AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganinsa sukayi ya shigo da Azima a hannun sai kace baby yana shirin sa kai ya haura sama,cikin masifa Maman Hanan ta ce
“Kai Al’mazeen! Wannan wani irin rashin hankali ne! Ya zaka dauko yar aiki haka a hannunka sai kace matarka!? A gabanka fa ta shaƙe Sumayya tana shirin kasheta amma baka dakatar da ita ba, zata bar gidan ka je ka dawo da ita, ga Sumayya nan dake bukatar taimako amma baka kalleta ba ka wani dauko wannan ƙidahumar jejin matarka ce ko aurenta zakayi! bayan kasan kuma su Sumayya da Sadiyya sune matan da zaka aura ko? ko dai akwai wani abu a tsakaninka da wannan daukar kaddaran ne?” (wai Azima ce daukar kaddara) rai a haɗe Al’mazeen ya juyo ya ce
“To auranta zanyi! Ta fiye min su Sumayya da Sadiyya sau dubu! Ina sumayyan ce ta jagaleta? Ita ma Azima ta suma,ku kai sumayyar sama bari na duba Azima tukunna,zan zo na duba Sumayyan daga baya” yana gama fadi ya hau sama ya bar su shanye da baki.

   A gadonsa ya kwantar da ita yana dubata, gefen kanta ya gani ya ɗan fashe, hannu yasa da niyyar yi mata treatment ji ya yi ta riƙe hannunsa, kallonta ya yi ya ga har yanzu idonta a rintse yake, a hankali ta miƙe ba tare da ta kallesa ba tasa kai zata fita yayi saurin shan gabanta,

“Azima yi hakuri! Ki fahimceni ba da nufi na mareki ba, laifinki ne inata miki magana ki saketa amma kin ƙi ki
saurareni, taya zaki shaƙeta haka idan ta mutu me kike tunani zai faru? Ba ke kaɗai ba harta ni sai an kulleni dan anyi kisan kai a gidana! da kin kasheta sunanki fa zai koma criminal ne, kuma ba zan so hakan ta faru ba amma kiyi hakuri kinji? karki yi fushi” ya faɗa yana haɗe hannuwansa alamun roƙo,Azima kuwa juya kanta tayi gefe har yanzu taki yarda ta buɗe, yana gama magiyarsa ta rab’a ta gefensa ta fice, riƙe kai Al’mazeen ya yi yana jan ajiyar zuciya,box dinsa ya dauka ya fito yayi side din su Hanan, ya nufi dakin baki wanda su Sumayya suke zama idan suka zo, da sallama ya shiga har zuwa yanzu suna tsaye a kan Sumy, rai a haɗe fuskarsa ba annuri ya shiga, allurai ya yiwa Sumy sannan ya ɗora mata ruwa, nan da nan bacci ya kwasheta, kwashe box dinsa ya yi zai fita Maman Beenah ta ce
“Al’mazeen? Amma ina fatan batun auren yarinyar nan kawai ka faɗa ne ba da gaske kakeyi ba?”
Cak Al’mazeen ya tsaya ya juyo ya ce
“Da gaske nakeyi! Zan aureta! taya zan auri Sumayya? daga zuwanta yau ta bi Azima da sharri! Laifi biyu wanda na tsana a rayuwata! tayiwa Azima ƙarya da ƙazafin abunda bata yi ba,ƙazafin ma kuma na sata!” yana gama fadi ya fice, aka barsu da zare idanu.

 Part dinsa ya koma, yana tajin babu dadi na ganin Azima tayi fushi, shirin bacci ya yi ya kwanta dan yana tashi sallar dare.

@@@@@

   Da washe gari kamar yadda Azima ta saba haka ta shigo ta kawo masa abinci amma bayan sallama ko gaishesa taƙiyi, shi kuwa kallonta yakeyi yadda ta duƙar da kai fuska babu rahma ranta a haɗe, ganin har zai fita bata yi masa magana ba ya saka shi fadin

“Ba ki huce bane? na fa baki hakuri, ba zaki min magana ba? to ga wayarki, kalli ki ga yadda zakiyi amfani da shi” turo baki tayi tana fadin
“Bana so” sannan ta fice, Al’mazeen ya sosa kai ya ce
“Tab lallai abun babba ne, duk yadda jiya ta nuna murna da farincikinta akan wayar yanzu kuma tace bata so?” haka yasa kai ya fice, a office sai tunaninta yakeyi, Azima kuwa wuni tayi fuskarta a murtuke dan abunda ya dameta ya dameta, tunda tazo fita akayi sama-sama da ita sannan aka maidota gidan ta rasa inda zata saka kanta.

