AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)
Follow me on wattpad,@Fateemah’0
????????????????????
PAID.
????️=4️⃣7️⃣↪️4️⃣8️⃣
Wajan Sarki Chubaɗo Malam Halliru yaje yana kuka yana ba wa Sarki yankin fulanin kwana hakuri a kan ya taimaka yasa baki ya yiwa Magaji Bawa magana ya taimaka ya duba masa ‘yarsa, Sarki Chubaɗo cikin tunzura ya ce
“Ayhoo!! Ashe ku kuna son yaranku, shi da ku ka kora masa nasa ya yi yaya kenan? har kwanan gobe Jumala bata magana bata um bata um-um,nan ku ka daure Aziza kuna shirin kasheta! anyi haka ko ba a yi ba?” cikin kukan nadama Malam Halliru ya ce
“Munyi kuskure ranka ya dade! Amma ba laifinmu bane Jauro ne ya zugamu ya sa mana tsoro da shakku, dan Allah a taimaka mini” Sarki Chubaɗo ya ce
“Idan Jauro ya ce ku faɗa wuta zaku faɗa ne? idan har Magaji zai taimaka maka a nasa ra’ayin farillahi hamdu! amma idan ya ƙi wlh daga nan fada babu wanda zai saka baki” Malam Halliru ya amsa da ya yarda shi dai ayi masa izini yaje gidan Baffa, Sarki Chubado ya daga masa hannu alamun yaje godiya sosai Malam Halliru ya yi ya tashi da gudu har yana tuntube, bayan Malam Halliru ya tashi Wazirin kwana ya ce
“Ranka ya dade bana tunanin Magaji zai ƙi taimakawa Malam Halliru” Garkuwan Fulanin kwana ya ce
“Tabbas haka ne maganarka Waziri, Magaji Bawa Allah ya masa kyakkyawar zuciya,yana da tausayi da hakuri, yanzu haka sai ka ga ya taimaka masa” Sarkin Fadar kwana ya ce
“Ai Halin Magaji Bawa sak wannan Yarinya tasa Aziza, amma ka ga wannan shaiɗaniyar Azima hummm!” Sarki Chubaɗo ya ce
“Barewa ba zata yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, itama Azima Banju ke rayuwa a jikinta,ba zamu iya tantace ya halayyarta yake ba har sai an rabata da Banju wanda yake rayuwa a jikinta,ko kun manta da komai na jikinta yake rayuwa? Azima fa ba Azima ba ce BANJU ne, amma ni dai nasan Ɗawisu ba zatayi k’yal-k’yal banza ba” Garkuwa ya ce
“Tabbas hakane, ranka ya dade, an fa ja watanni rabon da su Azima da Aziza a wannan yankin, wlh har bana son haɗuwa da Magaji sabida tausayin da yake bani, ga shi dole mutum ya dinga tunanin yaran suna lafiya ko akasin haka! Babban abunji ma ita ce Azima,mu nan da muke yankin jeji ne ya muka iya da ita,bare kuma aje ga mutanen cikin birni da suke da yawa ɗin nan”
“In Allah ya yarda suna lafiya, Allah kuma shi zai ƙare bayinsa daga sharrin Banju, ina da kyakkyawar zato wa yarinyar nan Aziza, zasu dawo In sha Allah, sannu-sannu baya hana zuwa sai dai a daɗe ba aje ba, duk tsawon watanni ko shekaru su Azima da Aziza zasu dawo” cewar Wazirin kwana,Sarki Chubado ya ce
“Haka shima Magajin yake faɗi, zasu dawo In sha Allah,yanaji a jikinsa yaransa suna nan lafiya, kuma zasu dawo garesa”
“To Allah ya dawo mana dasu lafiya,ni kam ma Azizan nake son haɗawa da ɗan wajena” cewar Garkuwa, Waziri ya ce
“Kai yanzu Garkuwa a tunaninka ɗanka Garbiyo zai yarda ya auri Aziza ne? Ai kai ɗanka bai yi halinka ba sam, tsoron bala’i garesa sai kace ba bafulatani ba” Sarki Chubaɗo ya yi dariya ya ce
“Wlh ko cewa akayi Azima da Aziza sun warke bana tunanin Garbiyo zai yarda ya auri Aziza” Garkuwa ya yi murmushi ya ce
“Garbiyo kam ai sai a hankali amma idan ya samu Aziza rayuwarsa zata yi kyau dan na yaba da halin yarinyar sosai wlh”
“Hakane kam, yanzu dai adduar shine Allah ya dawo dasu lafiya” aka amsa da amin.
