AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Basu farka ba kuwa sai hudu na yamma,Mom ma bata tashesu ba, ta dai musu odern abinci, bayan sun farka ruwa suka sake watsawa kafin suka ji sun watstsake, kasancewar suna fashin sallah dukkansu shiyasa basu wani damu ba, Sultana ce ta fara fitowa ta shiga dakin Mom ta sameta suna waya da Nawaz,sai da suka gama Mom tace
“Kin tashi? Kinyi sallah?”
“A’a Mom ina fashin sallah, Aziza ma haka”
“Yaushe kuka fara?”
“Ranar da muka isa zaria”
“Ok ya yi kyau,banda shan zaƙi dai da abu mai sanyi”
“To Mom”
“Kije ki ga idan Azizan ta farka,ku ci abinci”
“To Mom, amm Mom Khalil yace zai dawo a satin nan”
“Lafiya dai ko?”
“Nima ban sani ba, amma yace ya fasa cike sauran watannin” gya ɗa kai Mom tayi ta ce
“Nima maganar da muke yi kenan da Nawaz yace zasu dawo, jin abunda ya faru yace gwara kawai ayi auren kwanan nan a kaiki hankalinsa da nawa ya kwanta nima kuma nayi na’am da abunda yace, dan haka yace zasu dawo dukkansu shi da Son,idan suka dawo sun dawo kenan, nan da wata daya” shuru Sultana tayi dan bata so haka ba, ba tare da tayi magana ba ta fice, kasa ta sauko bata ga Aziza a parlour ba dan haka ta zuba musu abincin tayi dakin da sallama Aziza na zaune a bakin gado, tana sallaman Aziza ta amsa tana shirin rufe fuska, Sultana tace
“Babu amfani ai tunda nasan komai, zo muci abinci” ta fada tana zama kan carpet, zamowa daga gadon Aziza tayi ta kalli Sultana ta ga jikinta a sanyaye Aziza ta ce
“Anty Sultana yana ganki haka akwai matsala ne?”
“Babba ma kuwa Aziza, Khalil jin abunda ya faru yace zai dawo a cikin satin nan, Yaya kuma yace shima zai dawo nan da wata daya dan ayi aurena hankalinsu ya kwanta shi da Mom,kuma Mom tace shi da amininsa zasu dawo, dama yanzu dawowa mai gabadaya zasuyi” Aziza ta ce
“A’a bangane ba,ina da tambaya, shin Hamma Khalil ba shi bane abokin Hamma Nawaz ba wanda suke kasa daya?” dariya Sultana tayi ta ce
“Taya? Khalil fa shi yana paris ne, su Yaya Nawaz kuma suna america ne, sunan babban aminin Yaya ba Khalil bane, ke yanzu duk zamana dake baki san my husband to be ba? sunan babban aminin Yaya Nawaz AL’MAZEEN NE shi kuma ɗan Kano ne ba dan kaduna bane,gidansu ne Mom tace zata aikemu nace bazan je ba.
????????????????
MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
(???? Macizai ne????)
MALLAKAR.
ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)
Follow me on wattpad,@Fateemah’0
????????????????????
PAID.
????️=5️⃣3️⃣↪️5️⃣4️⃣
Cikin girmamawa Hadiza ta amsa da to, sannan ta yi waje can wajan kofar baya na kitchen, ta samu Azima zaune tana tsinke fulani tana wurgarwa, Hadiza ta ce
“Azima meke damunki?” ɗagowa tayi ta girgiza kai alaman ba komai
“To ki zo mu haura sama na nuna miki part din Oga Al’Mazeen zai dawo nan da sati biyu, Hajiya Lawiza tace
Ki fara karkaɗe kura” zunbur Azima ta miƙe tana fadin “muje”
saman suka haura step na hawan uku can ne part din Al'mazeen, kasancewar baya son hayaniyar gidan, shiyasa idan yana gari ya dawo office yake hawa ya zauna a can shuru abunsa, harta ƙaramin kitchen akwai a saman, shiyasa baya damuwa da a kawo masa abinci, dan baya so ma yana cin abincin gidan dan bai yarda dasu ba, suna iya zuba masa abinda ba haka ba a cikin abinci.
Tunda suka fara taka step din bugun kirjin Azima ya tsananta, Hadiza ke gaba Azima na binta a baya, har suka je bakin kofar parlourn Hadiza tasa key ta buɗe suka shiga, duk da mai dakin ya shekara baya nan amma har yanzu da kamshin turarensa na tashi, sai kuma uban kura kasancewar idan baya nan babu mai cewa a dinga bude dakin ana karkaɗewa, Hadiza ce ta kalli Azima ta ce
“Azima bari na tayaki dan kuran yayi yawa”
“A’a ki bar shi kawai Hadiza, ai aikina ne je ki kawai”
“Yanzu zaki iya wannan aikin ke daya?” shuru Azima ta yi bata ba wa Hadiza amsa ba,ganin haka yasa Hadiza ajiyewa Azima su tsintsiya da mopa dasu omo da dai kayan aiki, har Hadiza zata fita Azima tace
“Dama kin tafi da wa innan kayayyakin naki dan ba amfani zanyi dasu ba” da mamaki Hadiza ta juyo ta ce
“To idan ba kiyi shara da tsintsiya ba dame zakiyi?”
