AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

neman hanyar guduwa su Shaho suka hau yi, Aziza ta naɗosu da jelarta, sannan ta koma rabin mutum rabi macijiya, kafin ka ankara masu sakin zawo a wando da masu fitsari duk sunayi, cikin tashin hankali da kiɗima da ɗimauta Shaho ya ce
“Dama ke ba Mutum ba ce?”
” RUWA BIYU” (taken Hajiya Azima kenan).
"Ku godewa Allah bana kisa,bana fata kuma ranar da zanyi kisa! Inaso ne na muku gargaɗi da kakkausar murya, babu ruwanku da Hamma Nawaz shi da familynsa, sannan duk ranar da dayanku ya ƙara aikata abu marar kyau zan maida shi kwaɗo, sannan idan har ku ka ba wa wani labarin abunda ku ka gani yau a take zaku mutu, kuna jina!!?"
“E wallahi Mamanmu mun ji ki,mu dai dan Allah kiyi hakuri!” suka haɗa baki wajan faɗi, watsar dasu Aziza ta yi, sannan ta zama mutum, su kuwa da mugun gudu suka watse nafsi-nafsi kowa ya yi ta kansa.
Da sauri ta yi kan Sultana yayinda hawaye ya hau wanke mata fuska, zata tab’ata kuma sai ta fasa, zata tashi sai koma ta kara komawa tasa hannu ta shafi inda aka buga mata katako a bayan wuya, sannan ta mike zata tafi taji Sultana ta riko hannunta, ganin haka yasa Aziza hura mata wani farin hayaki, nan take Sultana ta buɗe idonta, tana buɗe ido ta saukesu a kan Aziza, nan ta saki wani kuka tana fadin
“Dan Allah kice min film nake kalla,ko kuma duk abunda ya farun nan ki ce min mafarki ne ba gaskiya bane” tana maganar ne a ruɗe tana juyi ta rasa inda zata sa kanta dan firgici ganin haka yasa Aziza ɗora hannunta a goshin Sultana, lokaci daya ta samu natsuwa, hawaye ne ya zubowa Aziza ta ce
“The game is over Anty Sultana! da,fari naso nayi tafiyata ba tare da kun san wacece ni ba, amma ke Allah ya nufa zaki sani, ba zan iya yarda na watsar da yardan da kuka mini ba,ko ba komai yanzu idan na tafi zanyi farin ciki idan kika koma zaki gayawa Mom cewa ni ba mutum ba ce,bazan taba manta alkairinku a tare dani ba, hakika Anty Sultana ni ba mutum ba ce MACIJIYA CE!!”
Girgiza kai Sultana ta hau yi tana fadin
“Gaskiyan Yaya ne da Mom wata rana sai na fara ganin abunda nake kalla a gaske, to ko dai na samu tab’in hankali ne sabida dukan da aka min? Amma taya mutum zai ga maciji a zahirance irin haka?” hannu Aziza tasa ta kamo fuskar Sultana ta ce
“Kalli cikin idona!” ɗagowa Sultana ta yi ta sauke idonta a cikin na Aziza nan ta ganshi sak idon mage mai fari-fari
“Wannan shine dalilin da yasa bana buɗe fuska sabida idona! Ki yarda Anty Sultana ni ba mutum ba ce,duk labarin da na baku a kaina karya nake yi, wannan shine asalin gaskiyata, ni macijiya ce,na zo neman ‘yar uwata ce ta biyuna, shine dalilin da yasa na shigo cikin gari, idan kinason jin labarinmu ba zan boye miki komai ba, ki kasa kunne ki sha labari” Aziza ta fada tana gyara zama,ita dai Sultana banda rawa da jikinta ke yi sai b’arin baki babu abunda takeyi tana yiwa Aziza kallon tsoro, nan Aziza ta dauko mata labari tiryan-tiryan a natse take warwarewa Sultana zare da abawa, bata boye mata komai ba ta gaya mata komai tsaff! Wani gauron ajiyar zuciya Sultana ta sauke ta ce
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Ai ko a fina-finan da nake kalla ban taba ji ko na gani ba, to meyasa baki gaya mana gaskiya ba?” murmushi Aziza ta yi ta ce