@@@@@@@
Baffa na zaune a bukka yana lazimi, Hajja kuwa ta samu zaman kofar bukka a kan tabarman kaba,idonta kamar kullum a bakin kofar gida, sallah ce kawai yake tayar da Hajja sai kuma tsakar dare idan zata shiga ta kwanta,duk da bacin sai dai sama-sama, ta ajiye idonta a bakin kofa tace ba zata gaji da jiran dawowar yaranta ba, zasu dawo gareta tanajin hakan a jikinta In sha Allah.
Sallamar Malam Halliru ne ya fargar da Hajja, amma bata amsa ba, sai Baffa da ya fito yana amsawa, Hajja ta jawo mayafinta tana gyara lullubinta, Baffa ya bada izinin shigowa, Malam Halliru ne da matarsa da 'yarsa a hannunsa suna kuka, suka zube a gaban Baffa, shuru Baffa ya yi yana kallon Malam Halliru kafin ya ɗora idonsa a kan 'yar dake hannun Malam Halliru,yana ganinta ya gano matsalar dake damunta, shuru Baffa ya yi ba tare da ya yi magana ba, Malam Halliru cikin kuka yake fadin
“Dan Allah Magaji ka taimakeni, wlh ita kenan mini yarinyar,na jima kafin na samu haihuwa ga shi Mayya tana shirin kashe mini ita ka taimakeni Magaji”
Shuru Baffa ya yi na wasu lokuta kafin ya ce
“Nima su kenan gareni, ɗaya ta gudu da kanta daya kuma kun kusa kasheta,inda daga karshe na koreta da kaina!”
“Hakika munyi kuskure Magaji kayi hakuri” shuru Baffa ya yi bai yi magana ba,ganin haka yasa matar Halliru zuwa ta kama kafar Hajja tana kuka, kallonta Hajja ta yi cikin sanyin muryarta ta ce
“Na san abunda kike ji a ranki a matsayina ta uwa na fahimci hakan, Baffan Biyu ka dubata dan Allah, su ci albarkacin macizai” Hajja na gama faɗi ta miƙe ta shiga bukka, Baffa kuma ya duƙa ya kama goshin yarinyar ya matse, ya rintse ido, ya gane mayyar dake jikinta, tana ɗaya daga cikin wa inda suka gudu ranar da ya haƙo kayansa, jin Magaji a kanta yasa ta hau kururuwa,Baffa ya ce
“Ai kin sake kawo kanki” cikin gurnani ta hau bai wa Baffa hakuri, Baffa ya ce
“Tun asalinki dama ke annoba ce, a wan can karan da ban ƙonaki ba dan na rufeki ne,yanzu kuma ƙonaki zanyi, dan idan na barki ban san wa inda zakiyi kokarin kashewa ba” Baffa na faɗin haka ya rintse ido tare da ɗora wa yarinyar wani farin dutse a kirji, ta sake ihu mai cike da amo, kafin ta koma tayi shuru zuwa wani lokaci aka ji ta ɗiff! Malam Halliru ya ce
“Magaji ba dai ‘yata ta mutu ba?”
