AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hajja ta bude baki za ta yi magana da sauri Aziza ta ce
“Dan Allah Hajja karki ce komai, Azima bata sallah bata salati bata Azumi duk wani aikin ibada bata yi,na gaji da miki karya Hajja, bazan iya jure miki karya ba!” tana gama fadi ta fice da gudu da kuka.
Aka bar Hajja da kakkarwar jiki.
@@@@@
Da yamma sai ga wasika daga yankuna uku izuwa yankin kwana, zasu kawo musu farmaki gobe da safe, hakika wannan sako ya hautsine hankalin jama’ar kwana inda mata da dama har ma da mazan wasu suka fara kuka, sarki Chubaɗo da mai unguwa ori suka ce ga shi Magaji baya nan, kuma babu halin yi masa saƙo har sai ya dawo, saukinta ma Garkuwa ya ɗan samu lafiya, kafin kace me Sarki Chubaɗo ya bada umarnin ayi shela a yankin kwana gabadayanta za a kawo farmakin yaƙi gobe kuma yankuna uku,dan haka kowa ya kasance cikin shiri amma bana tarban yaƙi ba.
@@@@@@
Hajja da Aziza sun kasa zaune sun kasa tsaye sabida tashin hankali sai jeka ka dawo suke yi a tsakar gida amma Azima na zaune hankali kwance tana fizgar dogon gashinta, Aziza ce ta kallenta ta ga babu alamun damuwa a tattare da ita,cikin haushi da tsanar Azima da ya fara ɗarsuwa a zuciyarta ta ce
“Wai ke Azima wace irin dabba ce ke ana maganar kawo farmakin yaƙi amma kina zaune kina tsifar kai?”
“Macijiya!” Azima ta faɗa ba tare da ta ɗago ta kalli Aziza ba, Hajja ta juyo a firgice ta ce
“Ma mai kika ce Azima! ?” tana shirin kara nanatawa Aziza tayi saurin faɗin
“Mahaukaciya kawai!”
“Ga ki kuwa babbar mahaukaciya!” Azima ta faɗa tana dagowa a fusace.
“Dan Allah fadan ya isa haka!” Hajja ta katsesu,
“Kuyi ta addua kawai Allah ya bamu mafita yafi wannan fadar naku” ko uhum basu kuma cewa ba.
????????????????
Da washe gari kamar yadda sako ya iskesu haka kuwa ta kasance inda yankin ja’i da yankin jimo da yankin tudu sukayi cincirindo sun zo yaƙar yankin kwana, amma abun mamaki babu wani daga yankin kwana da ya dauki makami, abun ya basu mamaki, Arɗo shine wanda ya fito ya fara magana kasancewarsa Babba, tsohon bafulatani mai dattako
“Mu ba zamuyi yaƙi daku ba, idan har kuna so duk ku sa takwabi ku kashemu! Har ga Allah munyi imani wannan ita ce kaddararmu! Bamu kashe Innu Maciji ba, a ranar da aka kashe Innu muma munyi rashin mutane a yankin nan har mutum sha huɗu, haka ma jarman macizai, sannan sarkin fulanin tudu bamu aikata muku komai ba kawai neman fitina kukeyi,idan kuma yaronka da aka kashe a yankin nan ne laifi ya aikata aka masa hukunci, na rantse da wanda ya busamin numfashi idan har aka samu ɗan wani yankin kwana da laifi makamanciyar wanda ɗanka yazo yankin nan ya aikata wlh mun yarje muku ku fille kansa ku kawo mana kamar yadda mukayi, ba a barin laifi a ɗoran kasa, dan ba a san mai zai kuma aikatawa a gaba ba, mu sabida muna bin al’ada da ibada shiyasa yankinmu ta yi baƙin jini a wajan sauran yankuna, idan har maganar da nayi baku gamsu ba kuna iya shafemu a doron kasa ko kwayi farin ciki” Arɗo na gama fadi jama’ar kwana suka miƙa wuya,ganin haka yasa yankin jimo jikinsu yayi sanyi suka ce ba zasuyi yaƙi da yankin kwana ba,nan take suka juya, yankin tudu da yankin ja’i kuwa sunce suna nan, sai sun shafe yankin kwana.
@@@@
Gudu Baffa ke yi a dokinsa dan haka yake ji a jikinsa mahaifarsa babu lafiya.
