AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Tab to mu dai a can kinga bamu san wani abu karatun boko ba amma akwai manyan malaman Muhammadiyya,kasancewar muna can cikin jeji ne amma bamu da wannan duhun kan na jeji muna da ilmin addini sosai, amma In sha Allah idan na koma zan wayarwa da mutane mahaifata kai ta hanyar karantar dasu ilmi daga cikin wanda na samu daidai gwargwado, tabbas na yarda ilmi ginshiƙi ne na rayuwa,ilminka baya cika kuma sai ka haɗa duka biyu a kanka, farko sai ka ajiye ilmin da zai ceceka ranar lahira, sannan ka kara da na bokon wanda shima ta sanadinsa zaka iya shiga aljanna, Allah ya bamu ilmi mai albarka, rugarmu kuma In sha Allah idan Hamma Khalil ya bar ki zakije, amma fa karkije ki ƙi dawowa”????
“Amin ya Allah Aziza, hahaha taya zan ƙi dawowa?”
“Idan kikaji dadin rugarmu mana”
“Humm ke dai, ai kya bari naje na ganewa idanuna ko?” Aziza ta yi murmushi ta ce
“Ai shiyasa ban baki labarin ni’imar dake yankin sassaninmu ba” Sultana ta yi dariya ta ce
“To naji, kar dai ki shashantar da
maganata”
“To abunyi shine kawai ki ƙara tuntubarsa” Sultana ta jinjina kai tana fadin
“Ok zanyi hakan In sha Allah,ina zuwa” ta faɗa tana ficewa a dakin.
@@@@@@@
Kamar yadda Aziza ta cewa Sultana ta kara tuntubar Khalil da maganar ya bar su suje kano hakan kuwa akayi, ganin ta takura yasa yace ta bari to idan su Nawaz suka dawo aka karasa saita komai sai taje tayi kwana biyu idan ana biki saura sati daya, tasan halinsa baya canza magana dan haka ta amsa da to, amma a zuciyarta ta yi lissafin garin da zasuje ya kai shidda, tace ai ba ayi auren ba, balle idan ta tafi tana tafiya akan wutar jahannama (Allah ya kiyashemu amin).
????????????????
Tunda aka shiga saura sati su Nawaz su dawo, Mom dasu Sultana da Aziza wacce faduwar gabanta ya tsananta a kwana biyun nan wanda ta rasa dalili hakan, suke shirye-shiryen dawowarsu Nawaz da Al’mazeen, da aka shiga satin karshe murna a wajan Mom da sultana abun sai wanda ya gani, Aziza ta kasa gane ita wani hali take ciki, shin murna take yi ne ko akasin haka, ta bangaren Azima ma kullum tana sama part din Al’mazeen zata shiga ta gyara ta zama macijiya ta kwanta tayi baccinta.
@@@@@
MA SHA ALLAH.
A jiya ne su Nawaz shi da Amininsa Al’mazeen suka samu damar sauka a kasarsu nigeria, sun sauka ne a airport din abuja, Al’mazeen ya kalli amininsa ya ce
“Dude mu wuce kd kawai”
“No wlh sai na huta, mu wuce hotel kawai mu watsa ruwa mu huta idan yaso gobe da safe tunda driver ya zo 10 ma muna kd in sha Allah, ka ga kaima idan ka so zaka huta kafin ka wuce kano,ko ya kace?”
“As u wish” Al’mazeen ya faɗa yana shiga mota.
A waya Nawaz yake gayawa Mom cewa sun sauka lafiya sai gobe da safe zasu shigo Kd, sannu da gajiyar hanya mom ta musu,sannan ta ce Allah ya kaimu goben lafiya,bayan ta katse take gayawa Sultana sun iso amma Nawaz yace sai gobe zasu shigo, itama dai Allah ya kaimun ta yi, ko da Sultana ta gayawa Aziza sai gobe su Ya Nawaz zasu shigo kd amma sun dawo nigeria suna abuja,itama Allah ya kaimun tace jikinta duk a sanyaye, ta bangaren hajjaju Azima,itama da taji kishin-kishin watakila sai gobe ko jibi Al'mazeen zai shigo kano amma ya dawo nigeria ko kaɗan bata ji dadin hakan ba, amma tace tayi hakurin jiransa na watanni masu tsayi dan dai kwana biyu babu damuwa.