   Wasa-wasa Azima ta dauki zafi dan har aka kwashe sati daya bata magana da Al'mazeen tsakaninta da shi sai dai ta kai masa abinci ta gyara masa daki,duk kulawar da take ba shi bata daina ba magana ce dai bata masa, a sati dayan nan kuwa Al'mazeen ya yarda ya kamu da soyayyar Azima, kullum sai ya bata hakuri amma taƙi ta sauraresa dan ita kadai tasan bakincikin da take ciki.



    Ta bangaren su Aziza sun fara shirin bikin Sultana wanda zai gudana nan da sati biyu ciff, Aziza daurewa kawai takeyi tana abubuwa, amma bata da wani kuzari da karfin dafi.


 Ana saura sati daya biki duk hankalin sultana a tashe yake.

Al’mazeen ya shaidawa Nawaz a kan cewa idan ana saura kwana uku ɗaurin aure zai zo.

Ko da Sultana ta kara yiwa Khalil magana a kan tafiyarsu kano yace ta hakura kawai sun yi magana da Al’mazeen yace zai gaya musu ita ba sai taje ba,sultana ji tayi kamar ta kurma ihu dan bakinciki.

@@@@@@@

     Fitowa daga daki Aziza tayi zata hau sama da wani jiri ya ɗibeta zata fadi dai-dai lokacin da Nawaz ya sawo kai parlorn amma kafin ya iso ya tarota tuni ta fadi kasa,sunanta ya ambata ya dagota yana jijjigata a hankali yana kiran sunan Mom da sultana, da sauri suka sauko kasa suka samu Aziza kamar ta suma ne yaya ne oho

“Nawaz me ya sameta!?” mom ta tambaya hankalinta tashe, Nawaz yace
“Wlh mom ban sani ba,ina shigowa ne na ganta tana faɗuwa!” Mom ta ce
“A gaskiya Nawaz shawaran Malam Yunusa zamu bi, kawai ranar daurin auren sultana a haɗa a daura da naka da Aziza! mu tausayawa yarinyar nan halin da take ciki! Sai daurewa takeyi tana hadiyar zafin ciwo, a kananun shekarunta tayi ƙanƙanta da jurewa!” mom ta fada tana sakin kuka mai ban tausayi, Nawaz wanda shima idonsa ya canza kala ya ce
“Duk yadda kikayi dai-dai ne mom”
“Ka dauketa ka kaita daki! Sultana ke kuma ki zauna da ita, bari naje na sanar da cewa auren biyu ne” mom ta fada tana hawa sama, shi kuwa Nawaz ya dauki Aziza ya kwantar da ita a daki sannan ya fice yana neman layin Al’mazeen dan ya shaida masa har da shima za a daurawa aure.

 A cikin ƙanƙanin lokaci mom tayi sanarwan auren Nawaz da Aziza wanda mutane sun sha mamaki, amma da shike ance ba a mamaki da ikon Allah sai kowa ya bi lamarin da fatan alkairi.


 Sadda Nawaz ke gayawa Al'mazeen akan cewa zai auri Aziza ba karamin mamaki Al'mazeen ya yi ba, har yaushe Nawaz ya fara soyayya da Aziza da har ta kaisu ga maganar aure nan da sati daya? Sannan Nawaz baya son auren yarinya kamar yadda baya son auren babba sosai ,ya tabbata idan Nawaz ne zai iya cewa Aziza tayi masa yarinta, haka dai ya share maganar yana fadin shima ga shi ya kamu da son Azima,yana so ya ba wa Nawaz labarin Azima amma sai yaji kamar an riƙi bakinsa, dan haka ya share maganar gabadaya yana tambayar Nawaz dame-dame zasu shirya da bikin tunda aure yazo a bazata, nan Nawaz ke gaya masa babu wani abunda za ayi wanda ya wuce daurin aure daga shi shikenan, dan harta sultana tace babu abinda zatayi da an daura aure kawai a kaita,babu yadda khalil baiyi da ita ba ko da walima ayi nan ma tace ta yafe, ya fahimci rigima ce kawai take ji da shi amma da ta shigo hannunsa zai sauke mata shi.