“Babu wanda zai zauna da macijiya, da ace a lokacin na gaya muku zaku koreni,idan kuma baku koreni ba zaku dinga tsorona, na zauna shuru a gidanku ne dan na tara kudin da zan nemi yar uwata mu koma al’karyarmu, dan Allah ki ba wa Mom hakuri idan kin koma, sannan ki nema mini yafiyarta idan na mata abu a rashin sanina, haka ma dan Allah ki nema min yafiya a wajan Hamma Nawaz, sannan kema ki yafe mini” Aziza na gama faɗi ta fashe da kuka ta tashi da sauri zata fita,sultana tace
“A yau kin ceci rayuwata, da ace ba dan ke ba, abunda nake yiwa gidan mijina tanadi da yanzu an karbe shi, bani da sauran wani mutunci da kima, da na koma matatta ko da ina raya, a yadda naji labarinki ke abun tausayi ce ba abun gudu ba daga ke har Baffanki da Hajjanki da kuma yar uwarki! Ai ke ba abun a gujeki bane Aziza, dan ke din mai tausayi ce, idan har kin yarda dani kuma kin yarda munyi miki halacci ba ki so ki saka mana da butulci to ki biyoni gobe mu koma kaduna,nayi miki alkawari zan tayaki neman yar uwarki gari ya gari, idan har kin yarda dani fa amma” wani kuka ne ya sub’ucewa Aziza ta ce
“Anty Sulty?” rungumeta Sultana ta yi ba tare da tsoro ko fargaba ba,
“Dama akwai mutane irinku a duniya? Tabbas duk lalacewar mutanen duniya na Annabi basu ƙarewa” cewar Aziza tana kuka, Sultana tana bubbuga bayanta ta ce
“Ni dai ki min alƙawari ba zaki gudu ba,kuma karki kara tunanin guduwa,Mom mutum ce mai zargin kanta a koda wani lokaci zata dinga zargin kanta da bata miki riƙon tsakani da Allah bane shiyasa kika gudu, dan Allah karki saka mata da haka”
“In sha Allah Anty Sulty babu inda zani” daga haka Sultana taja hannun Aziza suka fice a gidan ga dare ya tsaga ana neman gaff kiran sallan assalatu, fitowa bakin titi sukayi, Sultana ta ce
“Muna waya da Khalil yan iska sun bugeni wayar ta faɗi, na san za a nemu kam kuma hankalinsu zai tashi” Aziza ta ce
“Nima takalmina kafa daya ya fadi, yanzu ya za ayi kenan?”
“Kawai ki daukemu mu b’ace muje gida” zare ido Aziza ta yi ta ce
“A’a Anty Sulty,mu nemi wani hanyar dai” suna nan tsaye har aka kira assalatu, Aziza tace mu zauna a nan mu jira har ayi sallar asuba nasan a lokacin motoci zasu fara wucewa sai mu wani wanda zai kai mu gida, tunda bamu sallah ba da sauki ai”
“Yan iska mutanen banza! Da yanzu sai su mana fyaɗe muna period ko?”
“To suna tsoron Allah ne, ai basu tsoron Allah” zama Sultana ta yi a kasa tana fadin
“Ai shikenan” itama Azizan zama ta yi, nan kuwa aka yi asuba kafin motoci suka fara gilmawa da kaɗan-kaɗan har suka tare mai taxi, Sultana ta gaya masa unguwar da zai kaisu ya daukesu.
A gate din gidan mai taxi ya ajiyesu, suna fita suka samu harda yan sanda, mutane ana tsaye cirko-cirko daga ciki kuwa harda amarya da ango, wanda jiya da aka tashi a wajan dinner amadadin ayi gida ai sai hankali ya tashi, kuma ga wayar Sultana da suka samu a gate din da kafar takalmin Aziza guda daya, shiyasa suna gani suka sa a ransu ai kawai an sace su Sultana ne, sai kuma ya haɗe da Khalil da yake ta faman zabgawa wayar Sultana kira dan yaji lokacin da Aziza ta kwala mata kira sadda aka buga mata katako a kai wayar ta fadi kasa,kuma yaji sadda suke cewa a dauko da Aziza, itama aka dinga buga mata katako, sannan sun ga jini a wajan, jinin kan Aziza wanda ya fashe.