Washe gari tunda sukayi sallar asuba basu koma bacci ba, suka share cikin gidan tass suka goge, Aziza ta ce
“Anty Sulty kije ki k’ara gyara part din Hamma Nawaz, ni zan tsaya a kitchen” Sultana ta amsa da to sannan ta fice ta bar Aziza ta hau aikin haɗa su abinci,ko da Mom ta shigo kitchen Aziza ta ce
“Haba Mom kina damu a raye me zaki zo yi a kitchen, dan Allah kije ki kwanta ki huta” murmushi Mom ta yi ta kalli Aziza ta ce
“Hakika mahaifiyarki tayi farin haihuwa da ta haifeki, na yaba da hankali da natsuwarki, Allah ya miki albarka ƴata” Aziza ta dukar ta kai tana juya white eye dinta ta ce
“Amin Mom ɗinmu” fita Mom tayi tana wasu tunani a ranta, hakika da ace Aziza mutum ce babu abunda zai hana bata yiwa Nawaz kwadayin aurenta ba, duk da Nawaz Allah ya yisa da rainakon mace, yanzu zai iya cewa Aziza tayi masa yarinya,ita kuwa zata so Allah ya bata sirka kamar Aziza wacce zata maye mata gurbin Sultana idan tayi aure, ga shi dai Aziza ta shiga ranta sosai, duk da ita bata taba ganinta a macijiya ba, bata ma fatan ganinta a macijiyan, amma taya zata fahimtar da Nawaz har ya aureta? Dan Nawaz murɗaɗɗan mutum ne, zama tayi a bakin gado tana sauke ajiyar zuciya mai karfi,ta jima tana tunane-tunane sannan ta hau adduar neman zabin Allah wa ɗanta da kuma Aziza wacce bata so ta rabu da ita.
Karfe tara da rabi suka kammala komai suka jera a dinning, sannan suka sakawa gidan turaren wuta ya dauki kamshi, Sultana tace
“Aziza je ki dau wanka nima bari na tafi”
“To Antyna a huta gajiya” Sultana ta hau sama, aziza kuma ta shiga dakinta, toilet ta wuce dan tana da bukatar wankan nan sai kamshin abinci take yi,bayan ta fito ta dan murza mai kaɗan a fatarta wanda yake sheƙi, wani doguwar abaya ta saka, ta shafawa kanta mai,ta daure gashin, bata sa hula ba,illa lullubi da ta yi ta rufe fuskarta wanda ta jima bata rufe ba Mom ta hanata rufewa tace tayi rayuwarta ta daina takurawa kanta tunda sun san gaskiya, amma da shike yau Nawaz zai dawo harda bako yasa tayi lullubin.