“Ban taba shara da tsintsiya ba” Azima ta faɗa tana zuwa wajan jikin hoton da ta hango, hannu tasa ta goge hoton, nan take fuskar AL’MAZEEN ya bayyana, rasssrasssrasss!! ƙirjinta ya buga ta ja da baya tana girgiza kai, Hadiza ta ce
“Karki tsorata, shine Al’mazeen ɗin, karki ga fuskarsa a haɗe mutum ne mai saukin kai, nan gidansa ne, amma idan kika ga yadda yake rayuwa a cikinta sai kin tausaya masa” Hadiza ta fada tana matsowa kusa da hoton tasa tsummar dake hannunta ta goge wani wanda suke su biyu ta ce
“Kinga wannan? Sunansa NAWAZ babban aminine ga AL’MAZEEN,idan har kika ga Al’Mazeen na fara’a to yana tare da Nawaz, shi Nawaz a kaduna yake,kuma dukkansu likitoci ne, sabida tsananin shaƙuwa da son da suke yiwa juna,bayan sun bude asibitinsu suka saka masa suna mai harufan sunayensu ALWAZ HOSPITAL na Nawaz na shi na kaduna, shi kuma Al’Mazeen na shi na nan kano, yana da kyauta,baya da kyashi, yana da taimakon duk wani na kasa da shi,duk yadda zan baki labarin Al’Mazeen yafi haka, amma idaa ya dawo zaki tabbatarwa kanki” Hadiza na gama fadi ta juya ta fice.
Girgiza kai Azima ta hau yi, Banju dake jikin Azima yaji a jikinsa tabbas idan bai bar gidan nan ba, AL’MAZEEN shine makarinsa na farko a karo na biyu, to amma taya zai bar gidan? dan ya sha yunkurin haka amma zaiji kafafunsa tamkar an dauresa ne.
Baya-Baya Azima ta yi ta koma jikin kofa ta bude blue eye dinta ta zaro dogon harshenta tana busar da wani tururi shi ba fari ba, shi ba baƙi ba, shi ba blue ba, tana hura wanna iskan hayakin nan take parlour da dakin da toilet din da kitchen din suka zama sabbi dal, harshenta ta maida sannan ta saka key a kofar ta shige bedroom ta zama macijiya ta hau gado ta kwanta dan bacci take ji, a macijiyar tayi kwanciyarta ta hau bacci.
????????????????
“To yanzu Aziza a ganinki taya zamu je kano? Khalil ya hana, Mom kuma ta biye masa,kuma kinga yanzu ne nake da freedom bayan aure kuma sai abunda Allah ya yi, ga shi yanzu bikin saura wata daya da sati biyu, bai ma cika da sati biyun ba, wlh na rasa yanda zanyi” ajiyar zuciya Aziza ta sauke ta ce
“Anty Sulty, abubuwa suna shirin cakuɗe mana,ni a ganina ya kamata mu maida hankali a guda daya”
“To wanne kenan Aziza?”
“Bikinki! Kinga kamata yayi ace mu maida hankali a kan shirye-shirye,idan yaso bayan anyi auren a lokaci hankalu zai kwanta,idan ya so sai mu dubi gaba”
“Tabb lallai Aziza na tabbatar har yanzu da ƙuruciya na yawo a kanki, taya Khalil zai bar ni da aurena muje yawon gari ya gari neman Azima? A yanzu ma da ba ayi auren ba ya na ƙare? Gaskiya wannan shawara taki bata yi ba, ni wlh wannan biki da an bar sa idan na cika shekara ashirin sai ayi! tinda yanzu ina sha tara” ta faɗa da fuskar haushi, waro ido Aziza ta yi ta ce
“Cab Anty Sulty shekara ashirin fa kika ce? to wlh da a rugarmu na yankin kwana ne ace kamarki bata yi aure ba wollah ko zanar kofar gidanku bakki iya fita sabida gori da habaici da bakar magana, kin ganmu nida Azima, shekararmu sha biyar amma yadda kika san kamar mun shekara dari ne bamuyi aure ba, dan a al’adan rugar yankin kwana yarinya tana da shekara goma za a fara yi mata wankan kindirmo, tana shiga sha daya za a aurar da ita”
” a shekara sha dayan!?” Sultana ta faɗa tana zaro ido
Aziza ta ce
“Wlh da gaske Anty Sulty”
“Tabdijam, lallai kam, ai mu kam nan ke baki isa aure ba, amma da shike zamani ya canza ana iya miki, amma karatu ne yafi dacewa dake, ina son zuwa kauyenku”