Hajiya Habiba mahaifiyar amarya Sulaiha ganinsu yasa ta ta tarosu da kuka tana tambayar lafiyarsu, nan suka tabbatar mata da suna lafiya, aka tambayesu me ya faru,nan Sultana tace daukesu aka yi, yan sanda suka tambayesu waye suka ce basu gane mutanen ba, dan sun rufe fuskarsu,
“Taya aka yi kukayi escaping daga hannunsu?” Sultana ta ce
“Ashe bamu zamu dauka ba, su da kansu suka sakemu, a bakin titi muka kwana kasancewar dare ya tsaga, sai da akayi asuba muka samu mota ya kawo gida”
“Ina dai basu muku komai ba ko” cewar Hajiya Habiba
“E Ammi basu mana komai ba”
“Na godewa Allah, da me zan cewa Hajiya yara daga zuwa biki ni Habiba,tana can hankalinta tashe wallahi, dan ma dai tana da karfin zuciya” nan aka shiga jajinta lamarin, aka ce su shiga su huta Sultana tace sam ai yanzu kam gida zasuyi, anyi-anyi su bari sai anjima tace sam,ganin haka yasa Hajiya Habiba cewa to jami’an tsaro su rakasu har kaduna har cikin gida, kayansu kawai aka fiddo musu aka sa a both, Sultana ta rungumi Sulaiha ta ce
“Ƙawata kuyi hakuri fa jiya hankalinku ya tashi ga shi ko gidanki ba a kai ki ba”
“Haba Sultana ba dole ba”
“To shikenan ai muna lafiya, kiyi hakuri ba zan samu zuwa gidan ba amma na miki alkawari zan zo idan an kwana biyu, a sha amarci lafiya” daga haka sukayi sallama wata ƙawar Sulaiha ta mikawa Sultana wayarta da kafa ɗayan takalmin Aziza,bayan mota suka shiga jami’an tsaro suka rakasu a baya, har kaduna.
@@@@@@
Suna isa da gudu Sultana ta shige gida,Mom tana tsaye a parlour ta kasa zama, Sultana na shigowa ta ce "MOM!?" da sauri Mom ta juyo tace
“Sultana” rungumeta tayi, cikin hawaye Mom ke tambayar lafiyar Sultana, shigowa Aziza da yan sanda sukayi, Mom na ganin Aziza ta yi saurin zuwa ta rungumeta tana tambayar lafiyarta,jikin Aziza ne ya kara sanyi, da yanzu ta gudu wani tashin hankali zasu shiga? Da yanzu wannan abun bai faru ba da shikenan ta b’ata rawarta da tsalle, hakika zamanta dasu akwai wani babban sirri da Ubangiji ya boye, shin yanzu su gayawa Mom gaskiya ne ko yaya zasuyi?” Mom ce ta shafo fuskarta tace
“Kina lafiya ‘yata?”
Aziza ta gya ɗa kai,nan yan sanda suka kara yiwa Mom bayani kafin Mom ta musu godiya suka fice,suna fita Hajiya Habiba na kira,nan Mom ta shaida mata ta kwantar da hankalinta sun zo gida lafiya, dama tsautsayi ai baya wuce lokacinsa Allah ya kiyaye na gaba kawai, daga haka suka yi sallama aka rabu lafiya, Mom ta kallesu tace
“Bakuyi wanka ba ko?” suka gya ɗa kai
“Kuje kuyi wanka ku kwanta ku huta idan kuka tashi sai ku ci abinci, tunda yanzu ana neman shaɗayan safe ne” suka amsa da to, Aziza a sanyaye ta shige dakinta, Sultana kuma ta haura sama, sai da ta yi waya da Khalil dinta ta tabbatar masa tana lafiya dan hankalinsa ya tashi bai rintsa ba jiya, ta ba shi labarin ai Aziza ce ta taimakesu, amma bata gaya masa komai a kai ba, dan tayi alkawari ko wa Mom ne ba zata gaya ba har sai Aziza ta yarda, wanka ta yi sannan ta bi lafiyar gado dan bacci takeji sosai, haka ma Aziza ita ma wankan ta yi ta kwanta zuciyarta a cin kushe, ga tunani fal a cikin ranta,ji take kamar kanta zai fashe, ta ɗau minti talatin tana juyi kafin bacci ya kwasheta.