    @@@@@

Da misalin karfe tara hamma mazeen ya kira Hadiza a waya yace ta kirawo masa Azima, Hadiza ta amsa da to sannan taje kiran Azima wacce yanzu dakinta daban ita daya, a lokacin tana kwance a gado ta zama macijiya, Hadiza kuwa tana zuwa ta sako kai ta tura kofa, wani burki tayi turuss! Ganin abunda ko a mafarki bata taba gani ba, shirgiɗeɗen maciji blue sai sheƙi yakeyi, wani mahaukacin ihu Hadiza ta sake tana zubewa a kasa sumammiya, da sauri Azima ta waigo nan tayi saurin komawa mutum ta yo kan Hadiza.

 Da gudu su Maman Hanan suka fito har da Al'mazeen wanda ya sauko daga part dinsa, dakin Azima suka nufa inda suka ji ihu ya fito, suna shiga suka samu Hadiza a baje Azima na tsaye a kanta, suna shigowa ta duƙar da kai kasa.

“Me kika mata!” cewar Maman Beenah hankali tashe, Sumy wacce ta jima da dawowa dai-dai ta ce
“Ba mamaki itama an shaƙeta ne! Duk yadda akayi wannan yarinya ta taba zaman prison” Al’mazeen cikin fushi ya kalli Sumy yace
“Ban ce duk wanda yake son kansa da zaman lafiya a gidan nan ba ya daina shiga hidimarta!!?” shuru sukayi ya kalli Azima ya ce
“Me kika mata?”
“Ban mata komai ba,nima daga kewaye nake naji ihu na fito da sauri sai na ganta a sume,idan kuma baku yarda ba idan ta farfaɗo ku tambayeta” Al’mazeen ya kalli Sady yace
“Kawo ruwa a yayyafa mata”
“Me?”
“Nace kawo ruwa a yayyafa mata!” ya faɗa a tsawance Sady ta fice tana yatsine fuska, ruwan ta kawo aka yayyafawa Hadiza a firgice ta farka da karatun ayatul’kursiyyu a bakinta! Nan aka hau tambayarta menene, cikin fitar hayyaci Hadiza ke fadin maciji! maciji!
“Maciji!!” Sumy Sady da Hanan da Beenah suka rungumi juna suna ihu,harta su Maman Hanan da Maman Beenah bayan Al’mazeen suka koma jikinsu na kyarma suna tambayar Hadiza ina macijin, yayinda Azima take kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta cikin gashin kanta da ta sauko dashi ya rufe mata fuska, Al’mazeen yace maciji dai a dakin nan?”
“E wlh nagani! Katon maciji! Ruwan ganye! Babba ya cike wannan gadon! Na ganshi a kan gadon nan! Wlh na gani! Maciji! Babba maciji!” duk a ruɗe Hadiza ke magana,jin abunda take fadi yasa suka maida maganar ta ta shirme ba mamaki tayi gamo ne,su sumy suka hau tsaki
“Hanan je ki kirawo Talatu ta zo ta kai Hadiza daki,kafin nan bari nayi mata alluran bacci” ya fada yana ficewa, su ma su Maman Hanan duk ficewar sukayi.

 Ba jimawa Al'mazeen ya sauko da allura a hannunsa ya zo ya yiwa Hadiza sannan ya ce Talatu ta kaita daki ta kwantar da ita,bayan sun fita Al'mazeen ya kalli Azima wacce kanta ke duƙe yace

“Zan sha shayi, za a iya haɗawa a kawo min?” ya tambayeta yana mai ƙura mata ido, gya ɗa masa kai kawai tayi sannan ya fice ita kuma ta nufi kitchen dan haɗa masa.

 Bayan su Sumy da Sady sun koma daki Sumy ke fadin

“Duk lokacin da na kalli wancan jakar yarinya ‘yar fulanin can ji nake kamar na kashe shegiya! har yanzu ban manta da kaini kofar lahira da tayi ba” Sady tace
“Mu jawo shegiya yau mu ci ubanta a dakin nan kawai” Sumy ta ce
“Haka za ayi” fitowa sukayi nan suka hangi Azima da tray a hannunta tana hawa part din Al’mazeen, Sady tace
“Kalli Matsiyaciya, mu jira ta dawo mu ja banza muci uwarta!” nan suka tsaya suna jiran saukowar Azima.

 Da sallama ta tura kofar parlorn a lokacin Al'mazeen  suna waya da Nawaz, tana ajiyewa ta tashi ta juya zata fita da sauri Al'mazeen ya ce

“Azima tsaya!”
Nawaz ya ce
“Azima? Azima kuma? Al’mazeen wace Azima?”

    ????????????????????

MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button