AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yau ma kamar kullum ya shirya zai tafi asibiti, yana kan saukowa kasa har ya zo step din karshe sai ga Hanan, tana ganinsa sarai ta bangajesa briefcase dinsa ta faɗi, amadadin ta tsaya ta ba shi hakuri sai tana shirin rab'awa ta gefensa ta wuce, Al'mazeen cikin haushi ya ce

“Kee Hanan! Baki ga abunda kika min bane! Zo ki dau jakata ki bani”
“Wlh Al’mazeen sauri nake yi inaso naje na gwada wannan memoryn ne” ta faɗa tana shirin hawa sama taji an wani fizgota ta baya, ta ma zata Al’mazeen ɗin ne amma tana juyowa ta ga Hajja Azima wacce yau tayi shigan riga da wando idonta sanye da wani black shadow, Al’mazeen ne ya siyo mata jiya kasancewar itama ta masa karya da cewa ai idonta na ciwo.

fuskarta a haɗe da ka ganta sai tayi maka kama da irin bosawan film din indian nan, ashar Hanan tayi  ta kalli Azima sama da kasa tace

“Wato na kauye ya shigo gari ko?”

   "Ki duƙa ki ɗau jakarsa ki basa sannan ki ba shi hakuri" Azima ta faɗa cikin murya mai nuna umarni take badawa ba shawara ba.

“Lalala! Wlh ni ba irinsu Hajjaju bane, da zaki dinga yab’a musu magana kina juyasu kina basu umarni kina gasasu! Wlh ni karyaki zanyi! dan ni bana son raini!”

Hannunta Azima ta kama ta murɗe Hanan tasa ihu, Azima ta cije baki tace
“Kinga ni nayi miki kama da wacce take son raini? Tun kafin ki san wacece asalin Azima dau jakarsa ki ba shi sannan ki ba shi hakuri!”

Maman Hanan da Maman Beenah da beenah da Hanif ne suka sauko jin ihun Hanan.

 Nan suka ga Azima murɗe da hannun Hanan Al'mazeen na cewa da Azima a kan ta saki hannun Hanan, ita kuwa tace ba zata sake ba, sai Hanan tayi abinda ta sakata,jin wuya yasa hanan cewa zata yi yadda Azima tace, sakinta Azima ta yi ta duka ta dau jakar ta ba shi ta ce

“Kayi hakuri”

 "Kayi hakuri wa?" Azima ta faɗa a tsawa ce.

“Kayi hakuri Al’ma….” dauketa da mari Azima tayi har saida Hanan ta kai kasa,Azima tace
“Hamma! Daga yau idan na cire su Hajiya duk gabadaya Hamma Mazeen zaku na ce masa tunda ya girmeku, maza gaya masa!”

“Kayi hakuri Hamma Mazeen” Hanan na faɗi ta hau sama da gudu, Maman Hanan da Maman Beenah da Beenah suka bi bayanta, Al’mazeen ya haɗa rai yace
“Ina bakijin maganata? Ina cewa ki saketa amma kinki ko?” turo baki tayi tace
“Ba komai nake yi daukawa ba,kuma ma ai sabida kai nayi” tana gama fadi ta fice tana tura baki ta bar shi tsaye, murmushi Almazeen yayi ya fice ya tafi office.

   Ko a office din ya kasa aikin kirki tunanin Azima kawai yakeyi, wayarsa ce tayi kara yana dubawa ya ga Alisha,guntun tsaki yaja,yau kusan sati tin dawowarsa kano take kira baya dagawa.


   @@@@

“Yanzu me zamuyi wa wannan yarinyar dan tana son fin karfinmu?” cewar Maman Hanan, Maman Beena ta ce
“Shegiyar taga kudi duk yadda akayi sonsa takeyi”
“Abunda za ayi muyi mata sharrin sata na san shi da kansa zai koreta, dama yau su Summy da Sady zasu zo ko?”

“E sunce ma sun kusa isowa”.

(Summy da Sady, kannan Hajiya Lawiza da Hajiya luba, wanda suke so su aurawa Al'mazeen).


  ????????????????

MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

PAID.
????️=5️⃣5️⃣↪️5️⃣6️⃣

Da kyar ya tattaro jarumta jin yadda kafafunsa suka yi sanyi ya shiga parlourn, ya samu Al’mazeen zaune yana cin abinci, zama shi ma ya yi Sultana ta zuba masa ta tura masa gabansa, amma tunani yasa ma yaji abincin ya fita kansa, Aziza kuwa tin sadda ta ba wa driver sako ta maqale ta kasa shiga gidan ganin yayi babakere a bakin kofa, sai da ya shiga ta siɗaɗo a hankali ta shige dakinta da gudu,tana shiga ta zube a gado ta saki kuka, ba jimawa Sultana ta shigo ta sameta tana kuka ta ce
“Subhanallahi! Aziza lafiya me ya faru?”
Cikin kuka ta dago ta ce
“Anty Sulty Hamma Nawaz ya ga idona”
“Mtswww! To sai me dan ya ga idonki?”
“Wlh tsoro nakeji kar ya koreni, dan naga yana mini kallon tuhuma kamar yasan wani abu a kaina”
“Kinga Aziza dan Allah ki kwantar da hankalinki ki samu natsuwa kinji? Babu abinda zai faru,na san me zanyi, kuma ma ai idan ya san wani abu a kanki ai ya rage mana aiki, balle ina ma zai sani? daga wajena sai wajan Mom,kuma Mom da kanta ta kwabeni tace kar na gaya masa ta san ta yadda zata gaya masa,na tabbata mom bata gaya masa ba,dan da ta gaya masa zata gaya min, dan haka ki dai na damun kanki” rarrashinta Sultana ta yi har ta samu tayi shuru, kafin suka koma hiran karatu.