” ‘yarka bata mutu ba Malam Halliru amma ta samu lafiya In sha Allahu, ku tafi gida, ga wannan kuma idan ta farka kuyi mata hayaki da shi” hawaye Malam Halliru ya goge ya ce
“Tabbas mutane irinka basu da yawa a wannan duniyar namu Magaji, dan Allah ka yafe mini, wlh Jauro ne, kayi hakuri dan Allah, Allah kuma ya dawo da Azima da Aziza lafiya” Baffa ya amsa da amin, Malam Halliru da matarsa suka fita suna kan yiwa Baffa godiya, Baffa kuma bukkar Hajja ya shige ya sameta zaune a bakin gadon karanta, ta yi shuru, zama ya yi kusa da ita ya ce
“Jumala?” hannu Hajja ta daga, ta ɗan yi shuru kaɗan kafin ta ce
“Karka damu Baffan Biyu,na rungumi kaddarata,amma ka san ita zuciya bata da ƙashi sai tsoka, duk yawan watanni ko da an shekara ni kullum abu daya nake gani” tana gama fadi ta tashi ta fice, Baffa ya ce
“Duk inda kuke Allah ya kareku, hakika idan har na kama Banju kisan da zan masa wannan karon ƙare ba zai tona ba, dama irin wa innan hatsabiban aljanun basu gane rarrashi , nima zan nuna masa waye ni!”
????????????????????
Bayan wata biyar.
Abubuwa dayawa sun faru a wata biyar din nan, daga ciki kuwa har da ‘yar gayu da Aziza ta zama turanci a bakinta raɗau, ga shi shaƙuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da Sultana,haka ma Mom bata nuna mata bambanci tsakaninta da Sultana, lokuta da yawa Aziza ta sha yunkurin guduwa amma sai ta kasa hakan, sakamakon yardan dasu Mom suka yi da ita, ga shi ita ba zata iya gaya musu gaskiya a kan ƙaryar da ta musu ba, ta rasa yadda zata yi, ga shi a wannan lokacin tana da bukatar ta canza wani gari ko Allah zai sa a dace.
akwai ranar da suke hira da Sultana take gayawa Aziza zasu je zaria bikin ƙawar Sultana din, to yanzu shirinta idan suka je bikin daga nan kawai ta gudu,idan har ta duba bata ga Azima a zarian ba, to zata sake canza wani gari, dan yanzu alhamdulillah ko da Mom ba ta bata kudin aikinta ba, a kudin da take samun alkairi ya isheta yawatawa neman 'yar uwarta, bare kuma alkairin da su Mom suka mata yafi abunda zasu bata sau dubu dari.
Ta bangaren Azima itama tana nan ta zama wata iri da ita, sai faɗi take yi ta shigo gidan da ya dameta duk sadda ta shigo gidan taji kamar an ɗaureta, ga shi duk yadda ta ci burin hawa can sama part din AL'MAZEEN abun ya ci tura, ala dole ta yi hakuri tana jiran dawowarsa,dan ta fara jin ƙishin-ƙishin a bakinsu Maman Hanan cewa nan da wata shidda AL'MAZEEN zai dawo, dan haka Azima ta koma tsumayin jiran dawowar Al'mazeen.
