AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ahh lallai Walid baka da kunya, wato ma a haɗa da namu?”
“E mana Anty,kodayake ma ku da ba a saka ranar ba, sai a fara namu kafin Yaya ya dawo ke kuma kin gama skull kafin nan kema kin kara girma Anty” ya faɗa cikin tsokana, Sultana ta ce
“Wlh Walid ka rainani,zan haɗaka da Yayanka kuwa”
“Allah ya baki hakuri Anty,ni dai dan Allah ki fara min kamu” banza da shi Sultana ta yi ta shiga mota ta cewa driver yaja su tafi,basu tsaya ko ina ba sai gida,suna isa Mom ta musu sannu da dawowa tace musu idan sun huta su shiga kitchen suyi girki suka amsa da to.
@@@@
Da washe gari sai dare Mom ta samu damar yin waya da Nawaz ya shaida mata cewa ya isa lafiya, Mom ta ce
“Ma sha Allah haka akeso,Allah ya taimaka ka gaishemin da son”
“Zaiji Mom,ina Sultana?”
“Suna can daki ita da Aziza suna karatu, dama kuwa ni ina son yi maka magana a kan yarinyar inaso zan nema mata makaranta, tana da kaifin basira, wlh basu kai sati da fara karatu ba amma karka ga yadda kanta ke ja,abun mamaki” Shuru Nawaz ya yi na dan wani lokaci har sai da Mom ta kuma cewa
“Nawaz bakaji me nace bane?”
“Naji Mom duk yadda kikayi dai-daine, Allah ya baki lada”
“Amin Nawaz” hira suka ɗan taba kafin suka yi sallama da shi.
????????????????
Bayan sati biyu da tafiyar Nawaz abubuwa da yawa sun faru daga ciki kuwa harda fara azumi da aka yi, sosai a wannan wata ta ramadan Aziza ta dage da addua Allah ya takaita mata wahalar neman yar uwarta su samu su koma gida, dan ta ƙosa ta koma ta ga iyayenta,kullum da Hajja take kwana take tashi a ranta har ma da Baffanta, ta maida lamuranta ga Allah.
Ta bangaren Azima kuwa ta kasa gane meke mata dadi, dama duk azumin duniya ita kam ba yinsa take yi ba, to wannan din ma haka ta kasance dan ko daya bata yi ba, sosai kuma take sakawa su Hajjaju ido, duk wani ƙullin da suke yiwa AL'MAZEEN.
Ana azumi lafiya da yardan Allah, tunda Nawaz ya bar nigeria ya kasa samun natsuwa, ga mafarkin Aziza da ya gallazawa rayuwarsa wanda ya rasa ya zaiyi da wannan mafarki, ga shi ya kasa gayawa kowa, wanda hakan har rama ya fara saka shi, wanda da an tambayesa zai ce azumi ne kuma ya haɗa masa da ba a gida yake yi ba shiyasa.
Ana saura kwana uku sallah Sultana ta kai musu dinki wajan telarta inda ya cire musu zuƙa-zuƙan dinkuna na gani na fada, laces kala biyu, atampa kala uku, sai shadda da material kala ɗaɗɗaya, da gyalensu da takalminsu dasu sarƙa da ɗankunne, da komai da komai, hakika Mom ta yi kokari,Sultana kuwa ta yi bajinta wajan zabo musu kaya masu kyau, ita ma Azima anyi mata, amma sam basu gabanta dan bata saka a ranta zata yi wani kwalliyar abu sallah ba.
