AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

   "Matso nan kusa dani Aziza karki ji tsoro" Malam Shadi ya fada yana kallon Aziza, a hankali ta taso ta matso kusa da shi ta duka, wani magani ya ɗiba a kasko ya watsa mata a fuska,ihu Aziza ta saka tana furta "Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah! Baffana zafii!!" abun tausayi, hawaye ne ya cika a idon Baffa yana ji kamar ya tashi ya fita amma ina ba hali, Malam Shadi yasa hannu ya damƙi goshin Aziza da karfi, murkususu ta hauyi tana son kwacewa amma ta kasa,rintse idonsa ya yi yana gane-gane da hange-hange, ya dau lokaci yana riƙe da goshin Aziza wacce ke murkususun azaba har sai da ta suma kafin Malam Shadi ya saketa, Baffa ya yi saurin taro 'yarsa ta fada jikinsa,jikinsa na rawa hawaye na zuba a idonsa ya d'ago ya kalli Malam Shadi yana fadin

“Malam me ya sameta?”

“Haba Magaji! Sai kace baka san yanayin aiki ba,ka kwantar da hankalinka zata farfado, amma gaskiya akwai babbar matsala wanda ba zan iya ce muku komai a kai ba, akwai aikin da nake so nayi cikin dare ina so na bincika na ga taya za a rabasu da mugun nan Banju, sannan Babban tashin hankalin shine ‘yar uwarta Banju ya jata sun bar al’ƙaryan nan,ina take? Ina za a ganta? Duk babu wanda ya sani” Arɗo da Baffa Mandi suka sharo zufar tashin hankali, Malam Shadi ya ɗora da cewa
“Babban damuwar shine abunda Banju zai ja Azima ta aikata,amma zanyi bincike a kai yau In sha Allah,ina dai a nan zaku kwana?” Baffa suka amsa da eh, sannan Malam Shadi ya kira wani almajirinsa yace ya kawo masa tarbama wanda yake na kara ne, bayan an kawo ya ce a shinfiɗe Aziza a kai, bayan Baffa ya kwantar da Aziza Malam Shadi ya kunna mata hayaki, sannan suka fita waje suka zauna suna tattauna yadda zasu yi a kan lamarin.

   ????????????????

Sarki Chubado ne da mai unguwan kwana ori suke tattaunawa a kan batun Azima da Aziza Macizai ne,suna ta alhinin lamarin, su biyu suke magana a kan cewa suna tausayawa Baffa, a garin yaya sai ga Salti ɗan gidan Jauro mai maganin yankin kwana yazo wucewa caraf a kunnensa, dan Salti ba dai gulma ba,nan yaji duk wani tattaunawa da Sarki Chubado da Ori ke yi a kan lamarin har da tafiyar da su Baffa suka yi yankin ja’o, da gudu Salti ya kwasa yana fadin zai je ya gayawa Baffansa dan yasan zai yi farin ciki da wannan labarin da zai kai ma sa.

  ????????????????????

Comments
Vote
By
Momyn Ahlan
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

INA GAISHEKU KYAUTA YAN PAID GRP MASOYAN……..BAN DAI KARESA BA KU KARASA DA KANKU

PAID.
????️==3️⃣1️⃣↪️3️⃣2️⃣

Sarki Chubaɗo cikin fushi ya kalli mutanen da suke wajan ya ce.
“Amma wallahi kun bani mamaki! Kuma kunji kunya! Yanzu akwai masifar da zata samu Magaji wanda har zai sa ku juya masa baya? Idan har ku wa inda ku ka zo bayan shekara ashirin baku san gwagwarmayen da Magaji ya yi ba, to ku wa inda ku ka zo kafin bayan shekara ashirin zaku ce kun manta da wannan halaccin ne? Dayawanku a nan wasunku basu da dangi kaff Banju ya kashesu! dabadin Magaji ba babu ko da ƙwaro da zai rage a wannan yankin!!” Sarki Chubado ya karasa da tsawa idonsa jajur dan ransa ya b’aci matuka
“A ce ina sarkin fulanin yankin kwana amma Jauro ya ja ku ba tare da sanina ba ku zo yiwa Magaji rashin mutunci da dibar albarka! Jauro ne sarkinku!! Na ce Jauroo neee sarkinkuuu!!!?” shuru jama’a suka yi masu zare ido da masu tsilli-tsilli da ido suna yi, Mai Unguwar yankin kwana bayan Sarkin fulanin kwana Chubaɗo ya dasa ayar tasa shima ya karbe da cewa
“Jauro dai mai maganin yankin kwana ne kamar yadda ku ka sani, amma a da kun san waye GARKUWAN YANKIN KWANA KAFIN A ƊORA GARKUWA NA YANZU!! TO GA SHI NAN SHINE DAI! MAGAJI BAWA!! kafin ya sauke duk wata baiwa tasa ya binne bayan yasha wahalan kama aljanu da mayu ya kullesu!! Ya sauka ne a kan matsayinsa da yake da shi bayan ya kashe Banju! Amma har kwanan gobe! kai ba ma kwanan gobe kawai ba! HAR GABAN ABADA BABU WANI GARKUWAN FULANIN YANKIN KWANA SAMA DA MAGAJI! SANNAN BABU WANI MAI MAGANI SAMA DA MAGAJI! Har ta Garkuwan fulanin yankin kwana na yanzu da Magaji yake tunkaho”