    Da kyar Nawaz ya yi cokali uku a abincin ya tashi, Al'mazeen ya ce

“Dude ka ce yunwa kakeji amma ka kasa cin abinci i hope dai komai lafiya?”
“E lafiya,ina zuwa” ya fada yana ficewa, part dinsa ya koma ya kwanta a dogon kujera, hakika idonta babu bambanci da wanda yake gani a mafarkinsa, wai wacece wannan yarinyar nan ne kam? Ya zama dole ya tambayeta ita wacece sannan miye haɗinsa da ita,idan ma mayya ce to wlh shi namansa da ɗaci,kuma sai ya danna mata kashedi ta fita rayuwarsa ya huta, ya kara jan tsaki.

  Bayan Al'mazeen ya gama cin abinci ya koma part din Nawaz ya samesa yana kwance a dogon kujera,zama ya yi a 1siter yana fuskantar Nawaz ya ce

“Dr lafiya kuwa?”
“Nml, kawai kaina ke ɗan min ciwo”
“Ayya sorry, to ka sha magani mana”
“No ba yanzu ba, bari na gani zuwa dare idan banji dai-dai ba zan yiwa kaina allura ko kuma ka min”
“Ok, Allah yakara sauki”
“Amin” Nawaz ya fada yana lumshe ido, wayar Al’mazeen ne ya sake ƙara, Nawaz ya bude ido yana jan dogon tsaki
“Mtswwwwww!!! Wannan mayyar ce ko!?”
“Meyasa kake ce mata mayya bayan kasan ita zan aura?”
“Wlh Allah ya sawwake maka da aurar wannan kakar taka, duk da nasan bana son yarinya karama amma ina zaka kai Alisha? ni fa wlh na rasa meke damunka, duk matan duniya ka rasa wacce zaka zab’a ka aura sai Alisha? Ga uban saka gashin doki a kai, ga ƙarin farce, ga saka gashin ido, ga rashin kunyar taunar cingam, gabakidayanta ma wlh zube take da karuwai! Dan Allah ka bar batun auren Alisha!”

 "Haba dan Allah Nawaz ya isheka haka mana! Kai kullum baka da aiki sai kushe Alisha? A tsammaninka dadi nakeji idan kana kusheta? Shuru fa kawai nake yi" Al'mazeen ya faɗa ransa a haɗe, Nawaz ya yi tsaki ya ce

“Aikin banza! Abunda kai ma ba sonta kake yi ba, dan an kusheta miye naka na jin haushi,wlh da ace kana son Alisha yadda nake kusheta da mun jima da rabuwa da kai” girgiza kai Al’mazeen ya yi ya ce
“Mace ba zata rabamu da kai ba Nawaz, idan na rabu da kai waye zai dinga supporting dina? Plss karka kara fadin haka, abunda yasa nake son auren Alisha ita tana sona sosai,kuma ina sa ran zata bani kulawar da na rasa da soyayyar da ban samu ba” ya karasa fadin idonsa na canza kala,ganin haka yasa Nawaz matsowa kusa da shi ya zauna a hannu kujera ya riƙo kafadarsa yace
“Karka fadi haka, In sha Allah Aminina ya kusa fara dariya, ka tsaya kuma ka gani,mahakurci mawadaci, na fadi dai-dai?” Nawaz ya fada yana murmushi tare da miƙawa Al’mazeen hannu, shima Almazeen murmushin ya yi yana haɗa hannunsa da na Nawaz sannan suka rungume juna.

  Yau wuni zunbur Aziza ta yi a daki ta ki fitowa, bayan sallar isha'i gabadaya suna zaune a parlour suna hira, Aziza kuma na daki tana rike da book amma a zahiri ba karatun take yi ba,tunani takeyi na yadda idan mom ta gayawa Nawaz cewa ita macijiya ce ya zai dauki lamarin, tayi nisa sosai a tunani taji an turo kofar da sallama, amsawa tayi tana ɗaga idonta ta sauke a kan Mom, Mom ta ce

