AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

“son Al’mazeen din take yi ne?” cewar Sady tana tabe baki, Beenah tace
“Kar dai har kin fara kishinsa?”
“Wa? Ni? Allah ya kyauta! Al’mazeen baya raina sam, dan haduwa ya hadu amma ni zan auresa ne dan kudinsa kamar yadda ku ka ce Anty,zamu auresa ne sabida kuɗinsa da mun kwasheshi sai ya sakemu”
“Kai kuyi magana a hankali a ƙasa fa muke, kuma wannan shegiyar tana nan, to ma yanzu kin san me ya faru?” cewar Maman Hanan, nan ta basu labarin tsiyar da Azima ke yi a gidan, ta kara da murɗewa Hanan Hannu da Aziman tayi da safe sadda Al’mazeen zaije aiki, har Hanan na nuna musu hannunta da ya kumbura, haɗa baki Sumy da Sady sukayi suna fadin zasu ci Uban Azima, suna kan meeting din yadda zasu korata a satin nan sai gata ta shigo tana shirin sake wucewa kamar dazu Sumy da ta hangeta tun farkon buɗe kofa ta ce
“Keee ƙidahumar jeji jikar shanuka! Zo nan” wani birki Azima taci ta tsaya cak ba tare da ta dawo ba, Sady ta ce
“Dake ake ballagaza!” cije baki Azima tayi idonta na sake rinewa, rintse ido tayi ta hadiye takaicinta sannan ta dawo da baya ta tako tazo gabansu ta tsaya, Sumy ta ce
“Keee! Cire wannan bakin glass din idon naki!”
"Ke a wa fa!? idan naki cirewa wata uwar zakiyi!?" Azima ta faɗa tana tinkaro Sumy, ja da baya sumy tayi, ganin haka yasa Maman Beenah faɗin
“Kee Azima! ba kya ganin baki ne? Ki dau kayansu ki haura musu da shi sama a wannan dakin da Hadiza ta gyara dazun nan”
“Su ɗin kutare ne? ko basu da hannun dauka ne? idan sun ga dama su da kayan nasu su kwana a nan” Azima na gama faɗi ta juya tana taku jikinta na langwasa harta taka step daya ta juyo ta kalli Sumy ta ce
“Kee kuma! karki kuma kuskuren fadin cewa na cire wannan madubin, dan kuwa kallo daya ake yiwa idanuna! idan kika kallesa baki kara kallon komai a rayuwarki!” Azima na fadi ta hau sama fuuuu! Aka bar su Maman Hanan a daskare.
"Ahaf kun gani da idonku ko?" cewar Maman Beenah, Sumy ta ce
“Na san yadda zanyi da shegiya bari Al’mazeen din ya dawo” ta fadi tana hawa sama, Beenah ta kira su Hadiza suka dauki kayan su Sumy suka haura musu da shi tunda Hajiya Azima Banju tace bata hawa da shi.
@@@@@
Yau kasancewar ya wuni a office yana tunanin Azima yasa bai yi wani aikin komai ba, ga shi yana son magana da ita kuma ba hali tunda ba waya ne a hannunta ba,kuma tin daga ranar da ya dawo ya fahimci babu jituwa a tsakaninta da mutanen gidan balle yace zai kira alfarma su ba shi Azima yayi magana da ita, shawaran da ya yanke shine idan ya tashi a office ya biya ya siya mata waya sai ya koya mata yadda zata dinga amfani da shi.
Bai fara aiki da wuri ba sai wajan hudu ya fara duba marasa lafiya shiyasa yau bai tashi da wuri ba sai wajan takwas da rabi, bayan ya tashi sai da ya biya ya siyawa Azima waya tukunna ya nufi gida.
