AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

 Kusan mintuna talatin aka kwashe ana wankewa Aziza kai idonta kuwa yana lumshe ko da wasa bata buɗe ba, bayan an gama ne aka busar mata da kai din aka shafa mata mayuka masu kyau da ƙamshi aka taje mata shi sannan aka sa ribbom aka daure mata shi, Ma sha Allah! shine Abun da Sultana ta faɗa ta ciro wayarta tana daukar Aziza hoton wacce ta yi saurin maida hijabinta tana rufe fuskarta,bayan Sultana ta biya kuɗin mai salon suka mata godiya suka fice tana ta yabon kyawun Aziza da dogon gashinta,ita dai Aziza tana murmushi ne kawai sama-sama,    bayan sun shiga mota Sultana ta ce

“Yanzu mu fara biyawa mu karbo kayanki na wajan tela, yawwa dama ina so na tambayeki,kin iya karatu?”
Aziza ta gya ɗa kai ta ce
“Nayi sauƙan al’kur’ani mai girma a kauyenmu, sannan na karanta litattafai da dama,na iya rubutu kamar irinsu ko da wasika idan Baffanmu zai rubuta idan rubutun tayi masa yawa ina tayasa rubutawa amma ba da irin rubutunku ba, da harafin su Alif kamar ajimi haka”

Sultana ta ce

“Ahh Ma sha Allah ki ce malama ce” ta faɗa a mamakince dan kuwa ta sha mamaki ɗin sosai, murmushi Aziza ta yi ta ce
“A’a ina dai kan neman ilmin”
To shikenan zan koya miki karatun hausa da turanci ta yadda zaki iya duka,idan har kina ganewa da wuri zan cewa Yayana ya nema miki skull mafi kusa da saurin ganewa,sannan matsalar idonkin nan ya nema miki medicalglass”

“A’a Anty Sultana karki gaya masa,ki bari kawai idan kika koya mini ma ya isa, idona kuma haka yake haka aka haifeni dan Allah ko wa Mom ne karki ce mata komai” Sultana ta yi murmushi ta ce
“To shikenan”

  Bayan sunje sun karbo kayan suka koma gida a daki suka samu Mom, Mom tace "sannunku da dawowa 'yan matana har kun dawo" Aziza ta duka kasa Sultana kuma ta zauna a gefen gadon Mom, ta ce

