AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shampoo sosai Lantana ta zuba a kan Azima amma ta ga idan har ta juye ba isa wanke mata kai zaiyi ba, haka yasa ta dauke ledar omo sai da ta zuba ya kai kwankwani ɗaya da rabi kafin ta fara dirzan kai Azima wanda yake fitar da datti, sun kai mintuna talatin tana wanke mata kai kafin gashin ya fito baƙi da shi ga tsamtsi yayi fess! Lantana ta yi murmushi ta ce
“To kiyi wanka,bari na baki waje” har Lantana ta kai bakin kofa sai ji tayi Azima na faɗin
“Miyatti Inna” karo na farko da ta fara yima wani ɗan adam godiya a rayuwarta, murmushi Lantana ta yi ta fice, sai a lokacin tunanin ‘yan yankin kwana ya faɗowa Azima a rai,dariya ta hau yi tana fadin
“Ko ina Macijiya Aziza sarkin tausayi oho! Watakila sakaran tana can an kasheta a jeji! Ko da yake ba zasu iya kasheta ba! Amma nasan shanuwar tana can suna jibgarta” ta karasa maganar tana haɗe rai, wanka ta yi sosai ta dirje jikinta ta fito, sai da jikinta ya bushe ta kuma saukowa da gashin kanta kafin ta fito ta samu Lantana ta ajiye mata fallan zani da t-shart da su mai da turare, kayan ta saka, sannan ta dauki kum ta sharce gashin kanta ta zubo da wanda yake rufe masu gefen fuska sabida kar ana ganin kwayar idonsu, gashin ya sauko har ƙirjinta, kallon kanta ta yi a madubi ta ga ta yi kyau,murmushi ta yi, sai ga Lantana ta shigo
“Wa Subhanallahi bi’ahsanul Khaliƙin!” cewar Lantana Azima ta sunkuyar da kai, Lantana ta ce
“Zo muje na nuna miki ayyukanki” Azima ba ta kuma magana ba ta bi Lantana a baya, nunnuna mata komai Lantana ta yi har da dakin Baby da dakin Munir, Azima ta ce ta gane, sannan Lantana ta ce
“Yanzu ki fara gyara dakin Munir dan bai da mutunci ko kaɗan duk wulakanci Baby da Zuby suna bin bayan Munir ne, idan ya dawo ba a gyara masa daki ba ya ganki ba zaiyi la’akari da cewa ke sabuwar zuwa bace ya yi ta kwallo dake”
“DA KUWA KO ƘASHINSA BA ZAN RAGE BA!” Lantana ta ce
“Iyeeee!!?” sauri saita kanta Azima ta yi ta ce
“Inna je ki kawai zan gyara yanzu” fita Lantana ta yi,Lantana na fita Azima ta bi lafiyar gado ta kwanta dan tayi wanka mai dadin da bata bata yi ba taji bacci takeji.
????????????????
Karfe sha daya saura ya shigo kd bai wuce gida ba ya wuce asibitinsa da ita, har yanzu kuma bata farka ba,bai damu ba tunda ya mata alluran bacci mai karfi ne, bayan ya mata komai ya ba wasu nurse mutum biyu kula da ita wanda zasu yi nyt duty, kafin ya wuce gida.
A wani katafaren gate yayi horn da sauri aka zo aka buɗe masa, ya shiga ya yi parking din motarsa, da fari ji ya yi kamar ya shige part dinsa dan ya gaji,amma kuma gwanda ya shiga ya yiwa Mom sai da safe, da wannan tunani ya yi babbar parlon nasu da sallama,kanwarsa Sultana tana zaune wacce ba zata wuce 18 ba tana kallon wani horror seris film tana jin sallama ta miƙe da gudu tana fadin
“Oyoyoo BROS NAWAZZ!”
????????????????
MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
(???? Macizai ne????)
MALLAKAR.
ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)
Follow me on wattpad,@Fateemah’0
????????????????????
INA GAISHEKU KYAUTA YAN PAID GRP MASOYAN……..BAN DAI KARESA BA KU KARASA DA KANKU
PAID.
