AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Haba Nawaz! Miye haka sai kace ba likita ba, ka lallabata mana ka bita a hankali, Aziza ki tsaya kinji? idan ya miki zakiji sauki, kinga yau kin wuni a daki ga jikinki da zafi, bana son ina ganinki a haka kinji?” girgiza kai Aziza ke yi tana fadin
“Mom zai min illa!”
“To dan Allah fa kiji mom, wai zai mata illa, taya allura zai miki illa ana shirin nema miki lafiya” yana faɗi ya haɗata da jikinsa ya matseta,a karfinta na nml mutane ta kasa kwace kanta, sadakarwa tayi, jin ya matseta ya danna mata allura yasa ta ƙanƙameshi tana kara sa kuka, allura biyu ya mata kafin ya saketa ya fita a dakin, Al’mazeen wanda ya ƙura mata ido yana kallonta ya fita ya bar su Mom da sultana suna rarrashinta, cikin kuka ta ce
“Mom allura karfe ne,kuma jikina na maciji ne, zai min illa” a tare mom da sultana suka zaro ido,mom tace “Aziza meyasa baki gaya mana da wuri ba? Subhanallah! Yanzu me zai faru?” girgiza kai Aziza tayi jiri na dibarta ta zube a jikin mom abun tausayi, hawaye Mom ta goge tace
“Ya Allah, kasa abunda yake zuciyata wanda nake shirin haɗawa ya zama alkairi, Allah kasa ya zama jahadi dani da iyalaina, ya zama silar shiganmu aljanna!”
“Me kike shirin yi Mom?”
“Inaso na saka Yayanki Ya Auri Aziza!” jinjina kai Sultana tayi ta ce
“Mom nima na jima da fara wannan tunanin, dan babu wanda zai auresu yayi wannan jahadin idan ba wani ikon Allah ba,mom ya kamata ki gayawa Yaya tun daga yanzu, sannan dan Allah mom a daga bikina zuwa shekara mai zuwa” wani harara mom ta gallawa Sultana sannan tace
“To je ki gayawa Nawaz” shuru Sultana tayi dan ko giyar wake take sha ba zata gayawa Yayanta Nawaz a daga bikin ba, yanzu sai ya daki banza.

    Aziza zazzabi da kaɗan-kaɗan ya fara rufeta, ga shi abunda take so babu shi a cikin gari, furen huriri shine zata jiƙa ko ta tauna ganyensa shi kadai ne zai dawo da ita hayyacinta,amma ina zata samu?" haka ta dinga b'ari.

@@@@@@@

     A daren yadda Aziza bata rintsa ba,haka ma Nawaz, wanda da ya rufe ido ita yake gani sadda take kuka tana cewa kar ya mata allura, tausayinta ne ya rufe masa zuciya, tashi ya yi ya kalli Almazeen dake bacci, parlor ya fito ya zauna ya riƙe kansa, ji yake kamar yasa kuka, ko yaje ya ganta ko zaiji sauki a ransa, abunda ya shafe wata uku yanaji a ransa bayaso ya tabbata, baya so zuciyarsa ace ta kamu da son wannan jaririyar yarinyar, sannan meyasa yake mafarkinta tun daga ranar da ta shigo rayuwarsa, meyasa yake ganinta a siffar macijiya? Saurin tashi tsaye ya yi, tare da naushin iska, a fili yace

“Kamata ya yi ace na tsaneki, dan kin takurawa rayuwata da yawa! Tsawon dare bana bacci duk sabida dake! Why! Why! Why Azizaaa!!” ya faɗa yana rike kansa da yakeji kamar zai rabe gida biyu, anan ya zauna har asuba, bayan Almazeen ya farka ya shiga bathroom yayi alwala ya fito parlor nan ya ga Nawaz yashe a parlor, kallonsa ya yi ba tare da ya yi magana ba yace
“Nawaz kayi alwala kazo muje sallah” Almazeen na fadi ya fice, shima Nawaz din alwala ya yi ya bi bayan almazeen bayan sun dawo daga masallaci, Al’mazeen ya hau shiri, yana shiri yana tambayar meke damun Nawaz, Nawaz yace masa ba komai, bai takura ba ya kammala shirinsa, takwas ya shiga ya yiwa mom sallama, mom tace dan Allah kafin ya wuce ya shiga ya duba Aziza ya bata magani dan jiya bata rintsa ba jikin ya yi tsanani,da to Al’mazeen ya amsa.

