AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????
Azima kwananta biyu tana tafiya kafin ta fito bakin titi, tana fitowa wani guɗa ta yi da dogon harshenta, duniya sabuwa! Tana nan tsaye a kan titi da lullubi tana tunanin hanyar da zata fara dosa, nan ta yanke shawara kawai ta bi dogon titi ta ga iyakar karewarsa, haka ta hau tafiya a tsakiyar titi tana murmushi, kamar daga sama sai ga wani mota ta yanko da gudu amma sai ganin yarinya ya yi tana tafiya akan titi sai horn yake danna mata amma a banza! Azima kuwa tunda farkon fitowarta kenan ba fahimta tayi ba, da kyar mutumin ya taka burki ya fito a motar gami da daka mata tsawa “keeeeeeee!!” wani tsayuwa Azima tayi tare da ware blue eye dinta, babu wanda ya taba mata irin wannan ihun, a hankali ta kara jan mayafinta ta rufe fuska sannan ta juya a hankali kanta a duke, mutumin kallon sama da kasa ya mata yana yatsine fuska dan ya ganta da shigar fulani ba mamaki irin kidahuman nan ne na jeji dan haka cikin izgilanci ya hau ta da zagi.
“Ke wace iriyar bagidajiya ce da ana miki horn amma da shike kin fito a cikin jeji baki ganewa kwakwalwarki a toshe yake kina tafiya a kan titi banza ballagaza daƙiƙiya ƙidahuma tunkiya!!” hakika zagin ya soki zuciyar Azima, zaro ido ta yi tare da yaye mayafinta rai b’ace cikin hausar da babu sosai a kan harshenta ta ce
“Ba dai tunkiya ba, sai dai MACIJIYA!????*” ta faɗi tare da komawa macijiya ba ta jira ya gama firgita ba ta kai masa sara a wuya nan ya fadi kasa yana shure-shure,komawa mutum ta yi tana dariya ta ce
“Kaina mutum na farko da na fara kashewa daga fitowata,hakan na nufin cewa zan sha jini da yawa kenan sabida mutanen cikin gari basu da ɗa’a,ni kuwa AZIMA MACIJIYA bana daukar wargi!” ta faɗi tana murmushin gefen baki ta leƙa cikin motar ta wargaza ta ga kuɗi ta kwashe duk da bata san amfanin me zasu mata ba, ta ci gaba da tafiya, ta yi tafiya sosai inda ta iske tasha wanda yake cike yake da jama’a a hankali ta ƙutsa kanta cikinsu tana ji ana ambatar sunayen garurruka, garin da taji ya mata masauki a kunneta shine *KANO TUMBIN GIWA KO DA MAI KA ZO AN FIKA!* murmushi ta yi ta kara nanata KANO ranta, sannan ta afka mota ta nemi can baya ta zauna tana murmushi yau burinta ya cika ta bar yankin kwana.
Kuɗi aka fara karba aka zo kanta, ana cewa kawo kuɗinki nan kuwa ta cire ta miƙa ba tare da tayi magana ba ko tasan nawa ta bayar ba,duk da zuciyarta na raya mata da sun isa kanon da zasuje zata kashe mutanen da suke motar!.
Bayan yan wani lokaci ƙalilan mota ta tashi daga tasha ta hau tafiya, inda Azima ta ji ta gaji dan gani take yi motar bata mata sauri,amma ance biyan bukata yafi dogon buri dan haka ta kara rungume hakuri.
Basu da isa kano ba kuwa sai magriba, ganin tsananin girma da faɗi da cikowa irin na garin kano yasa taji ma ta fasa kashe mutanen da tayi niyyar kashesu, ta shagala da kalle-kalle ta ji ana mata magana ta bayanta
“Barka dai ‘yar fulani”
????????????????????????
????????????????
Yau baƙin ciki ne a raina sau biyu ina cin uban typing yana gogewa, Allah dabadin bana son nayi missing update ba da ɗiff zaku jini????
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
(???? Macizai ne????)
MALLAKAR.
ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)
Follow me on wattpad,@Fateemah’0
????????????????????
PAID.
