AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

      A cikin unguwa kuwa ana nan ana jiran isowar jarman macizai, tun ana sa ran ganinsa takwas har goma, inda a karshen mai unguwa ya ce aje a duba ko lafiya a binciki hanya aka tura mutum uku.

    Ai kuwa can suka gano gawar jarman macizai a yashe cikin jini, cikin tashin hankali suka juya da mugun gudu suka koma suka sanar da jama’ar gari an kashe jarman macizai.

    Fadin tashin hankalin da mai unguwa da jama’ar gari suka shiga b’ata lokaci ne.

????????????????

Fitowa Aziza ta yi daga bukka dan tun sadda taji motsin yar uwarta jikin dare kafin garin Allah ya waye  jikinta ya bata ta tafi kashe jarman macizai, abunda yasa bata yi yunkurin bin bayanta ta dakatar da ita ba sabida tasan dole Hajja da Baffa su leƙo duba lafiyarsu, tana fitowa dauke da murmushi a fuskarta Hajja ta ce
“Aziza ke kin tashi? Azima ta farka ta yi sallah kuwa?” tsilli-tsilli da ido Aziza ta fara kafin ta ce
“Eh Hajja ta tashi ta yi har ma ta fita wai ta je rafin jimulo” Aziza ta karasa maganar da in-ina sabida da asuba da Hajja ta shigo tada su kara Aziza ta jera kusa da ita ta yadda zata ga kamar Azima ce ke bacci, dan lokacin da Azima ta fita Aziza ta ji motsinta tsoron kar su fita duka a gane yasa Aziza hakura ta kwanta, dan Baffa kunnuwansa akwai saurin jiyo abu.

Kallon Aziza da kyau Hajja ta yi kafin ta ce
“Me ku ke zuwa yi kullum ne a rafin jimulo?”

   “Ba komai Hajja kawai rafin akwai dadi ne, ga iska mai dadi, Hajja kin manta sadda kike kai mu muyi wasa?” murmushi Hajja ta yi ta ce
“Eh na tuna, yanzu dai je ki kirawo Azima ku zo kuci abinci”
“To Hajja, Baffa ya fita ne?” Aziza ta tambayi Hajja kamar bata san Baffan ya fita ba, Hajja ta ce
“Eh ya fita kin san ai jiya yace yau Jarman macizai zai zo, yace min idan yazo zai zo ya kiramu muje gabadaya ayi gwaji” Aziza ta jinjina kai tana fadin “to Hajja bari naje na kira Azima kafin Baffa ya dawo”
“To a dawo lafiya,ki tabbatar kinyi lullube da kyau fa”
“To Hajja” Aziza ta fada tana ficewa jiki a sanyaye, tana fita da gudu ta yanki rafi inda tasan Azima ba zata wuce can ba.

   Tana zuwa ta sameta kwance a kusa da rafi.

Hannnu tasa ta janyota ta ce
“Kin kashesa ko Azima? Na ce kin kashesa ko!?” dariya ta kyalkyala cikin amo marar dadin sauraro ta ce
“Ai na gaya miki Aziza sai na kashesa!”

Rike kai Aziza ta yi ta ce
“Me kika so ki zama ne kam Azima?”

“Bana son ganin zaman lafiya a wannan yankin! Na fi so ayi ta b’arin jini! Ina so na haɗa maƙotan yankunan nan faɗa, duk wani mai kama macizai wanda za a yi masa aike ya zo yankin nan sai na kashesa! Kin ga daga nan za a fara yaƙi tsakanin yankuna da yankuna, sannan dama akwai y’ar tsama tsakanin yankin kwana da yankin tudu da kuma yankin Ja’i nasan kuma dole mai unguwa zai bukaci taimakonsu, duk wanda aka turo ni kuma zan kashesa! Na tabbata daga lokacin zaman lafiya ya kare, Baffa shine jarumi na farko a wannan yankin wanda da shi aka yi gwagwarmaya kinga kuwa ba mamaki a wajan yaƙin a kashesa!”

      ????????????????

DAN ALLAH JIYA NA FARA LITTAFIN NAN, BAN BUƊE PAID GRP BA, SABIDA BAN GAMA FREE PAGES BA,KUYIWA ALLAH IDAN BA KU GA UPDATE DINA A RANA BA KARKU CE ZAKUYI KORAFI, NA SANI DOLE NE TUNDA NA FARA ZAN KARASA DA IZININ ALLAH, SABIDA HAKA KU MIN UZURI RANAR DA BAKU GA UPDATE BA TUNDA BAN GAMA FREE PGS BA, IDAN ZAKI BIYA DARINKI YANZU FYN, IDAN KUMA SAI AN GAMA FREE PG NE DUK DAYA AMMA DAN ALLAH BAN DA KORAFI, MATAR GIDA CE NI MAI IYALAI, UWA UBA KUMA DALIBAR MAKARANTA, FATAN ZAKU FAHIMCENI,INA GODIYA GA MASOYANA MASU GANIN SUN BIYAN KUDIN KARATUNSU, NA GODE DA BIBIYATA DA KUKEYI, ALLAH YA BAR KAUNA, 1 LUV

COMMENTS AN SHARE
BY
MOMYN AHLAN.
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: https://chat.whatsapp.com/BXDHlYEJdRi65a26Qt5OSe

????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

   ????????????????????