Aziza kwance sai b'ari takeyi jikinta mugun zafi, hannunta Almazeen ya kama ya ga wani zobe a hannunta a ƙaramin yatsarta na karshe, bai damu ba, ya gama dubata ya ajiye mata magunguna sannan yamusu sallama ya tafi.


  Har wajen mota Nawaz ya raka amininsa tare fadin sai sunyi waya Allah ya tsare, sai da Al'mazeen suka fice kafin Nawaz ya shiga ya gaida mom idonsa a kumbure shima dan baiyi bacci ba ga kansa dake ciwo,cikin kulawa mom ta ce

“Nawaz lafiya kuwa?”
“Mom kaina ke ciwo jiya banyi bacci ba”
“Subhanallah! Sannu Allah ya baka lafiya, ka sha magani ka kwanta”
“To Mom” ya faɗa yana tashi, yana so ya tambayeta Aziza amma yakasa,dan haka ya koma part dinsa ya sha magani ya kwanta.

bayan ya fice wayar Mom ya dauki ruri, tana dubawa ta ga malamin da tasa ya mata istihara a kan Nawaz da Aziza, da sauri ta daga suka gaisa cikin girmamawa,nan ya shaida mata akwai alkairi mai girma da yardan Allah tsakanin Nawaz da Aziza, shi gwargwadon abunda ya gani kenan, godiya sosai mom ta masa nan ta kara jin karfin guiwa.


  Dakin Aziza taje ta samu jikin nata ya kara tsanani, sultana idonta ya zazzago tsananin tashin hankali, Sultana tace

“Mom a gayawa Yaya ko akwai maganin da zai bata, kar ta mutu”
“Sultana shima baya da lafiya idonsa a kumbure da kyar yake budewa shiyasa ban gaya masa na Azizan ba,mu bari nasa ya sauka tukunna” Sultana ta ce
“Mom,anya kaddaran Yaya ba a haɗe yake da na Aziza ba kuwa?” shuru Mom tayi, sai zuwa can tace
“Allah ka bayyana mana Azima cikin sauki Ya Allah, Allah ka jinkirtawa wannan baiwa taka Aziza,duk da tana karama da kananun shekaru amma tana da hakuri da tawakkali da juriya” hawaye Sultana ta goge ta fice a dakin, khalil ta kira a waya tana kuka tana roƙonsa a kan a daga bikin nan kar ayi nan da wata daya, dalili ya fara tambayarta amma ta kasa gaya masa,inda a karshe ya katse wayarsa dan ya kasa gane me Sultana take nufi ko dai ta daina sonsa ne?.

   ????????????????

Yau fa Azima murna tun daga baka har kunne, Al’mazeen na hanya, bayan su Hadiza sun gama shirya masa abinci ita kuma ta gyara masa part dinsa tas, ta zo shiga cikin kitchen ta hangi Maman Hanan akan abincin Al’mazeen tana barbaɗa masa magani, girgiza kai Azima tayi, ta bar wajan ba tare da maman hanan ta ganta ba,amma tayi alkawari ba zata bari al’mazeen yaci abincin nan ba.

    Goma da rabi motar Al'mazeen ta yi parking a harabar parker motoci, ya jima a motar yana sauke ajiyar zuciya kafin ya fito, nan ma aikatan gidan suka hau masa sannu da dawowa tare da gaya masa sunyi kewarsa, cikin parlour ya wuce nan Maman Hanan da Maman Beenah suka hau murna suna masa oyoyo, a hankali ya russuna ya basu girmansu ya gaishesu sannan ya fara haurawa samansa, Maman Hanan ta ce

“Fuskar mutum kamar fura a dame kullum, Hadiza! Zo ku kai masa abincinsa sama”