A lokacin Azima na parlour hankalinta tashe tana ta aikin safa da marwa sabida ganin yau Al'mazeen bai dawo da wuri ba, tana cikin wannan zullumi ya yi sallama ya shigo, wani ajiyar zuciya ta sauke wanda bata san lokacin da ya fita ba, da sauri ta karasa gabansa tana tura baki ya ce
“Yi hakuri ‘yar fullo”
“To yau ina ka tsaya kasa duk na damu! Nifa tinda nake a rayuwata ban taba damuwa da damuwar kowa ba sai a kanka na rasa dalili! Ban taba sanin miye tunani ko damuwa ba sai a kanka, abunda na sani a rayiwa shine daukar fansa!”
"Fansa kuma!? To kiyi hakuri yau aiki ne ya min yawa a office,nima wuni nayi ina tunaninki kuma babu ta yadda zanyi magana dake shiyasa na siya miki waya da zan dawo, zancan kuma nuna damuwa a kaina ba mamaki ni ɗin na musamman ne!" gaban Azima ne ya faɗi amma da shike tana zumudin waya yasa bata bada hankalinta a kan fadin da ya yi cewa shi ɗin na musamman bane.
Wayar ya nuna mata amma yace ba zai bata ba har sai ya mata chajinsa, jakar hannunsa ta karba, ya yi gaba tana binsa a baya idonta kyam a kansa,gani take kamar akwai wani mugun haske dake fita ta ƙeyarsa tare da wani farin mutum na mata kwala
“MAGAJI BAWA!” ta faɗa tana shirin kaiwa keyar Al’mazeen duka, juyowar da yayi ne yasa tayi saurin maida hannunta, ya ce
“Mene? Waye kuma Magaji Bawa?” haɗe rai Azima tayi ta ce.
“Tsohon abokin gabana ne”
“Abokin gaba kuma?” Al’mazeen ya faɗa cike da mamaki.
“Karka fiye tambaya” ta fada tana wucewa gabansa ta rigasa hawa, duk abunda sukeyi a kan idonsu Sumy:Sady:Maman Hanan:Maman Beenah:Hanan: Sumy tace
“Muje kasa ku ga yadda zan tsara wasan nayi cilli da shegiya wajen gate a daren nan” suka sauko a tare, suna saukowa, Sumy ta ware murya tana kwalawa Azima kira sai kace gidan ke ci da wuta, a lokacin Azima na tsaye a kan Al’mazeen dake jona mata wayarta a chaji, jin kira kuma Al’mazeen ya gane murya ya ce
“Sumayya? Sun zo ne? To meyasa take kiran Azima haka?” Azima wacce zuciyarta ya tunbatsa jin yadda ake kiran sunanta abun ya bata haushi, a tare suka sauko da Al’mazeen,ya kalli Sumy ya ce
“Sumy, Sady, yaushe ku ka zo? Sannan meya faru kike kiran Azima haka?”
"E mana,mun zo dazu, da muka zo na ba wa Azima kayana ta haura min da shi sama, na zo da sarƙata ta gwal amma yanzu na duba ban gani ba, da na shiga dakin kuma na ga Azima a jikin kayana ta bude min akwati har nake tambayarta me take yi sai ce min tayi babu komai nayi hakuri, ka dai ni ba saninta nayi ba banda yau" Maman Beenah ta ce
“Anjima ana yi mana dauki ɗaɗdai, amma dai bamu taba zarginta ba, kasancewar mun yarda da ita”
“Haka ne kam, nima na nemi sarkata wanda ka siya min ɗin nan ban gani ba” cewar Hanan.
Al'mazeen a rayiwarsa ya tsani mai halin b'era dan haka ya ɗago ido yana kallon Azima wacce jikinta ke rawa idonta sun ƙanƙace sun kara rinewa, harta hannunta ya fara sab'ulewa yana zama blue, cikin wani irin murya Al'mazeen ya ce
“Azima da gaske ne? Kin dauka mata sarƙa?”