“E Mom mun dawo barka da gida, dazu muna shagon salon Yaya ya kirani wai yana hanya mun kiraki baki daga ba”
“E munyi waya da shi daga baya,kema na kiraki bai shiga bane, lokacin da ya kirani ashe na tashi na bar wayar a parlour shiyasa, yanzu dai ku tashi kuje ku gyarawa Yayan naku dakinsa, idan kun gama sai ku shiga kitchen” dan mom bata yarda da lalaci ba dan babu irin girkin da Sultana bata yi shiyasa da shike basu da yawa a gidan kuma ba yara garesu ba shiyasa mai aiki daya kawai suke dauka, suka amsa da to, Aziza ce ta fara tashi ta fita, Sultana ta ce “zo muje part din Yayan” tayi gaba Aziza na binta a baya, suna fita sai ga wani ɗan ƙofa madaidaici Sultana ta buɗe suka shiga,parlour a kasa har da step wani sashene mai zaman kansa a wajan tabbas an tsara parlourn ya tsaru, Aziza matowa tayi da kallon parlour,idonta ne ya sauka a wani pic babba a parlourn shi daya da kuma wani a gefe su biyu, dukkansu fuskarsu babu murmushi,tabe baki Aziza ta yi,dan ita bata ga abum gyara a wajan ba,ganin yadda take kallon hoton ne yasa Sultana fadin “wannan shine Babban Aminin Yaya baya da wani sama da shi, a tare suke a america tare suka yi karatu gabaɗayansu kuma likitoci ne, karki ga fuskarsu haka a haɗe barin ma yadda kika ga na Abokin Yaya,to wlh yafi Yaya Nawaz sauƙin kai,kawai dai shi magana ce bai cika yi ba da dariya,amma idan kina neman zafin zuciya kika samu Yaya Nawaz kin gama” jinjina kai Aziza tayi ba tare da tayi magana ba,suka hau sama yadda k’asan ya tsaru haka ma saman ya tsaru haka de ta dinga bin Sultana har suka gama suka saka masa turaren wuta sannan suka wuce kitchen suka hau girki, dama Sultana na koyawa Aziza yanayin girkinsu,duk abunda ta koya mata sau daya kuma cikin ikon Allah ta riƙe kenan babu mantuwa, idan tazo yi kuma sai tayi wanda yafi na Sultana daɗi, haka suka yi girki a tare suka gama duk da ba wani hira sukeyi ba,tunda Sultana ta fahimci Aziza bata son yawan magana yasa itama bata takura ba,ita kuwa ba zata fahimci tashin hankalin da take ciki bane,bata fata su gano cewa ita ba mutum bace macijiya ce har su rabu tinda zama dasu na wucin gadi ne, bayan sun gama girki Sultana ta ce
“Aziza je kiyi wanka ki canza kaya, sai ki kwanta ki huta idan kika huta da dare sai mu fara karatun ko?”
“Dazu fa kafin muje wajan wankin kai nayi wanka”
“E na sani,ai ita tsafta bata yawa sai dai tayi kaɗan, zaki dinga yi ne dai-dai gwargwaɗon iyawarki,kuma gwara ki saba da shi tun daga yanzu dan bamu sani ba watakila Mom ta samu surki a nan garin” wani wawan faduwar gaba ne ya ziyarci Aziza ta sake maimaita kalman sirki a ranta, da kyar tayi murmushin karfin hali ta amsa da to a sanyaye sannan ta wuce daki,itama Sultana sama ta haura, Aziza na shiga daki ta wuce toilet, tana shiga ta maida kofa ta rufe ta rintse idonta ya sake komawa fari, fatar jikinta ma fari yana sab’ulewa, daga ƙasarta ta fara rikiɗewa nan ta zama rabi mutum rabi macijiya sannan ta zauna a gefen bath din wanka ta hau kuka, tunowa da maganar Arɗo da Baffa Mandi, na cewa ba zata warke ba har sai sunyi aure, kuma ita warakanta yana tattare da Azima wacce bata ma san a wani duniya Azima take ba, sai bayan da ta gama shan kukan nata kafin ta yi wankan ta fito.

????????????????

 Sai huɗu Nawaz ya samu damar isowa, ko da ya iso wajan Mom ya nufa nan take masa sannu da zuwa tare da fadin

“Nawaz sai yanzu?”
“Wlh Mom motata ce ta ɗan samu matsala a hanya sai da aka mata gyara”
“Subhanallahi! Karfen nasara babu tabbas Allah ya kara kiyayewa”
“Amin Mom bari na samu na ɗan watsa ruwa sai na fito na ci abinci,ina Sultana?”
“Ba mamaki tana dakinta,bata ji shigowarka ba ai da ka ganta da gudu” murmushi ya yi kawai ya fice, part dinsa ya shiga ya samu na tashin kamshi bai tsaya wani bata lokaci ba ya yi wanka ya shirya ya fito, ji yayi ba zai iya komawa babban parlour ba dan haka ya kira Sultana ta kawo masa abincin part dinsa.

     ????????????????

MOMYN AHLAN✍????
GARKUWAR MACIZAI????????
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

