambun girmamawa ni ne nan nayi na daya, dan haka sai na baki wahala! Na galabaitar dake sannan na daukeki na kaiki wajan mutanen yankinku na nuna musu ke!” yana gama fadin haka ya zaro wani dogon igiya ya naɗe Azima da shi, ya hau bugunta tare da watsa mata wani ruwan magani wanda da ya watsa mata zata kurma ihu, fatar jikinta ya koma blue sabida karfin dafinta ne ke raguwa, haka Innu ya ci gaba da ganawa Azima azaba wanda izuwa yanzu fadin halin da take ciki b’ata lokaci ne, sai da ya ga bata iya motsin kirki sannan ya kyaleta yana shirin daukarta ya ɗorata a dokinsa yaje ya nunawa jama’ar yankin kwana, har ya dauketa Azima ta buɗe ido a galabai ce, a ranta ta ce
“Yanzu idan aka kaini Baffa da kansa na san zai kasheni! To ina kuma daukar fansata!? Inaaa ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan bar yankin nan ba, ba tare da burina na son maida yankin kwana maƙabarta ba, sannan ba zan bari na mutu ba tare da na shiga cikin gari ba” tana gama fadi ta yanki gashin kanta ta haɗiye ta rintse ido ta mamayi Innu Maciji wanda ya sab’ata a wuya yana shirin ɗorata a kan doki, nan ta zama macijiya tasa jelarta ta shaƙe wuyar Innu Maciji, shaƙa bana wasa ba, sannan tasa hannu ta b’abb’alle guru da layoyin dake jikinsa ta zubar, sannan tasa ihu ta koma macijiya gaba dayarta ta hau sarensa,duk yadda Innu Maciji ya so kwacewa ina hakan bai samu ba, Azima sai da ta ga Innu Macijiya ya zube kasa babu rai a tattare da shi sannan ta sulale gefe ta koma mutum tana sauke ajiyar zuciya idanunta jajur, kallon Innu Maciji take yi na wasu lokuta sannan ta ja samari biyun da ta kashe ta haɗa da innu maciji sannan ta bar wajan.
????????????????
Bayan Aziza ta koma gida aikin gabanta ta ci gaba da yi, ko kaɗan bata tambayi ina Azima take ba, nan ta yiwa Hajja shara da girki sannan ta hau ɗibar ruwa, sai da ta cika babbar randar kasarsu sannan Hajja ta ce
“Ayye Aziza ba za ki huta ba?” murmushi ta yi ta ce
“Hajja hutuna shine naga Allah ya rabani dake lafiya” Hajja ta yi murmushi jin dadi tare da sa mata albarka,nan suka zaune hira suka shantake sai zuwa anjima Hajja ta ce
“Wai ni ina Azima ne kam?”
“Wa ya san mata” cewar Aziza,
“Bata rafin jimulo ne?”
“Ni dai wlh Hajja har na gama jido ruwa ban ganta ba, da ace tana can dana ganta”
“Ikon Allah!” Hajja ta fada, Aziza ta ce
“Hajja miye amfanin damuwa a kan Azima ita da ba jaririya ba,duk inda taje zata dawo ai” Hajja ta ce
“Hakane” suka ci gaba da hirarsu, sai zuwa can Aziza ta ce
“Hajja wai ina Baffa? Tun fitarsa sallar asuba fa bai dawo ba ga shi yanzu ana neman lokacin azahar” Hajja ta ce
“Oh! Kinga na mance ban gaya miki ba, ai suna can fadar sarkin fulani, Chubaɗo”
“Wani abun ake yi ne?” Aziza ta tambaya cikin rashin sani tana kallon Hajja, Hajja ta ce
“E lafiyar kenan, kin san ai an yiwa yankin ja’i aiken wasikar taimako, har Innu Maciji ma ya ce zai zo yau, to jiran Baffan naku nake yi idan Innun ya iso zai zo ya gaya mana muje can fadar sarkin fulani”