????????????????????????
????????????????????????????????????
YAU TAMBARINA NA MASOYA NE,INA GODIYA DA SAKONNINKU,KIRAN WAYA, KAI MA SHA ALLAH, ALLAH DAI YA BAR KAUNA,INA ALFAHARI DAKU A DUK INDA KU KE MASOYANA, ALKAIRIN ALLAH YA KAI MUKU HAR KUJERAR ZAMANKU????

FREE..
????️==5️⃣↪️6️⃣

Zaro ido Aziza ta yi tana kallon Azima kafin ta ce
“Na rasa dalilinki na son ganin bayan Baffa! A yadda na fahimceki, ke ba ki ƙi kowa ya mutu ke ki rayu ba, idan kika samu dama na tabbata za ki kashe Baffa”  dariya Azima ta kyalkyale da shi tana kewaye wajan kafin ta koma ta haɗe rai sosai ta ce
AI BA YAU BANE KAWAI NA SHA GWADA HAKAN!  ko a yanzu na samu sarari sai na kashe Baffa! Ko kin manta na sha yunkurin kashesa!? Lokuta da yawa ke ce kika katse min burikana! Ga shi ke ban san ya zanyi dake ba! Ke ta biyu na ce! Ba zan iya kasheki ba! Sabida duk muguntar gubana naki yafi nawa! Kuma ina sonki yar uwata! Da ace nike da karfin dafin da kike da shi da na jima da shafe wannan yankin kakaf dinta!” Azima ta fada tana daga hannuwanta sama.

    Aziza ta girgiza kai ta zauna a kasa tare da fashewa da kuka ta ce
“Azima ba zan taba bari ki cutar da Baffa ba,ko da kuwa zaki iya,ni dai a gaskiya inaji a jikina kamar ni da mutum ce! Ban san a garin yaya muka zama macizai ba, miye dalilinki na son kashe Baffa Azima!?” Aziza ta faɗa tana haɗa kai da guiwa tana ci gaba da kuka,duk sadda ta kalli jikinta ta ganta a macijiya tana jin zafi a zuciyarta, ta yi nisa sosai a kuka ta ji wani irin murya na namiji wanda yake abun tsoro an bata amsar maganarta.

     ” ZUNUBIN DA BAFFANKU YA AIKATA NE YAKE BIBIYARKU!, TARE DA GOYA MASA BAYAN DA JAMA’AR YANKIN NAN SUKA YI!” da sauri a matukar firgice Aziza ta dago tana waige ta ga daga ina ne maganar ya fito? Amma bata ga kowa ba illa Azima dake wasa a cikin rafi kana ganinta zaka san tana cikin nishaɗi, ta zama macijiya ta koma ta zama mutum.

Sauri tashi tsaye Aziza ta yi tana waige a fili ta kara furta kalman da ta ji “Zunubin da Baffanmu ya aikata? Me Baffanmu ya yi kuma?” tambayoyi ne maqil a ranta amma babu mai bata amsa, ko dai zata je ta tambayi Baffa ne? Kai amma kuma idan ta yi haka za a gane su ɗin ba mutane bane, riƙe wuyanta ta yi jin kamar zuciyarta yana shirin fitowa bakinta, kallon Azima ta yi ta ce
“Azima ki zo muje gida”
“Tare muka zo dake ne?”
“Idan ma ba tare muka zo ba Hajja ta ce mu dawo tare yanzu, kar Baffa ya dawo….” Aziza ba ta karasa ba Azima ta fito tana fadin
“Ke komai ki ce Baffa?”
“To idan ban kira sunan Baffana ba sunanki zan kira?” murmushi Azima ta yi ta ce
“Yau bana jin yin faɗa dake, dan yau ina cikin farin ciki, nasan idan sako ta iske sarkin yankin jimo an kashe masa Jarman Macizai me kike tunani zai faru Aziza?”
“Ban sani ba!” Aziza ta faɗa a ƙufule ta yi gaba, ita ma Azima a macijiya ta hau bin bayan Aziza, yau tsananin takaici ya hana Aziza ta cewa Azima ta koma mutum, Azima kuwa da gangan take wani abun dan Aziza ta mata magana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button