AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

     Kamar yadda Khalil ya fada bayan sati daya da dawowarsa aka zo aka tsaida ranar aurensa da Sultana wanda za ayi nan da wata daya da sati uku,wanda Nawaz shi da Khalil ɗinne suka yanke wannan shawara.


  Tunda aka saka wannan rana Khalil ya hana Sultana sakat, tayi-tayi ya bari suje kano amma ya ƙi, yace ta bari ba yanzu ba,ita da basu shiri da yan kano din ma, bayan sunyi haka da shi ta gayawa Aziza, Aziza ke tambayarta meyasa bata son kano, Sultana ta ce

“Ni da Hanan yadda kika san kamar wuta da auduga, sannan rashin kirki da mugunta irin na Maman Hanan da Maman Beenah abun ba a magana karki so ki yadda suke yiwa Yaya Almazeen, kuma shine mai kudin fa, gwara ma dai Beenah muna ɗan shiri amma banda Hanan, bana son halinsu ne sabida muzgunawa Yaya Al’mazeen da sukeyi”
“Mutane kam ai sai addua, Allah ya kyauta kawai” Sultana ta amsa da amin.

   ????????????????

Hadiza! Hadiza! Hadiza!.

Da gudu Hadiza ta fito ta zube a gaban Hajiya Lawiza Maman Hanan kenan, cikin yauki ta kalli Hadiza ta ce
“Hadiza, maza ki kirawo Azima ki haura da ita can sama part din Al’mazeen ta fara gani da tattare ƙura, suna nan dawowa nan da sati biyu”

  ????????????????

BACCI NAKEJI WLH????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????????????‍♀️
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

PAID.
????️=5️⃣7️⃣↪️5️⃣8️⃣

Damm! Gaban Azima ya buga tayi saurin ware blue eye dinta, ta maimaita
“Azizaa! Aziza dai!?” Maman Beenah ne ta kallesa ta ce
“Al’mazeen kasanta ne dama? Sannan sunanta ba Aziza bane, wannan sunanta Azima ne” girgiza kai Al’mazeen ya hau yi yana ƙarewa Azima kallo,yatsar hannunta ya kalla yaga irin zoben da ya gani a hannun Aziza dazu, sannan ace kuma ba Aziza bane? Ko dai ya yi gamo ne? da sauri ya haura sama, yana shiga part dinsa ya ga sai kyalli yakeyi an gyara sosai bai tsaya karewa ɗakin kallo ba, wayarsa ya ɗaga zai kira Nawaz sai kuma ya fasa ya kira layin mom,ringing uku mom ta daga suka gaisa yace mata ya isa lafiya,mom tayi hamdala ta masa sannu da hanya ta kara da cewa
“Ya ka samu mutanen gidan,su Hajiya Lawiza da Hajiya Luba?da kuma yaran?”
“Lafiyar su lau”
“Ya naji muryarka haka Al’mazeen? Kamar kana cikin tashin hankali ko damuwa, ba dai daga dawowarka suka fara cusa maka baƙin ciki ba?”
“A’a mom basu bane, amm nace ba mom? Aziza fa? Ya jikin nata?”
“Alhamdulillah da sauki, ko ba sauki musulmi ai ba zai ce babu ba sai dai yace alhamdulillah, Sultana tana tare da ita dik da naji tace tana da paper 12 zataje skull ga abokin naka ma shima baida lafiya, bayan tafiyarka da ya shigo idonsa a kumbure wai kansa ke ciwo”
“Subhanallahi! Allah ya basu lafiya, dama tunda na ga yanayinsa na san bai da lafiya dan ina kyautata zaton jiya bai yi bacci ba dan a parlor na samesa zaune da asuba, amma da na tambayesa yace min ba komai,zuwa 12 in sha Allah zan kirasa naji ya jikin nasa maybe yanzu yana bacci, bari na kira sultana naji ya na Aziza yake” nan ya yiwa Mom sallama yana katse wayar, sultana ya kira a lokacin tana magana da wata classmate ɗinta a waya,tana gaya mata ba zata samu zuwa skull ba, Brothern’ta da sistern’ta basu da lafiya, suna cikin magana ta ga wayar Al’mazeen ya shigo dan haka sukayi sallama da kawarta ta daga na Al’mazeen, sai da ta masa an isa lafiya kafin yace mata
“Ya jikin Aziza?” kuka ta sa tana kara masa wayar a saitin fuskar Aziza dake fidda huci tana gurnanin zazzabi,bayan ta kara masa wayar yaji kafin ta maida wayar kunnenta tana ci gaba da kuka tana fadin
“Bro ka ji ta ko? Yadda ka barta haka take sai ma abunda ya ƙaru”
“Subhanallahi! Allah ya bata lafiya kin bata wa innan maganin kuwa?”
“E bai jima ba da na bata,amma kamar bai yi aiki ba”
“Karki damu kinji zai mata a hankali kiyi ta yi mata addua, Allah ya bata lafiya!” daga haka ya katse wayar,ya hau jeka ka dawo a daki yana saƙa da warware, “AZIMAA!?” ya faɗa yana rike kai
“To ko dai yar uwar Aziza ce? Tunda sunansu mai haɗi iri ɗaya ne? Amma kuma Nawaz yace an kashewa Aziza kowa bata da kowa! To ba mamaki kamanni ne” daga haka ya miƙe ya shige toilet abunsa ya watsar da tunanin jin yana shirin saka masa ciwon kai.