????️==3️⃣3️⃣↪️3️⃣4️⃣
Saurin juyowa Azima ta yi ba tare da ta dago ba
Ya yi murmushi ya CE
“Yan mata magana nakeyi fa” da sauri ta matsa gefe ta hau tafiya tana sake rufe fuskarta, shi kuwa binta ya hauyi yana kan yi mata magana,da ya ga ba zata tsaya ba ya sha gabanta, cije baki Azima ta yi tana hade rai,babu abunda ta tsana kamar a sha gabanta,Cikin murya da yake nuna taji haushin takura mata da yayi tace
“Malam wai lafiya?”
Dariya ya hau yi jin yadda kalar Hausar ta ta ke fita, a ransa yake fadin “wow! Wannan daga ganinta bagidajiya ce daga jeji take,bari nayi mata wayo, ko Allah zai sa na shana da ita daga dawowata!”
“Amm yi hakuri ba nufina na ɓata miki rai ba,naga yadda kika ta kalle-kalle ne kamar baki san kowa ba, shine nake so na taimaka miki” ya karasa maganarsa yana murmushi, itama Azima murmushin ta yi ta ce
“To taimakona da me? ko nazo nace da kai inada bukatar taimako ne iyee!!? Na ce maka ina da bukatar taimako ne?”
“Allah ya huci zuciyarki sarauniyar kyawawa, Kano gari ce mai girman gaske da faɗi kuma ke naga alama kamar baƙuwa ce, dan haka ki yarda na taimaka miki naga ke mace ce,ki zo muje gidanmu” mutuwa da mamaki Azima ta yi ko me ta tuna ta yi murmushi ta ce
“Na gode da taimako muje”
“Ina kayan ki?”
“Wala!”
Ta ba shi amsa hankalinta yana can wajan kalle-kalle, jakarsa da ledarsa ya dauka ya ce
“Muje” ya yi gaba ta bisa a baya, kekenapep ya tare musu suka shiga, wani farin ciki ne ke mamaye zuciyar Azima sai magana yake mata amma ina hankalinta ya yi ƙololuwa wajan ganin girma da faɗi da cikowa irin na NA DABO TUMBIN GIWA, ana cikin tafiya sai ji ta yi kekenapep din ya tsaya sai a lokacin ta maido da dubanta ga wani ƙazamin gida wanda ko bukkarsu na yankin kwana ya fi sa kyawun gani, bata damu ba, yayinda ya ce mata ta fito a keken, ba musu kuwa ta fito tana kallon mutanen da suke zaune a kofar gidan masu caca da masu shan wiwi da sigari har ma da masu shan giya, jin yadda ta hadiyi hayakin sigari da wiwi yasa ta hau tari kadan-kaɗan tana yamutse fuska, mai kekenapep ya biya sannan ya kalleta ya ce
“Mu shiga ciki ko?” ya yi gaba ta bisa a baya mutane sai kallonsu suke yi har suka shiga,suna shigewa a cikin wa inda suke zaune a kofar gidan wata mace tayi shigar riga da wando,duk da babu mai kayan mutunci a cikinsu, tab’o dayar dake kusa da ita ta yi ta ce
“Kee Bariki Dadi, baki ga Hoge ya wuce da wata bafulatana ba?” wacce aka kira da sunan Bariki dadi tana riƙe da sigari a hannunta tana zuga suna buga caca ta ce
“Hoge dai? Yaushe ya dawo?”
“Ba mamaki dawowarsa kenan dan na gansa da kayansa” miƙewa tayi da sauri ta ƙudundumo wani ashar sannan ta yi cikin gidan da sauri wa inda suke zaune a tare suka hau zugata suna fadin “idan kinje kici uwarta da ubanta! Bariki dadi! Baki da kyau baki da dadi!” suna fadi suna ihu,ita kuwa fuuuu tayi ciki,a lokacin Hoge har ya buɗe a kulkin dakinsa ya kalli Azima ya ce
“Shigo mana yar fullo” a hankali Azima ta sa kafa ta shiga, a wani jagalgalalliyar katifa ta zauna tana saƙa abubuwa dayawa a ranta, tana zama sai ga Bariki dadi ta banko kofar kamar zata b’alla shi, Azima bata dago ba illa Hoge dake fadin
“Wannan wani irin iskanci ne haka?”