“Lafiya kuwa yau kika wuni a daki Aziza? Ko wani abu na damunki shine kika kasa gaya min?” murmushin yaƙe Aziza ta yi ta ce
“A’a Mom, yau din ne dai nake ɗan jin zazzabi amma ba sosai bane”
“Subhanallahi! Ai saiki faɗi ba wai ki zauna shuru a daki ba, gamu da likitoci har biyu a gida, bari nayi wa Nawaz magana ya zo ya dubaki, ko allura ya miki” zare ido Aziza ta yi sai kuma ta koma ta hau narai-narai da fuska, Mom ta ce
“Ai ba zaki zauna da ciwo ba” Mom ta fita tana ambatar sunan Nawaz, wanda suke lissafin bikin sultana shi da Almazeen
“Na’am Mom” Nawaz ya amsa yana maida hankalinsa ga mom
“Nawaz dan Allah zo ka duba Aziza kayi mata allura, ashe bata jin dadi ne shiyasa ta wuni yau a daki” Sultana ta ce
“Ya Salam! Aziza akwai zurfin ciki wlh,nan fa dazu babu kalar tambayarta da banyi ba amma tace min babu komai, dan Allah Bro Nawaz muje ka dubata”
“To ba ga Al’Mazeen ba” Nawaz ya fada yana shagwabe fuska yana kallon Mom, mom ta ce
“E ai naga Al’mazeen din nace kai kaje ka dubata, idan kuma ba zaka dubata ba sai ka gaya min na cewa Son yaje ya duba min ita” Nawaz ya miƙe yana fadin
“Yaushe na isa, yi hakuri Mom luv ɗina, yanzu kuwa zan dubata, Sultana je ki dauko min box ɗina” Sultana ta amsa da to ta fice da gudu, shi kuma ya yi hanyar dakin,yana zuwa ya tura kofar ya sameta kwance ta zubar da gashinta a kan pillow, a ransa ya ce
“Wai idan wannan gashinta ne ma sha Allah” sai da ya yi gyaran murya kafin ya yi sallama, da sauri Aziza ta mike tana jan hularta dan ta rufe kanta, tana saka hular wanda bai rufe mata gashi ba sauran ya kwanta a kafaɗunta, ta dukar da kai jikinta na rawa, kallonta Nawaz ke yi yana yaba kyawunta a zuciyarsa sai furta ma sha Allah yake yi, har Sultana ta shigo dakin tana masa magana amma bai ji ba, sai da ta tabosa kafin ya juyo, dariya Sultana ta hau maqalewa tana miƙa masa box din, ganin haka ya dalla mata harara ba shiri ta hadiye dariyarta, murya can ciki yace
“Me kike ji a jikinki?”
Murya na rawa Aziza ta ce
“Amm…..uhum……zazzabi ne sama-sama”
“Kinci abinci?”
“E naci”
“Tun yaushe?”
“Tun karfe biyu”
“Na rana?”
“E”
“Baki da hankali ne! Taya zaki zauna da yunwa bayan baki da lafiya! Ko baki san shima wani babban ciwon bane! Sultana je ki kawo mata abinci yanzun nan taci a gabana, na duba na gani allura zan mata ko magani zan bata” jin ya kira sunan allura yasa Aziza ta ɗago, nan hawaye suka b’alle kamar an buɗe pampo, cikin fuskar tausayi ta ce
“Dan Allah Hamma Nawaz zan sha magani amma banda allura,bana son allura” ta hau masa magiya tana kallonsa amma shi idonsa a kwayar idonta yake yana kalla bugun zuciyarsa yana kara tsananta, da kyar ya dauke idonsa a kanta ya juya baya, sultana ce ta shigo da plate da abinci da ruwa ta mikawa Aziza dake kuka wiwi, Nawaz ya ce
“Na fa tsani kuka, kici abincin nan idan baki son allura,bana son shirme, idan kuma baki ci ba alluran zan miki” jin haka yasa Aziza fara ɗurawa cikinta abinci, sai da taci rabi ta kalli Sultana da tayi shuru kamar bata wajen, ta ce
“Anty sulty na koshi, Hamma Nawaz bani maganin” kallon Sultana yayi babu alamun wasa ya ce
“Karba plate ɗin ki fita da shi” karba sultana ta yi ta fita,sultana na fita ya hau jan ruwan allura ganin haka yasa Aziza fashewa da kuka tana ba shi hakuri kar ya mata allura, bata so ko kaɗan karfe ya huɗa jikinta kasancewar tana da jikin maciji hakan zai iya mata illa dan karfe ne zai huɗa jikinta,maciji kuma baya son tab’o, ko kaɗan Nawaz bai damu da kukanta ba duk da yanaji har can kasar zuciyarsa, ya rasa meyasa yake jin tausayin yarinyar, bai so ko kaɗan yana mafarkinta a mugun yanayi, bayan ya saita alluran ya nufeta, da sauri Aziza ta miƙe ta diro a gadon ta hau ja da baya, ihu ta saka zata gudu yasa hannu ya jata, Mom da Sultana da Almazeen da suke parlour suka jiyo ihun Aziza da sauri suka tashi suka yo dakin da gudu, suna shigowa suka samu Aziza da Nawaz sai zagaye daki suke yi, Mom tace
“Miye haka me zan gani?” ganin Mom yasa Aziza rugawa da gudu ta buya bayan mom, tsaki Nawaz yayi yasa hannu ya jata a bayan Mom yana fadin
“Mom ai kinga irinta, bana son hidiman yarinta wlh,allura fa zan mata amma kalli yadda ta sakani zagaye daki sai kace wacce zan zare ranta!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button