AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

PAID.
????️==3️⃣9️⃣↪️4️⃣0️⃣

Hannu yasa jikinsa na rawa yana lashe baki yana kwashe gashin da ya rufe mata fuska cikin bacci Azima ta ji mutum a kanta, bata gama tabbatarwa ba sai da taji saitin hannun mutum a wajan dukiyar fulaninta, nan da nan ta farga da abunda ke wakana a kanta, idonta ne ya sauya, da tafin hannunta ta tokari kirjin Munir kamar kiftawar ido da bismillah sai ga Munir ya yi sama ya bugu timm da kasa!! Saurin tashi Azima ta yi,ta dauki mayafinta ta yi lullubi sannan ta yi kan Munir,tana zuwa ta shaƙosa da hannu daya ta haɗasa da bango,nan idon Munir ya yi waje yana so ya yi ihu amma baya so kannansa suji su rainasa, lallai yau ba shakka ya yi gamo da aljana a garin ɗan banzan son matan tsiya tun bai tsaya ya ga wacece ba ya afka mata ga shi tana neman kashesa, lokuta da yawa Munir ya sha yiwa yaran aikinsu fyaɗe,da anyi kara kuwa uwarsu zata zuba kuɗi ta karbo ɗanta tace an masa sharri.

 Cikin zafin zuciya Azima ta kamo hannun Munir wanda ya taba mata kirji da shi, matse hannun tayi jikake ƙashi na haɗewa yana bada ƙaƙassƙasssƙass!! Ihu Munir ya sake na azaba, Hajiya da Zuby dake parlour suka ji ihun Munir da gudu sukayi dakinsa, a lokacin da ya yi ihu Azima ta sakesa ta koma gefe jin kafar mutane da gudu, kafin su shigo Azima ta duƙa kasa a gaban Munir, Hajiya da Zuby suna shigowa Munir ya yi saurin maida hannuwansa baya, Hajiya tace

“Munir ihun me kakeyi haka?”
“Ha…ji….ya…wa..ce..ce…wan…nan…yarinyar..” sai a lokacin suka maida kallonsu ga Azima da take duƙe tana murmushin mugunta ta cikin mayafi, tsaki Zuby tayi tace
“Mtswww Munir amma dai wlh kaji kunya,duk iya shegenka amma wannan yarinyar kake yiwa ihu? Sabuwar mai aikin da hajiya ta dauka ne fa, wlh nikam har na manta da ita a gidan,ke dan uwarki miye kikeyi a dakin nan tun rana har yanzu?” matse hannu Azima tayi tana cije baki, da kyar ta ce
“Da na shigo na manta abubuwan da Inna Lantana ta gaya mini nayi ne,kuma da nazo fita ban san ta inda zan fita bane shiyasa na zauna, shi kuma da ya shigo ya ganni sai ya tsorata” Hajiya ta ce
“Ba dole ba!, fuska a rufe kina dukar da kai, banza kawai maza ki tashi ki gyara masa dakin yanzun nan idan kin gama kije ki gyarawa Baby da Zuby nasu, sannan ni kuma kije ki wanke min toilet, ohh ina nufin bayi ko kewaye ku ke cewa oho,dalla tashi!!” Hajiya ta faɗa da tsawa suna ficewa a dakin ita da Zuby, Munir ya ce
“Kee dan ubanki! Dama ke mai aiki ce shine kika shaƙeni! Kin san waye ni kuwa?” waigowa Azima ta yi ta ce
“Kamar yadda kaima baka san wacece ni ba! Ka kiyaye! Bana gargaɗi sai dai zartar da hukunci!” tana gama fadi harta juya zata fita ya ɗan sake ihu yana maqale hannunsa, juyowa Azima ta yi ta dawo ta cafke hannu yayinda ta sake matsewa ta ware hannun ya sake sakin kara, hannun nasa ya dawo dai-dai ta ce
“Ban taba lalata abu na gyara ba! Sai dai idan aka gyara na b’ata!” tana gama fadi ta fice, wajan Lantana a kitchen taje Lantana tana ganinta ta ce
“Ahh Azima tun rana ina kika shiga haka?” abunda ta gayawa su Hajiya shi ta kara nanatawa Lantana daga nan ta hau tayata aiki suna girkin Azima taji tana bukatar watsa dafi a cikin abincin,amma kasancewar tasan Lantana zata ci yasa ta hakura da watsa dafin,bata taba jin bata son kisa ba sai a kan Lantana ko meyasa hakan oho, bayan sun gama kowa yaci abinci suka gyara kitchen har sun kwanta Hajiya ta kwalawa Azima kira, cike da takaici da haushi Azima ta dauki mayafinta ta fice tayi dakin Hajiya, ko sallama ba tayi ba ta shiga Hajiya na zaune a gefen gado,tana ganin shigowar Azima kamar an bankota yasa Hajiya miƙewa da masifa
“Ke wace iriyar jahilace! Ƙidahuma bagidajiya! ‘yar can cikin jeji kawai! ban gaya miki ki zo ki wanke mini bayi ba?” Azima na shirin magana Munir na kwala mata kira, Hajiya tace
“Maza je kiji me yake da bukata ki gama masa ki zo ki wanke min toilet dina yau din nan, ai babu ke babu bacci” fita Azima ta yi ta nufi dakin munir yana tsaye daga shi sai gajeran wando,kallonsa tayi ko gizau bata yi ba balle taji dari-dari dan ta gansa a haka
“Keee!! Banza ‘yar jeji, gyara min gadona”
“Kaiiii!! Banza shanu ɗan iska ban gyarawa!” ta juya zata fita Munir yasa hannu ya fizgota ya ɗaura mata sannan ya tureta gado ya bita ya danne, wani gurnani Azima ta yi tare da rikiɗewa rabinta mutum rabinta macijiya! A haukace Munir ya tashi a saman kanta ya yi baya-baya ya faɗi a gado jikinsa na rawa, gashinta ta kwashe blue eye dinta ya bayyana ya ƙare rinewa
“Ban ce maka ka kiyayeni ba! Baka san wacece ni ba ko!?”
Cikin shiɗewar numfashi sabida tsananin tsoro da firgici Munir ya ce
“Dama ke ba mutum ba ce!!?”
Murmushi Azima ta yi ta ce
RUWA BIYU! Mutum Macijiya!”
“Dan Allah kiyi hakuri karki kasheni!”

