AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Sallallami su Inna wuro da Yawuro suke yi suna tafa hannuwa yayinda Hajja ke girgiza kai tana fadin ita a maido mata da yaranta tana wani irin kuka, Arɗo da Baffa Mandi suka ce Baffa yazo su je wajan Sarki Chubado da mai Unguwa Ori su gaya musu halin da ake ciki,    a tare suka fita aka bar Hajja da kuka ita da Aziza, su Inna Wuro suna rarrashinsu.

@@@@@@

    Bayani dalla-dalla suka yiwa su Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori yadda Malam Shadi ya shaida musu, Sarki Chubado ya ce

“Tashin hankali, gaskiya Banju ya mana illa dayawa, amma ina da shawara mai zai hana a gayawa mutanen gari halin da ake ciki, idan ya so sai a nemi wanda zai auresu ko da ba zai zauna dasu ba dai da sun samu lafiya sai ya sake su!”

  "Nima na fara wannan tunanin a raina ranka ya dade,amma abun dubawan a nan shine wa zai auresu?" cewar mai unguwa Ori, tattaunawa suke yi sosai ta yadda za a shawo kan matsalar amma duk inda aka dafa babu mafita, su na nan suna kan shawara sai ga Sanda da mugun gudu kamar wanda yake gudu a iska yana zuwa gabansu sarki Chubaɗo ya zube yana haki, Sanda jika ne ga Yawuro, Arɗo ya ce

“Sanda mahaukacin ina ne kai? Wannan gudu da ka zo a haka sai kace an kawo mana farmakin yaƙi miye haka? Meke faruwa?” kasa magana Sanda ya yi illa hanyar gida da yake nunawa da kyar ya furta “ADDA AZIZAAA!!” da sauri Baffa ya ce
“Me ya samu Azizan?” ya fada yana miƙewa tsaye, Sanda ya ce
“Baffa Jauro ne ya gayyo duka mutanen yankin nan wai zasu kashe Adda Azima da Adda Aziza wai macizai ne sune suka dinga kashe-kashe sune suka kashe su Ilu mai maganin Maciji dasu Jarman Macizai da Innu Maciji, yanzu haka ma sun saka wuta a gidan Arɗo ƙarami” da sauri su Chubado suka miƙe suna salati tare da al’ajabin ina Jauro yaji wannan maganar? Baffa Mandi ya ce
“Kafff yankin kwana da kewayenta babu munafuki sarkin gulma sama da ɗan Jauro Salti, to amma taya akayi ya ji wannan maganar?” Sarki Chubaɗo ya ce
“Yanzu babu lokaci maida magana muje kar su kashe Aziza” da gudu Baffa ya yi gaba idonsa har yana rufewa, ya rasa matsalar dake tsakaninsa da Jauro,bai san me ya tarewa Jauro ba a rayuwa da baya sonsa baya kaunarsa sam.

    Ko da su Baffa suka isa, sun samu gidan Arɗo karami na ci da wuta, ga Hajja a sheme a kasa an fasa mata kai, Aziza kuwa sun ɗaureta a jikin bishiya sai dukanta suke yi duk sun fasa mata jiki, a ranta take kalman shahada dama su kasheta kawai ta huta da wannan rayuwar, ihuuu Baffa ya yi ganin matarsa kwance a sheme a kasa an fasa mata kai ga 'yarsa da aka yi mata daurin mayu ana dukanta, ihun da Baffa ya yi yasa hankalin jama'a dawowa kansa, Jauro ya yi murmushin gefen baki kafin ya matso kusa da Baffa yana magana yana daga murya