    A kasa kuwa ba ƙaramin daru aka sha da Azima ba a kan abincin da za a kai wa Al'mazeen, ta dage ta kafe tace wlh ba zai ci wannan abincin ba, Maman Hanan ta ce

“E lallai kam Azima, wato kin samu waje kinyi freesh shiyasa zaki fara murza iskanci son ranki ko! To wlh ki bi a hankali” ba tare da Azima tayi magana ba ta karbi abinci a hannunsu Hadiza tayi wajan kitchen da shi ta ajiye ta hau yiwa Al’mazeen sabo, girki takeyi duk da ba wai ta wani iya sosai bane, amma da taji ance Al’mazeen zai dawo yasa kullum tana kitchen dasu Hadiza tana ganin yadda ake girkin barin ma wanda aka ce mata Al’mazeen ɗin ya fi so.

  Tana girki tana tunanin sunan da Al'mazeen ya kirata da shi,hakika hankalinta ya ɗan tashi

“Aziza! Aziza! Ina Al’mazeen ya san Aziza? Shi da baya ma kasar, to ba mamaki wajan kiran sunanta aka samu kuskure zai ce Azima yace Aziza” share zancan tayi ta ci gaba da aikinta dan ta san wan can sakaryan tana can jeji, sai bayan da ta kammala ta jera a tray ta dauka ta haura sama.

   A hankali ta tura kofar ba tare da tayi sallama ba, Al'mazeen na zaune a parlour da system a gabansa da alama aiki yake yi, yaji mutum ya shigo ba sallama, haɗe rai ya yi, ita kuwa Azima sallama baya daya daga cikin dabiunta, abunda Al'mazeen ya tsana kenan, dan shi mutum ne mai girmama addininsa fiye da komai a rayuwarsa, Al'mazeen da na riƙo da addini fiye da tunanin mai tunani, murya can kasa yace

“Fita ki min sallama, karki sake ki min magana ba tare da kin min sallama ba” juyawan kuwa tayi ta fita ta sake shigowa tare da fadin
“Salamu alaikum” tana tura bakin, bakintan kawai yake iya hangowa yadda take tura shi tana murguɗa shi tunda fuskarta a rufe yake, abun dariya ya ba sa dan haka ya ɗan murmusa ba tare da ta gani ba, abincin ta ajiye tare da fadin
“Kayi hakuri” bata ma san sadda tace masa ya yi hakurin ba, jinjina kai Al’mazeen ya yi,ya ce
“Kece Azima?” ta gya ɗa kai,
“Daga ina kike?” damm! gabanta ya buga, amma da shike zuciyarta a tsaye yake ƙyam tace
“Daga can cikin kauyen kano a wata rugar fulani”
Al’mazeen a ransa ya ce
“E tabbas to basu da alaƙa da Aziza”
“Ina abincin da aka dafa min?” murguɗa baki Azima tayi tace
“Na ajiye musu a bayan kitchen idan sun ga dama su dauka su ci ko su san yadda zasuyi da shi” tana gama fadi ta mike fuuuu ta fice, girgiza kai Al’mazeen ya yi ya ci gaba da aikinsa, sai wajan sha daya da rabi ya ja tray din da ta ajiye masa ya buɗe yana kan buɗewa sai ga ta ta shigo ta duƙa tunowa da dazu ya koreta akan bata yi sallama ba sai ta kara ficewa da sauri ta shigo tana fadin
“Salamu alaikum! ai saika kirani nazo na zuba maka”
“Kina da waya ne?” girgiza kai Azima ta yi ta ce
“A’a bani da shi,amma idan kace AZIIIMAAAA!!????️Ai zanji na taho da sauri!” girgiza kai Al’mazeen ya yi ya tashi zai shiga daki, da sauri ta ce
HAMMA MAZEEN abincin fa?”
Cak Al’mazeen ya tsaya yana nanata sunan “Hamma Mazeen!” kirjinsa ne ke bugawa da sauri-sauri,
“Ina zuwa ki zuba kawai ki tafi” ya faɗa yana shigewa bedroom, Azima haushin kanta ne ya kamata, wai meyasa take masa abu kamar wanda ake sakata ko ana bata umarni ne? Meyasa take jin faduwar gaba a kansa, meyasa take jin makarin gubarta yana tattare da shi? Amma kuma tana ji kamar ita da shi an jona musu kuran karfe, saurin tashi tayi ta fice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button