PAID.
????️=4️⃣5️⃣↪️4️⃣6️⃣

Hakika wannan mafarki ya tayar masa da hankali, ko da ya farka da washe gari jikinsa a mace, da kyar ya gama shiryawa ya fito ya yiwa Mom sallama da shike driver ne zai kaisa ya dawo, shiyasa zasu yi fitar wuri, bayan sun gama sallama da Mom suka rakasa har bakin mota, sai ware ido yake yi inda zan hangi Aziza amma bai ganta ba, kallon Sultana ya yi ya ce
“Ina Aziza ne?”
“Ina ga tana dakinta bari na dubota”
“Noo leave her” ya faɗa yana jan murfin mota Mom tana kan yi masa addua yana amsawa da amin, Mom da Sultana basu koma cikin gida ba har sai da motar ta fice a gate gabadaya aka ja gate din kafin suka koma,ko da suka shiga Sultana ta wuce dakin Aziza ta sameta zaune tana ninke kayan Mom da ta wanke, Sultana ta ce
“Aziza baki fito kinyiwa Yaya Allah ya kiyaye hanya ba har sai da ya tambayeki wlh”
“Ayye ban san ya fita ba da shike ina nan ina ninke kayan Mom ne” ta faɗa ba tare da ta dago ba, alhali taji sadda suka sauƙo dasu Mom har sadda ya shiga mota duk tana tsaye tana leƙensu ta window, sai da ta ga motar ta fice a gidan kafin ta koma daki, Sultana ta ce
“To ke miye haɗinki da kaya ina Buba yake?”
“Wlh jiya ne yaji ciwo a hannu shiyasa na karba kayan na wanke”
“Subhanallahi! Allah ya kiyaye gaba amma ai sai ki faɗa ba wai ki wankesu da kanki ba da an nemo mai wankewa,yanzu dai ki gama ɗin sai ki zo muje Mom ta aike mu karbo kulolin azumi wanda ake abincin sadaka dasu gidan wata kawarta a nan malali”
“To Anty Sultana bari na karasa gani nan zuwa”
“To kiyi sauri ki shirya, saura kuma wlh ki zunduma hijabin kin nan, dan Allah ki nemi abaya ki saka ki yafa gyale akwai gidan da zaki rakani mu shiga tare Mom ta bamu sako ma a gidan” da to Aziza ta kara amsa Sultana, Sultana tana fita Aziza ta sauke ajiyar zuciya tana fadin “Allah ya kaika lafiya Hamma Nawaz, ba mamaki ba zaka dawo ka sameni ba” ta fada tana mai lumshe ido, saurin kwashe kayan ta yi ta kaisu dakin guga, sannan ta koma ta shirya shap-shap tasa doguwar abaya baƙi ta dauki ash’color din gyale taja gashin kanta ta nannaɗesa ta daure a tsakiyar kanta ta dau hula ta saka kafin ta dauki mayafin ta yi lullubinta kamar kodayaushe,ko da ta fito parlour Mom da Sultana suna parlour Mom tana kara ba wa Sultana saƙo, itama ta yi shigar bakin abaya, tana fitowa Sultana ta ce
“Yawwa ko ke fa” murmushi kawai Mom tayi ta ce
“Ma sha Allah ‘yan matana, Allah ya kawo miji na gari,kodayake ma yanzu kam sai dai nayiwa ‘yata Aziza dan ita Sultana rana kawai za a saka”
A sanyaye Aziza ta ce
“Lahh Anty Sultana shine baki gaya mini ba? To Allah ya kaimu Allah ya sanya alkhairi” Mom ta amsa da amin Sultana kuwa ta dukar da kai tayi tana murmushi,bayan Mom ta gama basu saƙon ta ce
“Dan Allah karku kai magriba,Sultana karki ga dan Nawaz baya nan ku kai magriba kin san dai ko da wani lokaci kiran waya yake yi,da ya kira kuma zai ce ina kike, dan haka kuyi ku dawo”
“In sha Allahu Mom” suka faɗa suna ficewa, duk inda aka aikesu nan suka je, har gidan surakanan Sultana, a gidan kuwa wani ƙaninsa ya ga Aziza sai kallonta yake yi, har sai da ya biyo Sultana yana faɗin
“Anty dan Allah wannan fa?”
Murmushi Sultana ta yi tana faɗin
“Kanwata ce,kana ciki ne?”
“E wlh Anty ina ciki”
“Lallai kam to sai ka gayawa Yayanka”
“To Anty shi da baya kasar ki kirasa ki fara gaya masa,kinga ma sai a haɗa bikin da naku”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button