“Hakika bai kamata ace daku za a haɗa baki a munafurci mutanen yankin nan ba, (yana yi da sarki chubaɗo da mai unguwa ori) sannan kai kuma Magaji idan ka manta na tuna maka,kaine kace min duk ranar da na gano AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE kaine wanda zaka bani takwabin da zan kashesu! Dan haka yau sunan Aziza gawa,ita ma Azimar da ta bar yankin nan da ace tana nan da yau gunduwa-gunduwa zamuyi musu” murmushi Baffa ke yi hawaye na zuba a idonsa yana yiwa Jauro wani irin kallo wanda ko idonsa baya kiftawa, Jauro ya kuma cewa
“Shin zaku yarda ku rayu da macijiya mai kisa a cikinku?” jama’a suka amsa da a’a, Jauro ya kuma cewa
“Idan kuwa hakane ku ci gaba da dukanta har sai ta mutu!!” Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori suna dakatar da jama’a amma ina kamar kara ingizasu akeyi, wani ne da ya daga wani babbar sanda ya roɗawa Aziza a kai jikake kwasss!! Wani ihuuu Baffa ya kuma yi ganin yadda sandar ta shigi Aziza dan har sai da ta girgiza, Baffa ya kalli Jauro cikin jan ido ya ce
“Karka bari na nuna maka waye asalin Magaji!!”
“Zan so hakan” Jauro ya fadi yana dariya, ci gaba da dukan Aziza mutane suka yi, wani gurnani Baffa ya yi mai taken muryan zakin dawa, sannan ya rintse ido ya haɗa wani guguwa mai cike da barkono ya kwashi jama’ar da suke dukan Aziza ya watsar dasu, a take ya yi tsalle daya yaje gabanta yasa hannu ya shafe igiyar da suka daureta igiyar ta tsinke, sannan Baffa yasa hannu ya shafe mata inda suka ji mata ciwo ya kamo kafadunta cikin daga murya ya ce
“AZIZAAA!! NA YARDA DA KEEE!! INA SO NE KI BAR YANKIN NAN!! BANA SO SU KASHEKI ALHALI ‘YAR UWARKI TA BAZAMA GARI! INASO KIJE KI NEMOTA SANNAN KI DAKATAR DA ITA,IDAN HAR KU KA HADU KIKA GA B’ARNARTA YA YI YAWA NA MIKI IZINI KI KASHETA ITA DA BANJU!! IDAN KUMA KE MA TAKI TA ZO KARSHE DAMA BA ZAMA MUKA ZO YI BA,IDAN KUMA KIN SAMETA KU DAWO! NINA SAN TA INDA ZANYI MAGANIN BANJU!! AZIZA TAFIIIII!!” girgiza kai Aziza tayi tana wani irin kuka alaman ba zata iya tafi ta bar Hajja da Baffa ba, rai b’ace Baffa ya kara cewa bar yankin nan na ce Azizaaaa!! da gudu Aziza ta yankin jeji dan barin yankin kwana, Jauro ya yi yunkurin binta Baffa ya ce
“Kana bin bayanta zan mata umarni ta kasheka! Ka godewa Allah Aziza ce ba Azima ba ce! Da sunanku gawa gaba daya!! Ni zaku yiwa haka! Sabida su waye yanzu nake fuskartar wannan bala’in!!?”

 ????????????????????

