AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)
Follow me on wattpad,@Fateemah’0
????????????????????
PAID.
????️=4️⃣1️⃣↪️4️⃣2️⃣
Mai gadi ne ya leƙo jin ana kwankwasa kofa ya ga bafulatana tana tsaye kanta a duke,
“Baiwar Allah lafiya kuwa?” cewar Mai gadi,kuka Azima ta saka tana fadin ya taimaka ya yi mata magana da masu gidan,mai gadi ya ce
“Baiwar Allah zan gaya miki gaskiya,me wannan gidan baya ma kasar gabadaya! Ya jima baya nan,iyayensa ne a gidan,idan kuma wani neman taimako kikeyi to wallahi ba zaki samu komai a wajansu ba,dan basu kyauta” Azima ta ce
“Ina da bukatar yi musu aiki ne,don Allah kayi mini magana dasu, ni ba kudinsu nake so ba”
Ganin yadda ta dage yasa Mai gadi fadin “to ɗan shigo daga ta ciki sai nayi miki magana dasu” Azima tana sa kafa a gidan gabanta ya bada dammmm!! Da karfi sai da ta danne saitin zuciyarta,mamakin faduwar gaban nata take yi, a kan benci mai gadi ya nuna mata ta zauna shi kuwa ya nufi babban parlourn gidan da sallama, wata mata ce zaune a hakimce a kujera ta ɗora daya a kan ɗaya tana danna waya,sallamar mai gadi ya sakata ɗagowa tana kallonsa da kyar ta amsa,
“Allah ya taimakeki ranki shi daɗe”
“Lafiya kuwa Ɗan’Bala?”
“Wlh Hajjaju wata ‘yar fullo ce a waje take ta faman kuka a taimaka mata tana neman aiki, ina ga irin wa inda ‘yan fashi suke kai musu farmaki rugarsu ne, su kashe musu kowa su kwashe shanukansu, wlh Hajjaju abun tausayi” shuru Hajjaju ta yi kafin ta kalli Dan’Bala ta ce
“Je ka shigo da ita” Ɗan’Bala ya amsa da to sannan ya fice da sauri ya zo ya samu Azima dake zaune ya ce
“Zo mu shiga Hajjaju na kira” ba tare da Azima tayi magana ba ta tashi ta bi bayansa, suka shiga parlourn, sosai Hajjaju ta karewa Azima kallo sannan ta kwala kiran wata mai aikinsu
“Hadiza! Hadiza! Hadiza!” wacce aka kira da sunan Hadiza ta amsa da na’am da fito da sauri ta duƙa a gaban Hajjaju, Hajjaju ta ce
“Hadiza je ki yiwa Maman Hanan magana ki ce mata da sauko kasa yanzu” Hadiza ta amsa da to,sannan ta hau da sauri, a tare Hadiza suka sauko da wata dakekkiyar mata wacce ita ma da ka ganta zaka san ta yarda da kanta, tana tafiya a gaba Hadiza na binta a baya,tana saukowa ta ce
“Lafiya kuwa Maman Beenah?”
“E lafiya lau mai aiki ce dama za a dauka shine nace a kiraki tukunna”
“E ya kamata ai, idan yaso sai ta dinga gyara su dakuna tana sharewa da gogewa dan aiki ya masu Hadiza yawa”
“To shikenan sai mu kirasa anjima mu gaya masa mun kara daukar mai aiki dan ya tanadi kudin biyanta ita ma”
“Ah to shine magana ai,idan bai kashe mana kudin ba munyi wadaka yadda muke so ma wa zai yi ma wa? Tunda Uwar da Uban duk sun mutu” Maman Beenah ta yi murmushi ta ce
“Ai muyi kokari da ya dawo mu haɗa masa kannanmu ya aura dan mu ci gaba da tatsarsa”
“Wannan magana taki haka take, Hadiza shiga da wannan ki nunnuna mata abunda ya dace, su dakuna zata dinga gyarawa, dakin su Hanan da Beenah da Hanif sai kuma namu dakunan, sai idan AL’MAZEEN ya dawo zata dinga gyara masa nashi dakin dan haka har part din Al’mazeen zaki nuna mata amma ba yanzu ba”
“Tukunna ma ya sunanki?”
