AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

      @@@@

Maga Isar da Sakon yankin kwana ne yake karantawa fada sakon yankin ja’i kamar haka
DAMA MUNYI MAMAKI ACE KUNA DA MUTUM A YANKINKU KAMAR MAGAJI BAWA AMMA ACE KUN ZO YANKINMU NEMAN TAIMAKO DA INNU MACIJI! HAKIKA MUMA MUN ZAMA SHASHASHU DA MUKA YARDA DA KUDIRINKU! BAYAN MUN SAN DA CEWA KU ƊIN ABOKAN GABANMU NE NA TUN TULI-TULI! A KODAYAUSHE KU YANKIN KWANA KUNA SO KU DINGA NUNAWA KUN FI SAURAN YANKUNA! TO MUNA SO KU SANI KU KARA SANI, LOKACI YA YI DA ZAMU MAIDA YANKIN KWANA BABBAR MAƘABARTA! DAN KUWA MUNYI SAƘO YANKIN JIMO MUN ZUGASU NA JARMAN MACIZAI DA KU KA KASHE! TUN KAFIN KUYI AIKE YANKIN TUDU MUN RIGAKU DAN BA ZAMU YARDA DA KASHE MANA INNU MACIJI DA KU KA YI BA, MUN GAYAWA YANKIN TUDU KUN KASHE MANA INNU MACIJI SANNAN BA MAMAKI KU MUSU AIKE A BAKU IRO MAGANIN MACIZAI TO MUN TOSHE WANNAN HANYAR DAN MUN TONOWA SARKIN TUDU TSOHON RAUNIN DA YANKINKU SUKAYI MASA TA HANYAR KASHE MASA GUDAN JININSA, DAN HAKA KU FARA SHIRYAWA TARBAN YAƘI NA YANKUNA GUDA UKU, YANKIN JA’I: YANKIN JIMO: YANKIN TUDU: SAKO DAGA YANKIN FULANIN JA’I.

     Maga Isar da sako yana gama karantawa aka hau kallon-kallo, Mai Unguwa Ori ya ce
“Yaƙi da yanki uku a kan yankin daya?”

“Kuma lokaci daya?” cewar Sarki Chubaɗo,Arɗo ya ce
“Mu dai mun san bamu aikata komai ba, mu sa a ranmu wannan wata jarabawa ce daga Allah, kuma yana sane damu, shi zai kawo mana dauki, kar mu ce zamu yi wani shirin yaƙi, mu zubawa sarautar Allah ido” kowa ya amsa da haka ne sannan kowa ya watse cike da alhini.

       ????????????????????

Azima na kwance a kan bishiya rabinta mutum rabinta macijiya, jelarta na lilo a ta saman rashen bishiya fuskarta a haɗe har gefe da gefe ya yi jaa! Idonta kuwa ya kara rikiɗewa ya rine ya koma blue sosai harta fari babu, Aziza tana zuwa jejin hayi jelar Azima ta fara hangowa, saurin karasowa ta yi ta ce
“Azimaa!?” jin muryar Aziza yasa Azima sulalowa tare da komawa mutum, a fusace tayo kan Aziza tana isowa gabanta kafin ta yi mata magana Aziza ta yi saurin dafe goshin Azima nan take taji abu ya shige mata kai sai da ta girgiza.

     Ganin yadda Azima ta tsaya yasa Aziza faɗin
“Azima lokaci ya yi da zaki saduda! Ki dakata haka” murmushi Azima ta yi tana yiwa Aziza kallon baki da hankali
“Ni kike cewa na saduda? To naji zan saduda, amma bayan na kashe Baffa!” ta faɗa tana cije baki, Aziza ta ce
“Wai ke wace irin dabbace Azima?” murmushi Azima ta kuma yi ta ce
“MACIJIYA! ina kina tambaya ne wace irin dabba ce ni? To ni Macijiya ce kamar ke amma bambancin shine ni muguwa ce ke akasin haka! Har yanzu ban huce da abunda kika min ba, ki bar ganin kinsa jikina ya yi sanyi kin kafar min da dafina! Ba shi zai dakatar dani ba, na iya yau ne kawai, amma gobe zan haɗa da kisan da banyi yau ba!” Aziza ta jinjina kai ta ce
“Kin sha fadamin idan na isa na dakatar dake! Ni kuma na sha fada miki cewa bazan bar hakan ta faru ba, shine zan kara nanata miki, ba zan bar hakan ta faru ba! Dan haka muje gida, kafin Hajja ta titsiyemu da tambaya!” a hankali Azima ta juya tana dafe kirjinta dan abunda Aziza ta tura mata ya shigeta sosai, a hankali suka jera suna tafiya dan Azima na da bukatar ta kwanta dan jikinta da ya mutu, sabida abunda Aziza ta tura mata a hankali yake bin jikinta yana kashe mata shi, dan makarin dafi ta tura mata.