Tana nan zaune a dakinta har wajan goma da minti asharin, ihun Sultana ta jiyo tana fadin
“Oyoyooo my 2 Brother’s!!” wani wawan faduwar gaba ne ya dira a zuciyar Aziza jikinta ya dauki rawa, tana ji ana oyoyo tare da fadin ya hanya, muryan Sultana ta jiyo tana kwala mata kira, a hankali ta miƙe ta gyara mayafinta ta fito jikinta na rawa, a lokacin Nawaz da Al’mazeen suna rungume da Mom, Sultana na tsaye a gefensu tana dariya bakinta yaki rufuwa dan murna, bayan sun saki mom take kara musu ya hanya suna amsa da lafiya alhamdulillah, nan Mom ta rufesu da addua na nasarar da suka samo,zama sukayi a kujeran cikin parlourn, Sultana ma ta zauna kusa da Yayanta, tana kara gaishesa ya amsa yana tsokanarta amarya-amarya, rufe fuska tayi da tafin hannunta jin Al’mazeen shima ya hau tsokanarta, ganin yadda suke murna da nishaɗi yasa hawaye zubowa a idon Aziza tana kallonsu tana murmushi dan sun burgeta, a hankali ta juya zata koma daki idon Sultana ya sauka a kanta, ta ce
“Aziza kina jina tun dazu nake kiranki Yaya sun dawo amma kika min shuru?” tun sadda Sultana ta kira sunan Aziza hankalin Nawaz ya koma kanta yana kare mata kallo kirjinsa na bugawa, tunda ya bar nigeria mafarkin yarinyar nan ya hanasa kiba, Al’mazeen ya kalleta shima yaji gabansa ya fadi, Mom tace
“Karaso mana ɗiyata” a hankali Aziza ta fara taka kafarta wanda take jinsa tamkar baya jikinta dan kafafun sun mata nauyi, ta karaso ta duka tana gaishesu kanta a duƙe fuskarta kuma a lullube, amsawa Al’mazeen ya yi sabanin Nawaz da yake ji kamar zuciyarsa zata tsaga kirjinsa ta fito waje, bayan ta gaishesu ta mike ta kawo musu abun sha, suka ce ba zasu ci abincin yanzu ba, zasuje su kwanta su ɗan yi bacci zuwa azahar, sai sun farka kafin su ci abinci, a tashi lafiya Mom ta musu suka miƙe a tare, har sun kai kofa Mom ta ce
“Al’mazeen amma ba yau zaka tafi kano ba ko?”
“E Mom sai Allah ya kaimu gobe”
“To Allah ya kaimu lafiya”
“Amin” ya amsa a sanyaye yana bin bayan Nawaz wanda shi bai tsaya ba.
Kwanciya sukayi ba jimawa kuwa bacci ya suresu, karfe daya da rabi suka farka suka yi sallah, Nawaz ne ya fara tashi yana fadin
“Yunwa nakeji yanzu kam, ka zo muje muci abinci”
“Okay muje” Al’mazeen ya faɗi shima yana tashi, wayar Al’mazeen ne ya dauki ruri Nawaz na ganin mai kiran ya yi tsaki yana fita.
A hankali take tafiya Mom ta bata sako ta kai wa driver zai kai wa Hajiya Hauwa, kanta a sunkuye ga shi ta yi lullubi ga tunani,tana tafiya tana tunani, shi kuwa Nawaz hankalinsa na cikin waya yana dannawa, dai-dai wajan kofar shigowa babban parlour sukayi karo nan kafarta daya ya zame yana shirin wucewa ƙananan step guda uku na shigan parlourn ɗin, ganin haka yasa cikin saurin Nawaz yasa hannu ya fizgota, mayafinta ya faɗi kasa, gashinta da bata yi masa daurin kirki ba ya koma baya yana lilo, tsoro yasa ta waro idonta gabadaya waje, caraf sukayi 4 eye da Nawaz, wani mahaukacin bugawa kirjin Nawaz ya yi ganin white eye ɗin Aziza, saurin saketa ya yi ta faɗi ta bugu da duwawu, taji zafi dan haka tace
“Washhh Allah na!” Al’mazeen dake waya ya ga Nawaz ya saki yarinyar mutane a kasa ta bugu dan ya ga sadda sukayi karon zata faɗi ya riƙeta amadadin ya tsaidata da kafarta sai kuma ya saketa?.
"What's wrong with u dude?" Al'mazeen ya faɗa yana shirin sa hannu ya dago Aziza,kafin Al'mazeen ya ɗagata,tuni Nawaz yasa hannu ya sake fizgota ya tsaidata da kafafunta, ya duka ya dauki mayafita ya sa mata a kai, murya a daqile yace mata bar nan, da sauri kuwa Aziza ta bar wajan, Al'mazeen ya kallesa ya girgiza kai ya wuce ya bar sa tsaye, jikin Nawaz ne ya dau rawa yana kara tariyo yadda ya ga idon Aziza, me hakan ke nufi? Ya tsaya yana tambayar kansa.
????????????????
MOMYN AHLAN✍????[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
(???? Macizai ne????)
MALLAKAR.
ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.