“AZIMA BANJU!” cewar Azima kanta a duƙe
“To kin dai ji aikin da zaki dinga yi mana ko? Za a dinga baki dubu goma a wata”
“Na gode sosai” cewar Azima, Maman Hanan ta ce
“Kuje da ita Hadiza”
“To Hajiya,Azima zo muje ki ga dakinmu” da kyar Azima ta miƙe dan tun lokacin da aka kira sunan Al’mazeen ta nemi natsuwarta da karfin halinta ta rasa, a zuciyarta take tambayar kanta waye shi Al’Mazeen din? dole ta ga waye shi dan daga kira sunansa sai jikinta ya yi sanyi? anya zata iya zama a gidan kuwa? daga fara saka kafarta a gidan tayi tuntube da faɗuwar gaba,yanzu kuma an kira suna zuciyarta ta tsinke, jin babu kuzari a gangar jikinta yasata b’allan gashin kanta ta sa a baki ta lumshe ido tukunna taji ta dawo dai-dai, Hadiza ce ta nunnuna mata abubuwa dasu dakunan da zata dinga gyarawa a sama da kasa,amma bata haura da ita part din Al’mazeen ba, kasancewar an ce mata ba yanzu za a nuna mata ba,Azima kuwa tace ba zata iya jira ba ko da yaya ne sai ta shiga part din ta gani.
????????????????????
Yau kwanan Azima biyu a gidan,kuma cikin ikon Allah babu wanda ya shiga hidimarta kamar yadda bata shiga tsabgar kowa, sunan wanda ake kira da AL’MAZEEN shine ya tsaya mata a rai, ga shi bata san part dinsa ba,kuma ba zata iya tambayar su Hadiza ba,dan bata son yawan magana , Beenah har kyautar kaya suka mata,kuma babu wanda ya taba yi mata magana a kan rufe fuskarta da take yi kasancewar ansan kunya gado ce ta fulani, ko Hanif da yake namiji baya shiga hidimar Azima,idan kuma gyaran daki ne tana shiga zata hura iska ta bakinta dakin shi da kansa zai gyara kansa,idan ta shiga daki ko minti goma bata yi zata fito da an shiga za a gansa fesss! shiyasa daga Maman Hanan har Maman Beenah suke jin dadin zama da Azima,ita kuwa Azima yanzu tunanin kisa ya fita a ranta sai son ganin waye AL’MAZEEN.
????????????????
A kwana biyu kuwa Aziza ta ɗan sake dasu Mom da Sultana barin ma Sultana da bata nuna mata ƙyama tana janta a jiki, ranar da ta cika kwana biyar a gidan ganin jikin nata da sauki sosai yasa Sultana zuwa wajan Mom tace Mom ta basu kudi zata kai Aziza wajan gyaran gashi, Mom tayi murmushi sannan ta bata kuɗi ta ce driver ya kai su.
Bayan sun je shagon salon din za a buɗewa Aziza fuska ta hanyar kwashe mata gashi tayi saurin saka tafin hannunta a fuskarta dama da kyar ta yarda ta cire hijabinta, dariya Sultana ta sa tana fadin
“Duk rowan da kike mana na ganin fuskarki yau dai dole ki bude” da kyar mai salon ta lallaba Aziza tana kwashe gashin Aziza tayi saurin rufe idonta gam, kan aka hau wanke mata kai ɗin, Sultana na zaune a gefe wayarta ta yi ƙara tana dubawa ta ga Brother da sauri ta daga tace
“Assalamu alaikum, Brother ina kwana?”
Daga can ya sauke ajiyar zuciya ya ce
“Lafiya lau Sultana ya kuke? Ina Mom? Na kira wayarta bata ɗaga ba,ki gaya mata yau ina hanya”
“To Brother sai dai nima na kirata a wayar”
“Sabida me? yau ba saturday ba ai ba skull, ko kina skull din ne?”
“A’a Bro ina shagon salon na raka Aziza ne a wanke mata kai” jin sunan da ta kira yasaka shi katse wayar da sauri, dan tun ranar da ya buge yarinyar nan yake mafarkin tana neman taimakonsa,tun abun baya damunsa har ya koma damunsa, da fari ya yi tunanin ko dan ya bugeta ne amma a yanzu ya kasa fahimtar halin da yake ciki, da ya ji Mom tace ta dauketa aiki har cikin ransa bai so ba amma dai bai ce komai ba.
Sultana kuwa mamakin katse wayar ya yi tayi,daga baya kuma ta ce
“Uhum Yaya kenan” wayar Mom ta kira bata ɗaga ba itama, ta kalli mata mai salon din ta ce
“Dan Allah Anty ki gama mata da sauri zamu tafi gida Yayana wai yana hanya”
“Ai gashin nata ne dayawa wlh ga tsayi ga cika tabarkallah Ma sha Allah!” Sultana ta yi murmushi.