   "Ba zai ci wannan abincin ba, wani zan dafa masa!" saurin juyowa Maman Hanan da Maman Beenah sukayi suna kallon Azima da kanta ke duƙe da lullubi, cak Al'mazeen da zai hau sama yaja ya tsaya jin kamar ya san mai irin muryar, Maman Hanan ta ce

“Sabida me ba zai ci ba?”
“Sabida bana da bukatar yaci, a bai wa wasu su ci,ko a ajiyewa su Hanif su ci idan sun dawo!” a daqile Azima ke magana, da sauri Al’mazeen ya dawo da baya,nan kuwa ya ganta sanye da bakin abaya itama fuska a lullube, yatsar hannunta ya kalla ya ce
“AZIZAAAA!?” a mamakin ce.

     ????????????????

MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

PAID.
????️=5️⃣9️⃣↪️6️⃣0️⃣

“To yanzu miye mafita? Wani sharrin satan zamuyi mata?” cewar Maman Hanan, Maman Beenah ta ce
“Yanzu ke Maman Hanan idan kikace ta sace miki abu za ace dan ta murɗewa Hanan hannu ne, Al’mazeen ba zai yarda ba, tunda su Sady suna hanya mu jira isowarsa kafin mu yanke shawara” Hanan dake kuka ta ɗago tana kallon hannunta da shati ya fito raɗa-raɗa ta share hawaye tana fadin
“Wlh sai na koya mata hankali, zata gane shayi ruwa ne,ita har ta isa! Wacece ita! Waye ubanta! Tana ‘yar aiki!”

“Bar ta ubanta zamu ci dan naga abun nata ya fara wuce gona da iri” Beenah ta ce
“Hummm! Ku ga sadda tazo gidan nan ba ruwanta, amma daga dawowar Al’mazeen sai wani falli take ji da shi, ga shi kullum tana part ɗinsa da yana nan da baya nan, anya kuwa babu wani abunda yake gudana a tsakaninsu?”

   "Ai dama ba banza ba! kinga dai yadda Al'mazeen ke shakkarmu..."

“A’a fa Maman Hanan ba dai shakkarmu ba,yana dai kyalemu kasancewarsa mai biyayya yana shanye duk baƙinciki da takaicin da muke ƙunsa masa” Maman Beenah ta katsewa Maman Hanan hanzari ta hanyar faɗin haka.

   "To ai ga shi yanzu wannan 'yar banzar mai aikin tana shirin hanamu rawar gaban hantsi 'yan kuɗaɗen da muke karba a wajansa wannan shegiya 'yar banzan tayi ƙyam-ƙyam" Maman beenah zata kuma yin magana suka jiyo sallamarsu Sumy da Sady da karfi sai kace zasu tada gidan, kafin su Maman Hanan su sauko Azima ce ta fara sauƙowa ta fito part din Al'mazeen hannunta dauke da kaskon turaren wuta da alama saka masa tayi, wani kallo Sumy da Sady suka bi Azima da shi har ta gama saukowa tayi hanyar waje ta kofar baya ba tare da tasan Allah ya yi wasu halittu a wajan ba, Sumy ta ce

“Tooo! Ina aka samu balarabiya ko ba india?” yatsine fuska Sady tayi ta ce
“Oho” saukowarsu Maman Hanan ne ya katsewa su Sumy maganar da sukeyi, nan aka hau musu sannu da zuwa, sai amsawa sukeyi a gadarance,Sumy ce mai gajan hakuri ta ce
“Anty (maman Hanan kenan) wacece wata ‘yar dogowar yarinya fara ,tasa riga da wando da wani baƙin glass sai kace ba india?” Maman Hanan tayi tsaki tana bin Sumy da Sady da kallo ta ce
“Yoo ai ita ce wacce muke gaya muku Azima”

“Kan Uba! To ma uwarwa ta yiwa wannan shigan a gida tana mai aiki uban wa ya bata wannan damar!?” cewar Sumy, Hanan ta share hawayen da suka gaza tsayuwa dan ji take kamar hannunta zai fita ta ce
“Ba dai yanzu ku ka iso ba? To tunda Al’mazeen ya dawo take ji da iskanci iri da kala”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button