Ana gobe sallah sai aikin suke yi dukkansu a kitchen har da Mom, Sultana ta ce
“Mom wlh zan yiwa Walid ba dadi, kinga yadda ya takura min wai yana son Aziza?” Mom ta yi murmushi ta ce
“Kai yarinta, duka-duka nawa kike bare kuma Walid? to kuma aje ga maganar Aziza wacce take da 15, Aziza ki maida hankalinki a kan karatunki kinji ko? In sha Allah bayan sallan nan zaki fara zuwa university dinsu Sultana tunda Allah ya baki kwakwalwa karki biyewa shirmen Walid kar ma ki fara kulasa, idan Khalil yaji ma ransa ne zai b’aci” Aziza a ranta ta ce
“Ina kuwa nake da lokacinsa,da yasan wacece ni ba zai so kara yin magana da mai irin sunana ba ma” a fili kuma ta ce
“Ni Mom ina da burika da yawa bana da lokacin kulasa”
“Yawwa Azizata” cewar Mom suka ci gaba da aiki har karfe sha biyun dare kafin suka tattara suka kwanta, da washe gari tunda sukayi sallar asuba basu koma bacci ba, abinci sukayi dukkansu har da Mom, karfe takwas da rabi suka gama, Sultana ta ce
“Aziza kiyi wanka da sauri ki zo muje masallaci” Aziza ta amsa da to.
Wanka sukayi suka saka shaddarsu, sannan suka saka hijabansu mai alkebba da takalmansu, suka fito har da Mom itama da ta dake cikin lace dinta, gabadayansu zasuje masallaci dan Mom tace abu daga shekara sai shekara nan ma sai mai tsawon rai wanda Allah ya nufesa da gani.
Haka akayi idi lafiya, sai fatan Allah ya amshi ibadunmu na alkhairi ya yafe mana kurakurenmu amin.
@@@@@@
Bayan sun dawo gida, nan yan uwa da abokan arziki suka hau zuwa ana yiwa juna barka da sallah, masu kawo abinci suna kawowa wa inda ake kai musu ana kai musu, Mom tana haɗawa tana bayarwa ana miƙawa bayin Allah, dasu lemuka da purewater, da kuɗi haka Mom ta dinga rabo, Sultana kuwa tana cikin yan uwanta ana shan su pics ana gaisawa an dade ba a hadu ba, Mom ce ta shigo babban parlour ta kira sunan Sultana ta ce
“Sultana ina Aziza ne kam?”
“Wlh Mom tun da muka dawo inaji bayan mun gama hada abincin da za a fita da shi ban ƙara ganinta ba, dan tun sadda baki suka fara shigowa ban ganta ba” Mom ta ce
“Kin san Aziza bata son mutane kamar ma kunyarsu takeji yanzu haka to ba mamaki tana daki”
“Wlh kam Mom kunyar mutane takeji,ko mu a gida Aziza bata gama sabo damu ba bare kuma yau ta ga mutane ai ba zata fito ba,amma bari naje na fito da ita dan yau yawon sallah zamu je a ga yan uwa da abokan arziki” Mom ta ce “dubota to, sai ku shirya ku fita nima zanje gidan Hajiya Hauwa(gidan sirkan Sultana, Hajiya Hauwa ita ce Mamansu Khalil wanda zai auri Sultana) dan yau muma zamuje ziyara ne”
“To Mom” Sultana ta faɗa tana tashi da sauri ta yi dakin Aziza a lokacin ta gama kukanta tana tunanin wan can sallar tana gida tare da Hajjanta da Baffanta, Sultana tana shigowa Aziza na fitowa daga toilet ta wanke fuskarta, Sultana ta ce
“Ohh Allah Aziza, sabida kinji gidan a cike shine kika boya a daki? To maza ki shirya, zamuje yawon sallah”
“A’a Anty Sultana bana son fita,bazan je ba”
“Wlh sai kinje, Mom ma fita zata yi,yau ranar zumunci ce, yau fa ranar farin ciki ne amma ke na ga kamar ba baki farin ciki ko mun yi miki wani abu ne?”
Aziza ta girgiza kai,
“To idan har ba mu miki komai ba ki shirya yanzu ki canza kaya ki saka atampa,bari nima naje na canza kaya” Aziza ta gya ɗa kai, Sultana ta fice.
har Sultana ta shirya ta sha makeup ta kashe ɗauri ta yi pics ta turawa Khalil dinta, sannan ta fito dauke da handbag dinta ta shiga dakin Aziza ta sameta ta canza kaya amma tana zaune tana riƙe da ɗankwali a hannunta, Sultana ta ce
“Ba kiyi kwalliya ba?”