Wani ihu da gurnani Azima tayi tasa hannu ɗaya ta damƙi wuyar Sumy, nan Sumy ta hau jijjiga kai jin an shaƙe mata magudanar numfashi, cikin daga murya Azima ta ce
“Faɗi gaskiya ko yanzu ki jiki a kabari! Kikace na sace miki sarƙa! Nayi miki kama da b’arauniya! Da ku ka sakani daukar kayanku na dauka!?” duk maganar da Azima take yi tana rike da makogoron Sumy wacce ke mutsil-mutsil idonta har ya fara zazzagowa, su Maman Hanan sai dambe sukeyi da hannun Azima a kan ta saki wuyar Sumy amma sun kasa koda motsi ne da hannun Azima, harta Al’mazeen ya kasa b’anb’are Azima daga cikin Sumy, cikin in-ina da shaƙewa gami da fitar hayyaci Sumy murya irinta wa inda suka sha azaba ko suke sha ta ce
“Wallahiii…..karya……na…..ke…yi….”
????????????????
MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
(???? Macizai ne????)
MALLAKAR.
ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)
Follow me on wattpad,@Fateemah’0
????????????????????
JUMMA’@T MUBARAK????
PAID.
????️=6️⃣1️⃣↪️6️⃣2️⃣
Sakin wuyarta Azima tayi tana huci,tana sakinta Sumy ta zube kasa a sume, cikin tashin hankali suka ɗagota,Beenah wacce saukowarta kenan daga sama dan dama bata nan akayi wannan show din, Mamanta tace
“Beenah! Hanzarta dauko ruwa a fridge” ganin Sumy a baje yasa beenah kwasa da gudu taje kitchen ta dauko ruwa aka yayyafawa Sumy, da karfi ta fizgi numfashi, ganin ta saki ajiyar zuciya yasa Al’mazeen ya fizgi Azima ya wanka mata mari, wani gurnani Azima tayi tasa hannu zata shaƙi wuyar Al’mazeen da hannu biyu amma tamkar an daskarar mata da hannu ne ta kasa, cike da mugun zuciya da mugun jin haushin kanta ta yi hanyar waje, ganin haka yasa Al’mazeen dafe kai yana ambatar sunanta amma kamar ba da ita yake yi ba.
Gate ta nufa da niyyar barin gidan, dan ta ga Alkadarinta yana gaff da karyewa, kamata ya yi ace ta kashe sumy dan ita duk wanda ya tabata hukuncinsa kisa ne! haka ma Hamma Mazeen da ya mareta, amma ta kasa aiwatar da komai,to me hakan ke nufi? ai gwara ta bar gidan kafin abunda take rayuwa da shi shekara shabiyar zuwa sha shidda a rabata da shi.
Al’mazeen ne ya biyota yana kiranta amma kamar ba da ita yakeyi ba dan ta zuciya, karamin kofar gate tasa kafa tayi kwallo da shi,ga mamakin mai gadi sai ganin kofa ya yi a kasa da sauri ya tashi ya matsa ya bata waje, tana sa kafarta a waje da niyyar fita kamar wanda wutar lantarki ta kama haka taji a jikinta, ji tayi kamar an ja kafarta akayi sama da ita sannan aka wurgota cikin gidan, sai da ta yi sama tukunna ta faɗa kan wani dutse kanta ya bugu, zare ido Al’mazeen ya yi yana fadin
“Azimaaaa!” da sauri ya yi kanta yasa hannu ya dagota, harta baƙin tabarau dinta sai da ya fadi, a lokacin da Al’mazeen ya matso gareta ta rufe ido jin yadda wani mashahurin jiri dake kwasarta dan kanta ya buge sosai, cikin tashin hankali Al’mazeen ke fadin
“Subhanallahi! Azima! Azima! Azima! Dan Allah kiyi hakuri ba da nufi bane,meya sameki?” jinta shuru ba motsi yasa ya dauketa cak ya koma da ita ciki, yana shiga har yanzu ana tsaye a kan sumy wacce bata gama farfaɗowa ta dawo hayyacinta ba.