????️==2️⃣9️⃣↪️0️⃣3️⃣0️⃣
Ko da Salti ya isa gida ya kwashe kaff yadda yaji su Sarki Chubaɗo da mai Unguwa Ori suka tattauna ya gayawa Baffansa, a hankali Jauro ya mike yana murmushi ya ce
“Salti,tun da kake kwaso gulma baka taba kwaso mai amfani ba sai yau, jeka dole nayi maka kyautar shanuwa daya” da sauri Salti ya miƙe yana murna ya fice,Jauro ya dungule hannu yana dukar iska ya ce
“Lokaci ya yi da zan fatattaki Magaji Bawa, ka fi ni a komai kyau,martaba,baiwa,kyakkyawar mata Jumala,ga kuma yara kyawawa! kai kana gani ka fi kowa ne! zargin da nake yiwa yaranka ya tabbata, wato ma har b’oye-b’oye ake yiwa mutane ana munafurtarsu kar a gaya musu gaskiya, to ni nan zan bayyanawa jama’a su waye Azima da Aziza!” ya faɗa yana murmushin mugunta.
????????????????
Kamar yadda Malam Shadi ya faɗa da daddare ne ya yi bincike mai zurfi dangane da matsalar su Azima da Aziza,inda ya hangi gagaramin matsala mai rikitarwa inda tausayin yaran ya kamasa dan kuwa da wuya a samu maganin warakarsu.
Da washe gari bayan sun idar da sallar asuba ana gaggaisawa bayan sun gama gaisawa Malam Shadi ya kalli Baffa sai kuma ya duƙar da kai, Baffa ya yi murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo ya ce
“Malam Shadi karkiji komai gaya min ko ma miye ne,ni musulmi ne kuma nayi imani da kaddara mai kyau da marar kyau, ka gaya min kawai”
Jinjina kai Malam Shadi ya yi ya ce
“Tabbas ni shaidan hakane Magaji, wato a gaskiya ba zan boye maka ba, samun lafiyar Aziza yana tattare ne da Azima, domin kuwa wanda yake da alhakin abun ya ja Azima basu yankin kwana balle a musu magani, kai ko da Azima bata bar yankin kwana ba da wuya a samu wanda zai yi jahadin taimaka musu” goge gumi Baffa ya yi ya ce
“Malam Shadi ka gaya min kai tsaye kawai zan fi ganewa,dan a yanzu ji nake kamar kirjina zai tsage zuciyata ta faɗo kasa”
Malam Shadi ya gyara zama ya ce
“Dole sai sunyi aure kafin Banju ya rabu dasu, barin ma Azima ita ce wacce take bukatar taimakon gaggawa, sannan wannan miji da zai auresu sai ya sadu da Azima kafin Banju ya fita a jikin Azima, idan Banju ya bar jikin Azima a cikin kaso dari mun yaƙesa kaso sittin, idan aka yi sa’a idan Banju ya fita a jikin Azima, Aziza zata iya samun lafiya,idan kuma bata samu ba ita ma dole sai wanda ya aureta ya kusanceta kafin makarin sihirin da Banju ya mata na siddabarun maidata macijiya ya karya”
"Ma'asabamun musibatin Qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Innallahi wa inna ilaihirrajiun! Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" shine abunda Baffa da Baffa Mandi da Arɗo suke iya nanatawa suna fifita da hannunsu,Arɗo ya girgiza kai ya ce
“Tabdijam kawai Allah ya jikan Azima da Aziza, dan kuwa na tabbata babu namijin da zaiji cewa su macizai ne ya taimaka ya auresu har mu sa ran zasu samu lafiya”
"Kuma dole wanda zai aure su zai fuskanci ƙalubale kafin ya kusancesu,sannan bayan ya kusancesu zai iya kamuwa da mugun ciwo amma ba ina nufin ba zai warke ba amma tabbas zaiji a jikinsa,idan an samu damar hakan zaka iya kara kashe Banju a karo na biyu" hawaye ne Baffa ya hau yi yana kan tasbihi ga Ubangijin talikai, Baffa ya ce
“Tabbas da ace na dinga ganin tashin hankalin nan na b’arna da ta’adin da Azima ke yi da ni da kaina zan kasheta! to amma yanzu tana ina? Me take yi? Su wa da wa zata kashe!? Akwai tambayoyi dayawa a raina wanda babu wanda zai amsamin” Baffa ya hau kuka Arɗo da Baffa Mandi suna rarrashinsa, Baffa Mandi ya kalli Malam Shadi ya ce
“Malam Shadi, yanzu ya maganar raba Aziza da Bahula?”
