AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)
Follow me on wattpad,@Fateemah’0
????????????????????
TNK U 4 CMMNTS MY PPL’S.
PAID.
????️=5️⃣1️⃣↪️5️⃣2️⃣
“To meyasa kika ce ba zaki je ba? Ni wlh na zata Hamma Khalil shine Abokin Hamma Nawaz” cewar Aziza,Sultana ta ce
“A’a kinga hoton Khalil” Sultana ta faɗa tana nunawa Aziza hoton Khalil a wayarta, Aziza ta yi murmushi ta ce
“Ma sha Allah,kun dace sosai, Allah ya kaimu musha shagali”
“Amin-Amin”
“To ke yanzu Anty Sulty miye abun damuwa dan za a saka bikinki?”
“Ke Aziza baki da hankali ko? Ke kin san takura irin na Khalil kuwa? Wlh idan ya dawo ba zai bari na dinga motsawa ko nan da can ba,kuma duk abunda ya faɗi Mom zata hau kai ta zauna, taya zamu fara tafiye-tafiye wajan neman Azima? Sannan ma duk ba wannan ba, wannan babban lamari bai kamata ace zamu iya mu biyu ba, Mom tana da fahimta ni a ganina tun a ba kowa mu gaya mata gaskiya, dan kar a zo wata rana ta sani kuma abun ya kwab’e mana” jikin Aziza ne ya dauki rawa ta kalli Sultana ta ce
“Anty Sulty Mom zata koreni!” ture abincin gabansu gefe Sultana ta yi ta kamo hannun Aziza ta ce
“Taya Mom zata koreki Aziza? Babu amfanin boye mata abunda zata sani duk daren daɗewa kamar yadda nima na sani a yanzu, dan haka gwara mu gaya mata a san abun yi tun a yanzu, ga shi ana maganar tsaida bikina kwanan nan, tsammaninki yanzu Khalil zai dawo a cikin sati, su Yaya Nawaz zasu dawo nan da wata daya,ina mai tabbatar miki za a iya aurar dani nan da wata biyu, dan haka gwara muyi da gaske, yanzu ki tashi muje mu samu Mom mu gaya mata gaskiya, dan hausawa na cewa da zafi-zafi ake dukan karfe”
“Wani gaskiya zaku gaya min?” suka ji magana daga bayansu, ba iyakar Aziza ba, har ta Sultana sai da ta kwalalo ido waje, Mom ta ce
“tambayarku nake yi, sai zazzare idanu kukeyi ku min magana mana, dan wannan idon naku baku da gaskiya” Sultana ta kalli Aziza wacce take girgiza mata kai alaman kar ta faɗa, Sultana ta hau in-ina tama kasa magana,idan ta kalli Mom, Mom zata ce ta gaya mata me suke boyewa,idan ta kalli Aziza zata girgiza mata kai kar ta faɗi, dan haka Sultana ta kasa magana banda in-inar da takeyi dan an sakata a tsakiya, ganin ta ruɗe har zufa take yi, ga Aziza da ka kalleta kaga tashin hankali a fuskarta ganin haka yasa Mom kamo hannun Sultana ta ce
“A iya sanina ban yi miki tarbiyyar k’arya ba,ba halinki bane, sannan baki boye min abu, duk da ban san Aziza sosai ba amma zan iya tsayawa na bugi kirji na faɗi halin Aziza, dan haka karku fara min karya daga yau, karku boyemin komai, tun dawowarku nake ganin damuwa a fuskarku, ku gaya min meke faruwa” kuka Aziza ta fashe da shi tana duƙawa ta rufe fuskarta da tafin hannunta, Sultana tace
“Aziza ki kwantar da hankalinki, Mom zan gaya miki” Sultana ta zaunar da Mom tace
“Ban san taya zaki fara daukar maganar ba, watakila da ace ni daya ce zakice nayi gamo da aljanu” Sultana bata fara cewa Mom Aziza macijiya bace,tun daga tushen labarin ta dauko mata tana bata tiryan-tiryan har ta kawo mata shi karshe ta dasa aya, wani ware ido Mom tayi tana bin Aziza da kallo wacce ta haɗa kai da guiwa tana kuka, hakika hankalin Mom ya tashi, Sultana kuwa ta gaya mata ta ga Aziza a macijiya kuma ita ce ma ta taimaketa daga hannun su dan gidan Alhaji wanda da badin Aziza ba da sunyi mata fyaɗe, jikin Mom banda kyarma babu abunda yakeyi, ta jima tana karanto kalman
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!” kafin ta fara jin tana samun natsuwa, sai da ta ware tukunna ta yi kan Aziza ta duka duk da zuciyarta na dukan tara-tara ta kama Aziza ta rungumeta tana rarrashinta, cikin kuka Aziza tace
“Mom dan Allah karki tsaneni! Dan Allah karki koreni! Dan Allah karki ji tsorona!” girgiza mata kai Mom ta yi ta ce
“Ko daya ba zanji ba, kamar yadda kike a da haka kike a yanzu, ai ba laifinku bane, a gaskiya Banju ba karamin mugu azzalumi bane marar imani, Allah sai ya saka muku, Allah ya bayyana mana Azima lafiya, Allah kuma ya kare bayinsa wanda Banju yake shirin tarwatsawa” suka amsa da amin,bayan sun gama yan koke-kokensu da jajinta lamarin Mom ta miƙe ta fice zuciyarta cike da zullumi, abu sai kace a film, bata fata ta ga Aziza a macijiya a labarin ma ya isa, Mom na fita Sultana da Aziza suka sauke ajiyar zuciya, Sultana ta ce
“Alhamdulillahi! Mom ta rage mana aiki”
“Kamar ya?”