"Duk wanda ya ga kwayar idon Azima baya sake ganin wani!" tana fadin haka ta koma macijiya ta saresa a bayan wuya nan munir ya faɗi ya hau murkususu yana birgima har ya dai na! rai ya yi halinsa, sai da Azima ta ga ya mutu kafin ta zama mutum ta fice a dakin taja ta rufe shi, ta koma dakin Hajiya da take ta sababi, Azima ta ce Hajiya

“Ki ɗan jira a parlour na gama gyara miki dakin”
“Saura kuma karki gama da wuri ki ga yadda zanyi dake a cikin daren nan ‘yar can cikin jeji kawai!” Hajiya ta faɗi tana ficewa, Hajiya na fita Azima ta kulle kofa ta hau gadon Hajiya ba daɗewa bacci ya kwasheta, Hajiya kuwa tana parlour tana jiran Azima ta gama gyara da fito yau ne gobe ne shuru,har bacci ya fara kwasar Hajiya, ta farka taje ta tura kofar ta jita a gangame! Bugawa Hajiya ta hau yi amma a banza har ta gaji, tana bugawa tana aunawa Azima zagi, dakin Zuby taje ta buɗe mata Zuby tace ita ba zata tashi ba ta riga da ta kwanta,haka ma Baby ita kam har da yiwa Maman tsawa ta tayar da ita a bacci, haka Hajiya ta dawo parlour ta kwanta a kujera nan ta kwana.

   Azima bata farka ba sai bakwai na safe tana tashi ta wargaza dakin Hajiya ta kwashi kudin dake dakin kafin ta buɗe dakin ta fito,nan ta ga Hajiya na bacci wani murmushi ta yi na gefen baki, dakin Lantana ta nufa taje ta sameta zaune tana karatun al'kur'ani mai girma, wani wawan jiri ne ya ɗibi Azima,Lantana ganin haka yasata rufewa ta tashi da sauri ta kamo Azima tana tambayarta lafiya? Azima ta ce

“Lafiya lau! Ga wannan kudi ke da mai jiran ƙyauren gidan nan(gateman) ku bar gidan nan ku koma garinku,ke yar wace gari ce?”
“Ni ‘yar can cikin kauyen kano ne, amma meyasa zamu tafi?” cikin tsawa Azima tace
“Bana son tambaya zaku tafin nan ne ko zaku shiga sahun wa inda za a binne?” jin haka yasa Lantana karban kudi jikinta na rawa dan bata taba jin murya nai amo da firgici irin wannan ba harta kayanta tace ta yafesu dama tsumokara ne, ta ce “ki yafeni Hajiya Azima idan na bata miki sai wata rana” bata jira amsar Azima ba ta fice, ta kai wa Mai gadi yana tambayarta miye tace masa kawai ya yi ta kansa, sai da Azima ta tabbatar da sun bar gidan kafin ta ja kofa ta koma, shiganta parlour ya yi dai-dai da farkawar Hajiya, bata yi wata-wata ba tasa hannu ta fizgi Azima ta gaura mata mari dai-dai sadda Baby da Zuby suke buɗo kofa dan lokacin haɗa musu tea ya yi, Zuby ce ta ce
“Hajiya me ya faru haka?” cikin kumfar baki Hajiya ta ce
“Wannan ‘yar jeji ni zata bari na kwana a parlour?”
“A parlour kuma?” cewar Baby tana bin Azima da kallo da kanta babu dankwali sai gashinta da ya rufe mata fuska
“Ke ba magana ake miki bane?” cewar Zuby tana hararan Azima dake tsare jikinta na tsuma, hannu Baby tasa taja gashin Azima yana kwashe na fuskarta nan Azima ta ware kwayar idanunta a kan Baby,wani ihu Baby ta saki tana ja da baya, Zuby tasa hannu zata juyo da Azima dan ta ga me Baby take yiwa ihu kafin ta juyo da Azima, Azima ta juyo ta hura mata baƙin hayaki a fuskarta, kafin su farka tuni Azima ta yi juyi ta zama rabi mutum rabi macijiya, fadin yadda su Hajiya suka shiga firgici ba zai misaltu ba, ihu suke yi suna kiran Munir,dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce
“Ya ri ga ku mutuwa! Yanzu a cikinku wa zai bisa na biyu? Bari na kawo muku shi ku gan shi” Azima ta faɗa tana shiga dakin ta naɗo munir da jelarta ta zo ta jefar da shi a gabansu a tsakiyar parlour, wani kuka su zuby suka saka ita da baby hajiya kuwa jiki na kyarma ta takure jikinta gefe daya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button