"A gaskiya Mandi ni a ganina a shawarce, kar a raba Aziza da Bahula, tinda bata cutar da ita, sannan ko an raba Aziza da Bahula Aziza fa ba zata taba komawa mutum ba, ni a ganina tunda Banju yana son kanwarsa Bahula sannan yasan cewa tana rayuwa a jikin Aziza dole wata rana zai dawo, karku manta kamar yadda Azima da Aziza suke 'yan biyu haka ma Banju da Bahula suke 'yan biyu, zamu iya samun dawowa da Azima gida ta hanyar Bahula dake jikin Aziza,ni a ganina kar a raba Aziza da Bahula a barsu tare idan ya so aka samu wanda zai yi jahadin aurensu bayan an raba Azima da Banju sai a raba Aziza da Bahula"
"Tashin hankali wanda ba a sa masa rana" cewar Arɗo yana kan rarrashin Baffa dake kuka wi-wi, da kyar suka rarrashi Baffa ya samu ya tsaida hawayen idonsa sannan ya miƙe yana yiwa Malam Shadi godiya ya ce masa zasu wuce yau, Malam Shadi ya ce
“Ba damuwa Magaji,karka damu Allah zai shiga cikin lamarin” Baffa bai iya ya kara cewa kala ba, Malam Shadi ya miƙa masa wani ganyen magani ya ce
“Wannan idan ka je ka haɗawa Aziza,ita kuma Azima Allah ya dawo da ita cikin gaggawa, bari nasa a kira muku Azizan sai ku wuce” su Baffa Mandi da Arɗo suka yiwa Malam Shadi Godiya sannan suka fito a tare,bayan an kira Aziza ta fito Baffa ya kama hannunta idonsa jajur ya ɗorata a kan doki, Aziza tunda ta ga yanayin Baffanta tasan cewa kwai gagarumin matsala, haka sukayi sallama da Malam shadi cikin amince suka kama hanyar yankin kwana.
????????????????????
Sai da lokacin sallar azahar ya gauta kafin suka iso yankin kwana kai tsaye gidan Arɗo suka nufa, Hajja na zaune tayi zugum Yawuro ta ajiye mata kwaryan nono a gabanta amma haka nonon ke kallonta, Yawuro ke fadin
“Haba Jumala! Dan Allah ki sa wani abu a cikinki mana, ga jikinki da zafi, kiyi hakuri mana haba dan Allah” hawaye Hajja ta goge ba tare da ta cewa Yawuro Uffan ba, sallamarsu Baffa ne yasa Hajja ta dago da sauri ta sauke idonta a kan Aziza da ta shigo kanta a sunkuye, duk irin kunya na Hajja amma da sauri ta tashi ta rungume Aziza wacce itama ta saki kuka take ji a ranta da ace kisan kai ba haramun bane babu abinda zai hanata bata sha guba ta kashe kanta ba, kuka sukeyi sosai sai da Inna wuro ta dakatar dasu, sannan Inna wuro ta hau tambayarsu ya suka yi a can yankin ja’o ɗin, Baffa Mandi ya ce “babu amfanin a boye muku, gwara a gaya muku gaskiya” Ardo ya ce “tabbas dan wannan ba abun boyewa bane” nan Arɗo ya kwashe yadda suka yi da Malam Shadi ya gaya musu, wani mahaukacin zare ido Aziza ta yi jin bala’in da suke ciki wai sai sunyi aure an sadu dasu kafin su warke! Wa ma zai auri macizai!? Barin ma wanda zai auri Azima ya ji labarin kisan da Banju ya yi tayi a jikinta ai ma babu mai aurensu,in kuwa dole sai hakane sun zama annoba a cikin jama’a barin ma yanzu da Azima bata nan.