“Da taji mana, da yanzu muna nan muna wallahi tallahi dake” murmushi Aziza ta yi tace
“Duk da haka ku zuciyarku daban yake, mutane irinku kaɗan ne”
“Humm! Yanzu ke kuma kenan dole kafin ki koma mutum sai kunyi aure?”
“Ai babban damuwar yana jikin Azima, idan har ta warke nima na warke In sha Allah, amma da kamar wuya a samu wanda zai auremu har ya taimaka mana mu dawo mutane kamar kowa”
“In sha Allahu, Allah zai kawosa,kuma zaki gani,muddun kunyi tawakkali Allah zai dubi hakurin da kukayi na cinye wannan babban jarabawan, sannan ya saka muku ta yadda baku tunani”
“Haka ne kam” Aziza ta faɗa tana gyara zama, sun jima suna hira.
????????????????????????
Bayan kwana biyu komai ya dawo dai-dai, kamar yadda Khalil ya faɗa zai dawo cikin sati to hakan ne ta kasance,dan kuwa shirye-shiryen dawowarsa akeyi,dan da ya dawo biki kawai za a sha, yace ayi biki a ba shi matarsa.
Ranar lahadi da da daddare ya iso gari, bayan da ya huta maganar biki Hajiyarsa ta hau masa, yace tunda yau ya dawo a bari nan da kwana hudu ko biyar sai aje dan a saka rana, duk da shima Nawaz ɗin yace zasu dawo su ma kwanan nan, da haka suka ajiye maganar.
Washe gari da misali karfe goma na safe yasha wankansa yasa manyan kaya na mutunci ya shiga ya gaida hajiyarsa, ta ce
“Khalil ina zuwa ne haka? Ko dai za a je ganin ɗiyata Sultana ne?”
“E wlh Mom, zanje dai gaishe da Mom ne”
“Ah ba wani nan kar ma ka wani fara fakewa da Mom Ah to ,a gaishe min da su Sultanan” tashi ya yi yana dariya yace zasuji sannan ya fice.
@@@@@
Bai gayawa Sultana a kan cewa zai zo da safe ba, ya dai gaya mata ya shigo kaduna da daddare da misalin takwas da rabi, ko da ya isa gidan kasancewar mai gadi ya san shi ya hau masa sannu da dawowa, Khalil ya amsa yana dariya, da shike gidan ba baƙonsa bane, nan ya shige kansa tsaye yana buga sallama, Aziza ce kawai ta farka a lokacin ta gana mopping kenan, ta ga mutum,tana ganinsa ta ganesa ta ce
“Lahh Hamma Khalil marabalale” ta fada tana hawa sama da gudu ya yi murmushi ya ce.
“Kanwarmu kenan” ya nemi waje ya zauna, da gudu Aziza ta shiga dakin Sultana ta haye gadon ta janyeta, Sultana ta bude ido cikin haushi ta ce
“Dan Allah miye haka Aziza!?”
“Kai Anty Sultana kin san da cewa Hamma Khalil zai zo shine kike bacci har yanzu baki masa girki ba, ba kiyi wanka ba haba dan Allah” ai Sultana tana jin an ambaci sunan Khalil yazo ta miƙe zunbur, ta ce
“Ke Aziza da gaske Khalil yazo?”
“Wlh yazo yana parlourn kasa” da sauri Sultana ta miƙe da kayan bacci ta ɗiro a gadon ta fita ta shiga dakin Mom ta ce
“Mom wai Khalil yazo”
“E na sani”
“Shine Mom ni ban sani ba, bai fa gaya min zaizo ba, ga shi ban shirya masa komai ba, ban yi wanka ba” Mom ta dauki mayafinta tana fadin
“Too idan kin gama mitan saiki haɗa masa komai ɗin sannan kiyi wanka” ta fice, fita itama Sultana ta yi, ta samu Aziza na kwashe kaya a parlourn sama,ta ce
“Aziza yanzu ya zanyi?”
“Karki damu Antyna,yanzu kedai kawai kije ki cakare wanka, zan kula da saura”
“Thats my lil’sis” Sultana ta fada tana shiga daki da sauri, kasa Aziza ta sauko ta shiga kitchen, a cikin mintuna qalilan ta jera tray ta haɗa abubuwa a kai na burgewa da ban sha’awa tazo ta ajiye a gaban Khalil wanda yake duƙe a gaban Mom suna magana, sun jima suna magana da Mom kafin Mom ta tashi ta koma sama, ba jimawa gimbiyar tasa ta sauko, nan aka hau hiran soyayya na yaushe gamo, sannan ta kara gabatar masa da Aziza.