@@@@@@
Yau saura kwana uku su tafi zaria, Aziza na zaune Sultana ta shigo da sallama da waya a kunnenta hannunta dauke da kaya ta zuba a kan cinyar Aziza,kaya ne kala shidda kala uku iri daya, Aziza ta hau ɗaga kayan tana mamaki, zama a gefen gadon Sultana ta yi, tana ci gaba da wayarta bisa alama kuma da ƙawarta wanda za ayi aurenta suke waya, sai da ta gama wayar tsaf ta tabbatar mata cewa gobe da wuri zasu fito kana suka yi sallama,sannan ta waigo wajan Aziza ta ce
“Azizi baby, ga anko ɗinmu fa”
“Ankonmu kuma?” Aziza ta faɗa tana cikin mamaki tana ɗaga kayan, Sultana ta ce
“E mana, zamu je biki ne ba tare da kinyi anko ba? Wlh muna zuwa zaki zama kamar bare, shiyasa da na tashi na cewa Bros Nawaz ya turo mana da kudi nayi mana mu biyu” shuru Aziza ta yi sai kuma ta sa kuka, Sultana ta ce
“Miye haka kuma Aziza?” cikin kuka Aziza ta ce
“Anty Sultana, anya dawainiyyar ba zaiyi yawa ba? aiki nake muku amma kun maidani tamƙar yar gida, ni kuwa dame san saka muku? Sai dai na bi ku da addua ke da Mom,Allah ya saka muku da mafificin alkairi” hannu Sultana tasa tana sharewa Aziza hawaye ta ce
“Ni da Mom kawai? Shi kuma Yaya ɗin fa! Yana yawan tambayarki wlh idan muna waya da shi, Aziza kin riga da kin shiga ranmu ne wlh, muna jinki ne a jikinmu, shekaran jiya Mom ke faɗamin cewa ita tana miki kallo ne tamkar ita ta haifeki,kuma tana tausaya miki na rashin iyaye da yan uwa da kika yi, tace ba zata taba wulakantaki ba, dama wulakanci mu ba halinmu bane, duk wanda ya riƙe maraya tsakani da Allah,Allah zai ba shi lada, In sha Allahu ko neman aurenki aka zo yi ba zamu taba cewa ke ba yar gidan nan bane, Allah ne ya saka mana kaunarki a ranmu, sabida hankalinki da natsuwarki, wlh Aziza ina jinki tamkar kanwata uwa daya uba daya, a rayuwata ina son na ganni da ƙanwa, amma ana haifata Allah ya dauki ran mahaifinmu, har kwanan gobe Mom taki kara aure, Yaya shike mana komai da shike Allah ya dafa masa, idan har Allah ya baka dama da dukiya amfaninka shine kai ma ka taimaki wa inda basu da shi, dan haka ki daina sa damuwa a ranki ki saki jikinki nan gida ne, bari naje nayi waya da My Khalil” share hawayen da ya sake zubo mata Aziza tayi ta ce
“Na gode sosai Anty Sultana, Allah ya shayar daku ruwan alkausara, Sultana ta amsa da amin tana fadin
“An fa fara maganar tsaida aurena,wlh ana maganar sai da naji zuciyata ta buga”
“Kai Anty Sulty waya gaya miki?”
“Nima ba gaya min akayi ba,dazu ne zan shiga dakin Mom naji suna magana da Hajiyar su Khalil, akan cewa za a tsaida lokacin bikin”
“To shi da baya kasar ma?” Aziza ta faɗa tana ninke musu anko din, Sultana ta ce
“To nima dai naji Mom na cewa a bari sai Yaya ya dawo, kin san fa sun kusan dawowa gida gabaɗaya, shima Khalil din ya kusan dawowa, wai ko kuma a tsaida ranar sai ya kasance lokacin da zasu dawo kar bikin ya wuce saura wata biyu, na dai ji Mom na cewa wata takwas ko wata tara,kafin nan sun dawo dukkansu kuma sun huta” Aziza ta gya ɗa kai tana fadin
“Allah ya tabbatar mana da alkairi”
“Amin ya Allah, da bikina fa ke ce zaki yi min babbar ƙawa wlh” Aziza na shirin magana wayar Sultana ya dauki ruri tana dubawa ta ga Khalil ɗinta, da sauri ta miƙe tana fadin
“My love ya yi kira sai anjima” tana fadi ta fice da gudu, Aziza kuwa ware idanunta tayi tana jinginuwa da bango sabon hawaye na sake zubo mata, komai yana shirin kwab’e mata, kawai mafita shine zatayi addua Allah ya zaba mata abunda yafi mata alkairi,bata so sam Nawaz ya dawo ya sameta a gidan, dan haka taja akwati ta haɗa kayanta tun daga yau, anko din kuma dakin guga ta yi dasu idan aka goge sai ta miƙawa Sultana nata.