       Da haka suka iso kofar gida Aziza ce ta fara shigewa da sallama ta samu Baffa da Hajja suna zaune yana labarta mata wasikar yankin ja’i wanda kaff abunda Baffa ya faɗi a kunnen Azima, a tana rarrafawa da kyar amma wani dadi ne ya mamaye zuciyarta nan ta hau murmushi tare da fadin
“Yankuna uku zasu yaƙe yankin kwana? Wayyooo Dadi!bari na ɗan daga kafa dan ganin yadda za a shafe yankin kwana idan ya so na kashe Magaji Bawa daga baya!” ta faɗa gami da sallama ta shiga gidan, Hajja ta ce
“Azima ina kika je ne? Ni anya jiya na ganki kuwa? Yana ganki haka kamar wacce bata da lafiya?”

“Kin ganni mana Hajja! Ko dai wannan bala’in ne yasa kanku ke da Baffa ya kama da wuta!? Sannan da kika ganni haka ba wata matsala bace babba kaina ke ciwo, da nayi bacci na farka zan dawo dai-dai” Azima ta fada tana kallon Baffa, da ido Baffa yake bin Azima yayinda take yi masa wani irin kallo, Hajja ta ce
“Allah ya kyauta, jeki kwanta” Hajja ta shige bukka, Azima ta juya kenan zata shiga bukka idon Baffa na kanta dan ya kasa kauda ido a kanta, wuyarta taji ya mata ƙaiƙaiyi tasa hannu ta sosa, tana sosawa sai ga sab’ar maciji ya fadi carab a idon Baffa, wani wawan firgita Baffa ya yi,ya tashi jikinsa na rawa ya karasa ya dauki sab’ar yana kalla,saurin girgiza kai ya yi yana fadin
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!! Me hakan ke nufi?” jikin Baffa ya yi mugun sanyi dan ya tsorata ba kadan ba, bukkarsa ya shige yana jeka ka dawo dauke da fatar a hannunsa, cikin rawar murya ya ce
“me ya kamata nayi? Dole na haɗa maganin ganowa idanuna, amma kafin na samu furen surfa sai naje jejin gangare, kuma kafin na dawo sai na samu kwana biyu sabida dogon tafiya ne ban ci ta zama ba, In sha Allahu zan tafi gobe” yana gami fadi ya fito ya shiga bukkar Hajja ya gaya mata gobe da safe zai tafi jejin gangare Hajja ta ce
“Me zaka je yi?”
“Akwai maganin da nake son haɗawa ne, kuma furen da ganyen dole sai naje jejin gangare”
“To Baffa yan biyu Allah ya kaimu lafiya” Baffa ya amsa da amin ya fice, bai zarce ko ina ba sai wajan Ardo bai boye masa komai ba kasancewarsa mahaifinsa ya gaya masa komai, sosai hankalin Arɗo ya tashi ya kallesa ya ce
“Magaji bana so ka gaya ma kowa wannan batun ka ji ko? Har sai ka tabbatar” Baffa ya gya ɗa kai cike da damuwa, nan suka ci gaba da tattaunawa a kan lamarin.

    ????????????????????????

COMMENTS AN SHARE
BY MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

STILL FREE..
????️==1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣

Amma bata ga inda Azima ta yi ba, rafin jimulo ta je amma ba Azima bare mai kama da ita, hankali tashe Aziza ta hau neman Azima amma bata ganta ba, jejin kwana ta nufa ta hau dubata amma bata ganta ba, riƙe kai Aziza ta yi tare da furta “YA ALLAH! dabadin ace kisan kai haramun bane babu abun da zai hanani ban kashe kanmu a yau ba kowa ya huta, wannan wani irin bala’i ne haka? Ya Allah ka yaye mana, Allah ka bani mafita ka nuna min haske, Ya Allah ka nuna min hanya! Ya Allah ni dai bana da masaniya a kan fansar da Azima take dauka, dan a iya sanina banga wanda ya mana laifin komai ba, Ya Allah idan ita haka halinta yake Allah kai kasan yadda zakayi da ita, Allah ka taimake Baffana da Hajjata da jama’ar mahaifata! Ya Allah ka karesu daga dukkan sharri!” Aziza ta karasa adduar hawaye masu zafi suna wanke mata fuska tare da jinginuwa a jikin bishiya, wani nishi taji na tashi a bayanta da sauri ta buɗe idonta da ta lumshe tana waige daga ina nishin ke fitowa, taji ashe ta bayan bishiyar ne,saurin leƙawa ta yi nan ta iske wata budurwa kwance bakinta sai  jini ke bulluƙowa, cike da tashin hankali Aziza ta karasa ta ɗagota, tana dudduba meyasa meta,goshinta ta kalla ta ga bakin maciji wanda yake sara ne na Azima, ihu Aziza ta yi tana ajiye kan budurwar a kasa ta tashi da sauri tana ja da baya ta kuma sakin wani mahaukacin ihu tana furta “AZIIIMAAAAAAA!!!?” da gudu ta bar wajen dan babu taimakon da zata iya yiwa budurwar dan kuwa gubar ya shige mata jiki sosai dan harta idonta da tafin hannunta sun koma blue.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button