AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

     ????????????????????

Sai 1 Nawaz ya farka ya ɗan ji kan nasa da sauki amma kan ya yi masa nauyi, wanka ya yi a nan daki ya yi sallah, sannan ya lallaba a hankali ya shiga cikin gida, ba kowa a parlor dan haka ya fara haurawa sama, sai kuma ya juyo yana kallon kofar dakin Aziza, saukowa ya yi ya nufi dakinta, a hankali ya tura da sallama, mom da sultana ma ashe suna dakin, Aziza na jingine tana sallah a zaune a kan gado, saurin karasowa kusa da mom ya yi ya ce
“Mom jikin nata ya yi tsanani ne haka shine baku tasheni munje asibiti ba?”
“Humm! Nawaz kai ma fa ba lafiyar gareka ba, ka ganta nan jiya bata rintsa ba”
“Bari ta idar da sallar sai a kaita asibiti”
“A’a Nawaz ba sai anje asibiti ba, babu amfani, zaku ƙara huda mata jiki ne kawai, yanzu sai kuce zaku sossoka mata allura a ɗaura mata ruwa aja jini, wanda hakan kuma…!” sai Mom tayi shuru, a lokacin Aziza ta sallame sallarta, Nawaz ya miƙe yana fadin
“Mom dan ta gaya miki bata son allura sai a biye mata dan lafiyar wa akeyi? Ina dan lafiyarta ne!” ya faɗa cikin haɗa fuska, ya nufeta yana faɗi wa Sultana ta tashi taje ta cewa driver ya juya mota.

Aziza kuwa ganin ya nufota yasa ta kwalalo ido waje, dan kuwa jikinta yana fidda farin sab'ar maciji idan ya gani fa? Saurin girgiza masa kai ta hau yi muryarta a shaƙe da baya fitowa sosai ta hau fadin ya kyaleta kar yazo inda take, ko kaɗan bai tsaya ya saurareta ba yasa hannu ya yaye bargon jikinta ya kamo hannunta,ji yayi kamar wani fata ya maqale masa a hannunsa, sake hannun nata ya yi yana kallon tafin hannunsa, wani zare ido Nawaz ya yi sai kace idon zasu faɗo ƙasa,ganin sab'ar fatar maciji fari sol a hannunsa, Aziza kuwa banda kakkarwa babu abinda jikinta ke yi,tana sake boye hannunta a cikin hijabin dake jikinta tana jan bargo tana son rufe kafafunta, saurin fizgar bargon Nawaz yayi jikinsa na kyarma, yasa hannu ya figi hijabinta ganin haka yasa mom cewa da sauri

“Nawaz ka haukace ne!? baka da hankali ne!? mai kake shirin yi!?” ba tare da ya saurari mom ba ya ɗago Aziza tsaye wacce jiri ke kwasarta, hannunta ya riko ya ware nan kuwa ya ga jikinta duk b’awu, a lokacin kuma Aziza ta suma, dagota ya yi yana jijjigata cikin tashin hankali yana tambayarta wacece ita.

Cikin kuka Sultana tasa hannu ta kwace Aziza daga hannun Yayanta ta rungumeta ta ce
“Yaya ta suma fa? Dan Allah Mom kiyi wani abu a kai”

Nawaz yasa hannu zai kara jan Aziza daga jikin sultana, sultana tayi saurin juyawa da ita ta kwantar da ita tana murza tafin hannunta tana kuka
“Zan fa karyaki Sultana ina wasa dake ne!!?”
“Wlh Yaya ko kasheni zakayi ba zan bari ka kasheta ba, dan Allah mom kiyi magana ki gaya masa gaskiya,babu amfanin wannan boye-boyen”

   "Nawaz ya isa haka! Aziza Macijiya ce!" Mom ta faɗa a tsawace,

Nawaz ne ya yi baya-baya yayi zaman yan bori sharab, mom ta karaso ta kama hannunsa.

kenan mafarkinsa akan yarinyar macijiya ce gaskiya ne? Kallon Mom ya yi da jan ido ya ce
“Mom da macijiya muke rayuwa kuma ke ma kin sani? Taya hankali zai dauka ace mutum maciji? Da ace sultana ce ta faɗa ba abunda zai hanani ban kaita asibiti an duba min kwakwalwarta ba”
Ajiyar zuciya mom tayi tace
“Zaka iya tsayawa ka saurareni uhum? Nawaz magana nake maka” kifa kansa ya yi a kafadar Mom hawaye suka hau gangaro masa wanda bai san dalili ba.