“A’a Anty Sultana ba zan yi ba”
“A yau sallan? Wlh baki isa ba” Sultana ta fada tana daukar powder ta hau gogawa Aziza a fuska, sannan ta shafa mata red lipstick, duk da fuskarta taki bari ya fito sosai amma ta yi kyau, sannan Sultana ta kashe mata ɗauri, Subhanallahi! Aziza ta yi kyau sosai, nan Sultana ta daukesu hoto, duk da Aziza bata ɗago fuskarta sosai ba, sannan bata ɗaga idonta ba.
Bayan sun fito parlour suka sake yi da Mom, sannan suka fice a gidan, a mota Sultana ta turawa Nawaz pics din tare da rubuta masa HAPPY SALLAH BRO NAWAZ.
Ko da Nawaz ya buɗe ya ga hotunan yan uwa da abokan arziki, Allah Sarki gida dadi,ya fada yana murmushi a ransa, wani hoto ya bude ya ga Mom sai da ya sumbaci hoton, sannan ya sake buɗe wani ya ga Sultana ta yi kyau sosai ya ce "nice sis" ya sake bude wani ya ga da Mom da Sultana ya yi murmushi yana faɗin
“My world” wani hoton ya sake buɗewa ya ga Sultana da Aziza amma bai ganeta ba, sai da ya kara buɗe wani ya ga tana dukar da kai kamar amarya kafin ya ganeta, sun sha lalle kuwa, wani hoton ya sake buɗewa Aziza na zaune a mota bata ma san sultana ta dauketa ba, lumshe ido Nawaz ya yi yana karanto adduar masifa dan Aziza ji yake yi ta zamo masa masifa, kansa ne ya hau sara masa sai da ya ɗan ji dai-dai kafin ya fita dan yaje ya samu amininsa su ɗan fita suma.
????????????
Kwana hudu su Sultana suna yawo,kullum kuma idan suka yi wanka sai Sultana ta musu hoto ta turawa Nawaz, tun yana buɗewa har ya daina buɗewa,dan ganin hoton shike kara masa mafarkai a nasa ganin kenan.
????????????
Ta bangaren Azima ko kaɗan bata yi wankan sallah ba bare shigar sallah, haka ranar sallar ta wuni tana jin haushin kowa,kiris ya rage abincin sallar ma bata watsa masa dafi ba, dan haka kawai ta ga kowa na murna da farinciki ita kuma tana ji kamar zuciyarta ya fashe da baƙin ciki da takaici, haka aka gama cin sallah Azima bata yi shigar sallah ba illa kayan fulaninta da ta dinga yawo da shi har satin sallah.
Bayan komai ya daidaita haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, bayan sallah da sati biyu Aziza ta fara zuwa university din su Sultana, bata shiga hidimar kowa kasancewar tasan ita din ba mutum ba ce,haka zata je ta dawo,idan kuma Sultana na da paper su kan je tare su dawo tare, tana nan tana tara kuɗinta har ma da wa inda ta samu da sallah dan tace kwanan nan zata bar gidan.
????????????????????
“Innalillahi wa inna ilayhirrajiun! Dan Allah Jauro ka taimakawa ƴata kar mayyar nan ta kasheta!” ya faɗa yana mai riƙe kafar Jauro, Jauro ya ce
“Wlh Malam Halliru na kasa yiwa ‘yarka magani, wannan mayyar tana da taurin kai” Salti dan gidan Jauro ya ce
“Wlh Baffana baya da baiwa irinta Baffa Magaji, dama wajan Baffa Magaji kuka je da yanzu ta samu sauki, amma ku fara zuwa kuyi kamun kafa da Sarki Chubaɗo”
“Wlh zanci ubanka Salti! Zaka fita mini ka bani waje ko sai na bazar da kai da sanda?” Salti ya miƙe yana kunkuni yana fadin
“To dan na fadi gaskiya kuma Baffa” Salti na fita, Malam Halliru ya ce
“Hakika munyi kuskure, dole wajan Magaji zamu je neman taimako”
????????????
MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
(???? Macizai ne????)
MALLAKAR.
ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.