MOMYN AHLAN CE✍????
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

ASSALAMU ALAYKUM, SAKO ZUWA GAREKU MASU FITAR MINI DA BOOK DA MASU KARANTAWA BASU BIYA BA, DA WA INDA SUKE GANI SUKE KARA WATSATA A DUNIYA,DA FARI ZAN FARA DAKU MASU FITARWA DAN BABU MASU LAIFI SAMA DA KU! HAUSAWA SUKA CE SAI BANGO YA TSAYE KAƊANGARE K……! DAYAWANKU WASUNKU SUN JAHILCI WANNAN LAMARIN NA CEWA WAI KUDINSU SUKA CIRE SUKA BIYA YA ZAMA NASU MALLAKINSU, YAR UWA TA INA LITTAFI YA ZAMA NAKI? LITTAFI HAKKIN MALLAKAR MARUBUCIYA CE ITA DA TA ZAUNA TA TSARA LABARINTA SANNAN TA RUBUTA TA WALLAFASHI TA WATSA SHI HAR KIKA KARANTA SHI,KE KIN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI,KI KARANTA KI BAR WA MARUBUCIYA ABUNTA, KUNA FADIN YANZU MISALI KUJE KASUWA KU CIRE KUDI KU SIYI ABUN SAI ACE MUKU KARKUYI KYAUTA DA SHI KO KU BADA ARO? TO INASO KI SANI AKWAI BAMBANCI TSAKANIN ABU A ZAHIRI DA SOCIAL MEDIA, YANZU NE AKA SAMU CI GABA KINA DAGA KWANCE A DAKI BA SAI KIN SHA WAHALA BA KINJE KASUWA KIN SIYO LITTAFI BA, A DA KAM WA INDA SUKAYI KARANCE-KARANCE SUN SAN TSADAR LITTAFI DARI BAKWAI DARI TAKWAS KAI HAR DUBU DAYA, SANNAN MIYE RIBARKI FISABILILLAHI DAN KIN CIRE DARI! NAIRA DARI KIN BIYA KUDIN KARATUN LITTAFINA SANNAN KI DAUKA KI WATSAWA MUTANE SAMA DA DUBU DARI DA BASU BIYA BA? ANYA KUWA AKWAI ADALCI A LAMARIN? DUK TALAUCIN MUTUM MAGANA TA DOMIN ALLAH ZAI CE BAI DA NAIRA DARI DA ZAI BIYA YA KARANTA LITTAFINA NE? BAN TSAULAWA BA SABIDA NA SAN KUNA SON LITTAFIN SHIYASA BANSA TA YADDA BA ZAKU IYA BIYA BA, WLH WLH WLH AZIM DA ACE KUN SAN WAHALAR RUBUTU KO A SHAFI DAYA ZAKU DINGA BA WA MARUBUCIYA DARI BIYAR A DUK SAKIN PAGE WLH BAKU BIYATA BA, BALLE KUMA NI DA NA ZAUNA NA TSARA MUKU LABARI NA CE KU BADA NAIRA DARI KACAL! YAKE MAI FITAR MIN DA LITTAFI INASO KI SANI HAKKINA NE,KUMA DUK HAKKIN DA KA RAINA SHI KE GIRMA YA TSOLE MAKA IDO, IDAN HAR BA ZAKI DAINA TOZARTANI BA TA HANYAR WATSA MIN LITTAFI BA TO INASO KI SANI BA ZAN MIKI ALLAH YA ISA BA, AMMA SHURUN DA NAYI WLH SAI ALLAH YA SAKA MIN, MASU CEWA SAI SUN SATO KUMA SAI SUN KARANTA ALLAH YA BAKU SA’A, A AL’ADANCE SATA SUNANTA MA BABU DADI BARE A ADDINANCE HARAMUN NE! SANNAN WANNAN ALLAH YA ISAN DA KUKEJI MARUBUTA NA FADI BA KARAMAN KALMA BA CE WLH,KE IDAN KINA DA TUNANI KI ZAUNA KIYI NAZARI A KAN KALMAN ALLAH YA ISA! SANNAN NA DAWO KANKU MASU KARANTAWA HARDA TAMBAYAR CI GABA,IDAN HAR KINA KAUNAR ALLAH KINA GANIN GIRMAN DARAJAN ANNABI MUHAMMADU SALALLAHU ALAIHI WASALLAM! KI DAINA KARANTA MIN LITTAFI BAKI BIYA BA,KI NEMENI TA LAMBATA KI BIYA NA SAKAKI A PAID GRP DINA IDAN KUMA KIN SAN ZAKI BIYA NE DAN KI WATSA SHI DAN ALLAH BA SAI KINZO GARENI BA????????, HAKA KEMA MAI YADAWA DUNIYA INA ROƘONKI DA GIRMAN ALLAH DA DARAJAN IYAYENKI KI BARI! BAKI SIYA BA AMMA IDAN KIKA GANI JIKINKI NA RAWA KI TURAMA WASU KEMA KIJI TSORON ALLAH KI DAINA, ALLAH YA BAKU IKON FAHIMTAR ABUNDA NA FAƊI, WA INDA BASU SON SU CI HAKKI SAI KU NEMI NAKU!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button