   "Nawaz labarin Azima da Aziza da baffansu da kauyensu abun tausayi ne mai cike da zallar al'ajabi" cikin taushin murya Mom ta hau zayyanawa Nawaz labarin Aziza bata boye masa komai ba kamar yadda Aziza ta ba su haka ta bai wa Nawaz, mom tana gama ba shi labarin ya dago yana fadin

“Wlh mom yawancin abun da kika faɗa min ina ganinsa a mafarkina, tun ranar da na bugeta a mota na kawota kaduna tun daga ranar na daina bacci kirki,mom ina yawan ganinta a siffar macijiya tana kuka tana neman taimakona!” jinjina kai Mom tayi ta ce
“Ba mu san me Ubangiji ya boye tsakaninka da Aziza ba Nawaz, amma inaso muyi wani jahadi wana Allah ya zama silar shigarmu aljanna, Nawaz har zuciyata ina jin Aziza,yarinya ce mai hankali da natsuwa da sanin ya kamata duk da tana da kananun shekaru amma tana da hankalin manya da imani da kaddara ga tawakkali da miƙa wuya,kuma dama abunda akeso kenan ga musulmi mumini ko mumina, Nawaz sultana zata bar gidan nan kwanan nan, dan Allah ina so kayi jahadi ka AURI AZIZA!!” dummm!! gaban Nawaz ya bada ya kalli Mom da sauri, Mom ta gya ɗa kai tana fadin
“Tun kana yaro ban taba cewa ina neman alfarma ka kasa min ba, ina so ka taimaka ka auri Aziza, ka zamo silar warkewarta, duk wanda ya zama silar farin cikin mutum daya Allah zai zama silar farincikinsa a ranar da babu wani mai gata sai fiyayyen halitta, Nawaz kana da ilmi duk abunda zan gaya maka ka sani sai dai na kara yi maka tuni, idan ka auri Aziza ka zamo silar warkewarta hakika zaka saka mutane dayawa ne farinciki, zaka fidda UWA da UBA daga ƙunci, da sauran yan uwansu, wlh har zuciyata na aminta” kallo fuskar Aziza Nawaz ya yi, hakika daga fuskarta zaka san cewa tana jin jiki
“NA AMINCE MOM! ZAN AURETA!” da sauri Sultana tazo ta duƙa ta rungumesa cikin murna, “da gaske yaya zaka aureta!? Wayyo dadi wlh nayi farinciki”
“Allah ya maka albarka Nawaz” cewar mom tana shafa kansa.

  Nan suka zauna a dakin har sai da aka yi sallar la'asar kafin suka fita da niyyar sallah, nawaz msallaci yaje, bayan sun idar ya jima yana kwararo adduoi a kan wannan lamari da yake gani tamkar a mafarkin da ya saba ne.


 Bayan ya dawo part dinsa ya wuce, ya dauki wayarsa ya ga miss calls din amininsa,kiransa ya yi ya daga yana tambayarsa ya jikinsa,Nawaz ya amsa da sauki shima yana masa ya gajiyar hanya, Al'mazeen ya amsa da alhamdulillah ya kara da fadin ya jikin Aziza, alhamdulillah Nawaz ya fada, sun ɗan jima suna magana inda Nawaz yake ji ko ya gayawa Al'mazeen? Daga baya kuma ya fasa har suka gama wayar sukayi sallama.



  Sai wajan shidda Aziza ta farka sultana ta taimaka mata tayi alwala tayi sallah a zaune kamar dazu, bayan ta idar tayi addua sultana ke gaya mata sadda ta suma mom ta gayawa Yaya Nawaz komai, a lokacin da sultana ke gayawa Aziza Nawaz sun shigo shi da mom, kuka Aziza ta saka tana fadin

“Shikenan zai koreni! Dan Allah Anty Sultana ki ba shi hakuri kar ya koreni, wlh da na samu Azima zan tafi da kaina,tafiya na har abada ba zai sake ganina ba in sha Allah” rasss! gaban Nawaz ya buga jin tace zata tafi na har abada, a hankali Nawaz ya juya ya fita ganin yadda take kukan duk sai yaji babu dadi yana danasanin abunda ya mata, tayi mugun karya masa zuciya.