Garkuwan fulanin kwana na yanzu ya fito ya ce

“Tabbas hakane, da taimakon Magaji Bawa na zama Garkuwan fulanin kwana shi ya maidani mutum, gaskiya baku kyauta ba” wasu ne jikinsu ya fara sanyi ganin haka yasa Jauro ƙara tattaro sauran munafurcinsa dan shi baya so ace mutane su banzartar da maganarsa idan ba haka ba ba zai cika burinsa ba,baya so yaji sunan Magaji na daukaka! yafi so duk yankuna yadda ake kiran sunan Magaji Bawa! Magaji Bawa! ya kasance shi Jauro Mai Maganin yankin kwana shi ake kira ba wani Magaji Bawa ba, ace shine shahararsa ta kai inda yake so kuma yake bukata, saurin cewa ya yi
“Babu wani borin kunyar da za ayiwa mutane an dai cutar dasu! Wa inda aka kashe musu yara su ce mai? Sannan tunda daɗewa Magaji yasan yaransa Macizai ne amma ya boyewa mutane bai gaya musu dan yanzu yana da mugun nufi a ransa!”

   "Magaji baya da masaniya a kan cewa *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE* taya idan ya sani har zai barsu su yi kisan kai!? Da kake maganar su na kisa Aziza bata taba kisa ba,akasari ma ita dabi'un Magaji ne tattare da ita, ku a tsammaninku da Azima ce har kwa fara yi mata abunda ku ka yiwa Aziza? Inaaa! Da kafin mu iso wlh sai dai gawawwakinku!" cewar Baffa Mandi, jauro ya ce

“Owoohh! Kenan da saninku ma kamar yadda na faɗa! Jama’a kuna dai ji ko? An zalinceku an munafurceku an kashe muku! Kuma ta yadda zaku gane Magaji ya san yaransa Macizai ne shine basu zuwa bikin gargajiya ta al’adun fulani wanda ake gabatarwa duk shekara, sabida sun san a lokacin ana amfanin da magungunan macizai! Sannan……”

   "Ya isheka haka Jauro!!" Baffa ya katse Jauro jikinsa na rawa, ya tako ya zo gabansa ya ce

“Da ace da sanina yarana macizai ne da tuni na dauki mataki wani zancan 7ake yi yanzu ba wannan ba, a da nace maka muddun ka gano yarana macizai ne nina maka lamuni ka kashesu! Amma tunda na gano cewa ku ɗin ba mutane bane dabbobi ne wanda shanu ma sun fiku hankali ko da Azima da Aziza sun dawo yankin kwana duk wanda ya yi gigin taba min yara a lokacin zan basu umarni su kashe min koma waye!! Sannan ka zuba ido ka gani, zan maida yarana mutane ko da kuwa hakan zaiyi sanadiyar mutuwata, a yau kuna zaginsu macizai kuna ci min mutunci, amma ku sani ko nace kai jauro ko sani, MAGAJI BAWA KAFIN ALLAH NE BA KAFIN MUTUM BA! KO DA ACE MISALI BANA RAYE! AZIMA DA AZIZA SAI SUNANSU YA BUGA TAMBARI A YANKUNA BA MA IYAKAR YANKIN KWANA BA! KAMAR YADDA NA MAHAIFINSU NI MAGAJI BAWA NAYI! NA MAKA WANNAN ALKAWARI! BAIWA DA FARIN JININMU DAGA ALLAH NE KA ZUBA IDO KA GANI JAURO!!!” Baffa na gama faɗi ya bar wajan tare da daukar Hajja suka yi gida yana tunanin tashin hankalin da Hajja zata farka da shi, da fari yara macizai yanzu kuma babu su ma kwata-kwata, amma ya zata yi dole su rungumi kaddara.

     Bayan Baffa ya bar wajan Sarki Chubaɗo ya kalli Jauro ya ce

“Ka dai ji kunya wlh! Da ace nima tsoron kar nayi abun kunya ba wlh da yau a yanzu na koreka daga yankin kwana, ku kuma idan dai Jauro ne gaku ga shi,in dai ba a mutu ba to ba shakka ba a daina kallo ba, ba fata nake muku ba amma na tabbata akwai jarabawa,sannan Allah ba azzalumin bawansa bane, duk wani abunda ya sameku karku sake kuce zakuje wajan Magaji ya taimaka muku! kuje wajan Jauro ya taimaka muku, wannan umarnina ne a matsayina na sarkin wannan yankin!! Idan kuma na ga akasin abunda nace mutum zai fuskanci mugun hukunci!” Chubaɗo na gama faɗi ya yi gaba ya bar su a tsaye a wajan, wasu jikinsu yayi sanyi inda nadama ta kamasu wasu kuwa zuciyarsu kamar busashshen itace!.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button