“Ga ka nan kuwa babban dan iskaci baƙin munafuki! Ka hanani kula ko wani bunsuru, sannan ka dauko wata banziya daga dawowarka ka huce da ita a gabana! To wallahi sai naci Uwarta! Ke kuma munafuka zo nan! Sai wani rufe fuska kikeyi sai kace wata ta Allah kina sunkuyar da kai, to idan baki sani ba ki sani! Kina sa kafarki a nan gidan dukkan wata mutuncinki ya zube kuma saina koya miki hankali!” murmushi Azima ke yi a ranta ta ce
“Inason mutane irin haka! Wa inda basu shiga gonata ba ina kau dasu balle wa inda suka shiga” bata gama maganar zucinta ba Bariki dadi ta shaƙo wuyarta, tashi tsaye Azima tayi,tana tunanin dame zata kasheta! ta sareta ne ko ta watsa mata dafi? Hoge ne ya fizgi Bariki Dadi ya koɗa mata mari sannan ya ingizata waje ya juyo yana ba wa Azima hakuri, bata ce masa ci kanka ba,illa da ya gama rawar bakinsa ya fice wai zai kawo mata abinci, bai jima ba kuwa ya shigo da bakar leda ya ajiye mata, budewa Azima ta yi nan tayi arba da kayan dadi murmushi tayi dan bata taba ganin kalar abincin ba, da sauri ta buɗe ta hau ci tana lumshe ido tana gya ɗa kai, shi kuwa yana zaune a gefe yana kallon gashin kanta da ya rufe mata fuska aransa ya ce
“Hummm! dama ana ganin irin wa innan matan a gaske? Dole na shana wlh,daga ganin wannan ɗanya ce jaƙab, zatayi ruwa zata kai yadda ake so, idan tayi daga nan zata zama cikata!” sai sambatu yakeyi a zuciyarsa yana hadiye yawu,Azima kuwa fess ta cinye abubuwan da ya kawo mata, ta kwankwaɗe maltina har tana lashe baki, tana gamawa ta koma ta jinginu da banko tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido,jin saukar numfashi ta yi a wuyarta, saurin buɗe ido ta yi ta gansa ya matsota sosai, sai wani washe baki yake yi, bata gama karantarsa ba taji yana fadin
“Meyasa kike rufe baiwar kyawun da Allah ya miki da wannan dogon gashin naki? Duk da ba a ganin fuskarki da kyau amma da an ganki an ga kyakkyawa ajin karshe, dan Allah ki buɗe idanunki na ganki,sannan ina so ki bani hadin kai nayi miki alkawari zan baki duk abunda kikeso zan miki komai” cije baki Azima ta yi jin yadda wani baƙin ciki ya mamaye zuciyarta,daurewa ta yi tasa yatsarta babba manuniya a kan goshinsa, ta ture kansa daga wajan saitin wuyarta sannan ta ce
“Kasan daga ina nake? Sannan ni fuskata kallo daya ake mata,idan har ka gani babu fuskar da zaka kara kalla a rayuwarka”
“E na yarda ni dai ki bude fuskarki na gani, sannan zan baki abun dadi” ya fadi yana shirin kai hannunsa kirjinta,da sauri Azima ta ja da baya tana fadin
“Owohh kenan kai ɗan iska ne! Zan koya maka hankali, ka taba ganin maciji?”
“E amma a zahiri sau daya na taba gani kuma ƙarami ne ma,amma ina gani a fina-finai”
“To yau zaka ga Babban a zahiri ido da ido!” ta faɗi tana dariya yayinda ta kwashe gashinta ta maida su baya,blue eye dinta ya bayyana, a gigice hoge ya ja da baya, yayinda ta hau rikiɗewa,tun kafin Azima ta taba Hoge numfashinsa ya fara barazanar daukewa, yana ganin zureren Maciji har na sheƙi a gabansa nan ya fadi sumamme, Azima ta sa baki ta saresa a gabansa, sannan ta koma mutum ta fice, ta zo fita kenan suna karo da Bariki dadi,shaƙeta bariki dadi tayi,Azima tace
“Dama kafin na tafi ina nemanki!” tana gami fadi ta zaro harshenta ta watsa mata dafi sannan ta bar gidan.