A kwana kuwa ganin yadda yankin ja’i suka fara zubar da yara da manya ta hanyar saresu da takwabi yasa garkuwan fulanin kwana cewa Sarki Chubado da Ardo
“Ranka ya dade, hakika ba zamu tsaya a shafemu ba tare da mun sa hannu ba dan bamu aikata laifi ba, burin yankin ja’i shine su ga sun shafe yankin kwana, dan haka kowa ya dibo makamai mu gwabza tunda haka suke so” mai Unguwa Ori ya ce
“Tabbas hakane” nan garkuwa ya bada umarnin a dauka takwabi a fara maidawa yanki biyu martani.
Duk wannan tarzoma da akeyi Azima na saman bishiya tana kallo tana dariya, Aziza ganin kisan da ake yiwa mutanen yankinta ya yi yawa ne ya sa ta fadi a ranta “inaaa! Burin Baffa shine ya ga ya mutu ya bar yankinsa lafiya, dan haka dole ne na dakatar da yaƙin nan ta ko wani hanya in ba haka ba, tabbas yau babu sauro da zai rage a yankin nan” ta kalli Hajja dake tsaye tana kalman shahada dan yawancin mutane sun sadakar da zasu rayu ta ce
“Hajja ina jin fitsari zanje gida na dawo” ta karasa fadi tare da juyawa,saurin kamo hannunta Hajja ta yi ta ce
“Aziza bakki hankali ashe ban sani ba?kina ganin yadda ake zubar da jini tamƙar ana ɗibo ruwa a rafin jimulo ne ake watsawa kice zaki koma gida kiyi fitsari? Idan kika bincika wasu a nan har da kashi sukayi a jikinsu,dan haka Aziza yi fitsarinki kawai a jikinki, gwanda mu tsaya ta nan idan har Allah yasa aka gama da sauran kafin a iso kanmu,idan kuma Allah yasa Baffanku ya dawo a kan lokaci to, dan shiyasa nace miki mu tsaya a nan sabida ga hanyar da zai fito nan” Hajja ta faɗa tana kara riƙe hannun Aziza, girgiza kai Hajja ta yi ta ce
“Hajja to ni kin riƙeni babu fa Azima a nan” da sauri Hajja ta ce
“Na shiga uku! Azimaaaa!?”
“Kwantar da hankalinki Hajja bari na je nayi fitsari sai na dubota mu dawo tare”
“To dan Allah Aziza ki kula,ki min alkawari zaki dawo lafiya?”
“Na miki alkawari Hajjata zan dawo lafiya” sai da Aziza ta faɗi haka kafin Hajja ta saketa,da gudu Aziza tayi hanyar gida dan ta shirya ta dawo ta tare yaƙin.
@@@@
Haka Baffa ya shigo yankinsa ya samu gagarumin yaƙi, amma da shike baya da lokacin tsayawa gida ya wuce kai tsaye ya haɗa maganin furen surfa, sannan yaje ya kirawo Hajja a inda ya ganta sadda ya shigo, amma ita bata gansa ba, yake tambayarta ina Aziza da Azima? Hajja ta ce
“Aziza tace min zata zo gida ba mamaki tana kewaye cikinta ya tsure sabida wannan tashin hankalin,Azima kuma ban ganta ba dan Aziza tace min idan zata dawo zata dubota su sameni a can”
Baffa ya ce
“Boye a can,ni kuma zan boye a nan karki kuskura kiyi magana kinji ko?” Hajja tana shirin tambayar Baffa me yake son yi ya ce
“Jumala karki tambayeni komai! Zaki ganewa idanunki!ke dai kiyi abunda na sakaki! Yaƙi kuma inada yaƙini a kan garkuwa zai tarewa yankin kwana tunda yasa hannu kafin na gama wannan binciken da zanyi, dan haka karki tambayi komai kawai je ki boye,kuma karki kuskure ki fito” Hajja ta amsa da to, maganin da Baffa ya haɗa ya kewaye kofar shigowa gida da shi, sannan ya zuba wani ya koma ya maqale, Azima dake kwance a jikin bishiya haka kawai taji kamar an tsikareta saurin saukowa tayi a saman bishiyar idonta ya kara canza kala nan ta nufa hanyar gida ba tare da tasan dalilin hakan ba wanda take ji kamar an saka mata kuran karfe ne yake janta.
@@@
Aziza ce ta fito daga kewaye idonta jajur alama ce na taci kuka, tana fitowa ta shige bukkarsu, Baffa dake maqale ta zanar kofar waje ya hangi Azima na tahowa tana layi, tana zuwa zata shiga gidan da aka yi wani sama da ita aka bugata da kasa, yayinda taji ko wani fata ta jikinta na mata zafi, ihu ta saka tana rirriƙe jikinta, ta kafarta ta fara rikidewa, wani wawan zare ido Baffa ya yi,yayinda yayi sumar wucin gadi, wannan shi ake kira tashin hankalin da ba a sa masa rana.