Mom tace
“Injiwa yace zai koreki a gidan nan? Bana so na ƙara ji kince zaki bar gidan nan na har abada, dan kuwa kina nan a gidan nan har abada In sha Allah,kinji ko?” Aziza ta gya ɗa kai tana kuka.

@@@@@@@@

      Da washe gari tana kwance tana fama da kanta,bata san ta yadda zata samu furen huriri ba, da ace ta samu da tuni an wuce wajan, turo kofar akayi da sallama, jin muryan mai sallaman yasa gaban Aziza bugawa, murya na rawa ta amsa, karasowa yayi a hankali ta dago idonta ta kallesa a tsorace, ta gansa da plate a hannu, mamaki ne ya kamata, zama yayi a gefen bedside'drower fuskar yau da sassauci, murya a can kasa ya ce

“Ya jikin naki?”
“Alhamdulillah, ina kwana?”
“Tashi kici abinci ki sha wannan rubutun, wani babban aminin Daddyna ne malami ne wajansa naje jiya da daddare na masa bayani a kan matsalarki, yace na baki wannan zakiji dama-dama duk da ba lallai bane ya dauke miki abunda kike ji gabadaya ba, amma zaki samu karfin jiki” mamaki ne ya ƙara kamata, amma bata da lokacin tsayawa mamakin, a hankali ya dagata ya jinginata da pillow, ya dau spoon ya ɗibi abincin ya kai mata shi saitin bakinta, tsananin mamaki ya hana Aziza buɗe baki taci dan ji take kamar mafarki takeyi, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Nawaz furta kalman
“I’m sorry Aziza” a sanyaye, sake yin ƙasa da kanta Aziza tayi gabanta na ci gaba da bugawa, muryarsa taji yana kara fadin
“Na sani, na cusa miki tsorona a zuciyarki, am sorry once again” kuka ta fashewa da shi, ya ɗan rintse ido ya ce
“Kamar na gaya miki bana son kuka ko?” ta gya ɗa kai
“To meyasa kikeyi?”
“Na…ba…ri” ta fada murya na rawa,
“To kici abincin” ya fada yana bata a baki cike da tausayinta, bata wani ci sosai ba ta ce masa ta koshi, cup ya dauka ya tsiyaya mata rubutun ya bata tasha tana sha taji kanta na wani mugun juyawa, ba jimawa ta zube ta hau bacci, ganin tayi bacci yasaka shi tashi ya fita,a parlour ya samu Mom da sultana, zama ya yi kusa da mom, ta ce
“Allah ya maka albarka Nawaz, Allah ya faranta maka duniya da lahira” a tare suka amsa da amin shi da sultana.

  Ko da ta farka taji jikin nata da dama-dama,dan kuwa ta miƙe da kafafunta har tana iya tafiya, jirin ne dai bai daina dibarta ba.

????????????????????????

     Bayan kwana biyu taji sauki alhamdulillah amma lokaci zuwa lokaci jiri na zubar da ita, tsakaninta da Nawaz kuma yanzu babu tsangwama, sai tausayawa, har mamakinsa take yi,ita dai ba zata gushe ba tana yiwa su mom addua.

????????????????????

Bayan sati daya da dawowar Al’mazeen kano komai ya canza a gidan, Azima ke zuba mulki son ranta, ga shi yanzu tana kwatowa Al’mazeen yancinsa a cikin gidan, duk wani guba da maganin mallaka idan aka zuba masa a cikin abinci sai dai azo a samu Azima ta juyewa karnuka abincin, su Hajiya Lawiza da Hajiya Luba sun rasa yadda zasuyi da Azima, ta bangaren Al’mazeen kuwa a sati ɗayan nan kacal ya shaƙu matuƙa da Azima dan har zuciyarsa yake jinta, shi mutum ne mai son kulawa da soyayya amma bai samu ba, sai ga shi rana tsaka ya samu a wajan mai aiki dan ba karamin kulawa da shi Azima ke yi ba.

Kamar yadda Azima bata son dogon magana haka ma al’mazeen, amma su kan zauna suyi hira, inda take gaya masa ai itama bata da kowa duk an kashesu, idan Azima na magana ya kan ji muryan Aziza, duk da ba wai ya taba ganin fuskokinsu sosai bane, dan itama Azima duk shaƙuwan nan bata buɗe fuskarta, bayan dawowarsa da kwana uku taso guduwa ta bar gidan amma haka ta kasa har ya kai sati daya,inda takeji kafafunta sunki amincewa da barin gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button