AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

     Aziza na tsaye a gefe da lullubi hawaye ne cike a idonta,ba dan komai ba illa su na zuwa wajan aka fara darewa ana matsawa babu wanda ya tsaya kusa da ita.

   Azima kuwa za ta zo yau ne gobe ne shuru, har aka gama tattaunawar da za ayi Azima bata zo ba.

     Bayan an fara watsewa Arɗo ya kira Baffa gefe ya ce
“Magaji? A gaskiya ba zan boye maka ba, ka binciki yaranka! Barin ma wannan yarinyar taka Azima,jiya an kawo min wani magana a kanta, bana son na tsawaita zargi dan babu kyau, sannan jikokinane kasan dai ba zan so abunda zai cutar dasu ba, amma ya kamata mu san abunyi,kasa ido sosai a kansu, bana so na kirawo Jumala dan duk abinda za a gaya mata ba yarda zatayi ba, sannan bayan sallar isha’i za a zauna ayi tattauna a faɗar mai unguwa, zamu je neman alfarma a yankin tudu” da sauri Baffa ya ce
“Arɗo yankin tudu kuma?”
“E Magaji, yankin tudu bamu da wani mafita wanda ya wuce hakan”
“To amma Arɗo kana ganin anya Sarkin Tudu zai sauraremu? Ko ka manta abunda ya shiga tsakanin yankinmu da nasu ne? Ɗansa yazo ya yi laifi a yankin nan an masa hukunci hakan ne ta haifar da gaba mai tsauri a tsakani, bana tunanin Sarkin yankin tudu zai yarda Iro Mai maganin macizai zai zo taimakonmu, kana gani duk wasu masu kama macizai da muke dasu a yankin nan sun mutu, a gaskiya inajin tsoron abunda zaije ya dawo, kar bamu gama da wani yaƙin ba mu sake kunna wani, a gaskiya bana so duk shawaran da za ayi ace za a bukaci taimakon yankin tudu da yankin ja’i”

    Nauyayyiyar ajiyar zuciya Arɗo ya sauke ya ce
“To Magaji mai zai hana kai ka maida hannun agogo baya?”
“Bangane ba Arɗo?”
“Ina nufin ka dawo yadda kake a da dan mu taimaki yankinmu, Kayan aikinka da kaje ka binne kaje ka hakosu saboda……” girgiza kai Baffa ya hau yi yana ja da baya, ya ce
“A’a Arɗo na riga da nayi alkawari ba zan sake ba, har kwanan gobe ban manta da kuskuren da na aikata bisa tsautsayi a baya ba, abun shekara ashiri amma a yanzu gani nake yi yanzu abun ya faru, Arɗo ba a son raina na kashe BANJU ba, na kashesa ne sabida shafe mutanen yankin nan da ya fara, sannan idan baka manta ba yace zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan! tunda na kashe Banju nayi alkawari na dai na! duk wani abu wanda na gada daga gareka da kakanni! Dan Allah Arɗo a bar wannan maganar”

   ????????????????????

WLH IDAN NAYI POSTING A GRP BAN CIKA BI TA CIKIN GRP DIN BA,AKWAI WASU GRP DIN MA BANA BUDEWA INDAI BA GOGE SAKONNI ZANYI BA, IDAN KINA SON BIYAN KUDIN BOOK DIN NAN KI TUNTUBENI TA LAMBAR WAYATA TA SAMA, IDAN TA ACCT NE KO KATI.

AND PLS&PLS 4 ALLAH’S SAKE, IDAN KIN SAN BA BIYA ZAKIYI BA KARKI KIRANI KI GAYA MIN MAGANAR DA BA HAKA BA, A BOOK DIN NAN DAI BAN CE DARI BIYAR  KO DARI UKU BA,HAR TA DARI BIYU MA BANCE BA, DARI NE NACE DAN MASOYANA,BAN SAKA TA INDA BA ZAKI IYA BIYA BA, SO PLSS A DINGA FAHIMTA,DAN WATA MAGANA JIYA BAI MIN DADI BA SAM.????????
   

MASU KIRA NA DAN KARA MIN ƘWARIN GUIWA NA GODE,NA SAN ZAKU GANI DIK DA BAN SANKU BA AMMA KUNA RAINA????????????

COMMENTS AN SHARE

BY MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

JINJINA GAREKI UWA BA DA MAMA, ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA, SHUGABA DAYA TAMKAR DA DUBU,(GWAGGOTA TA KAINA ALLAH YA IYA MIKI.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

   ????????????????????

JINJINA GAREKI HAJIYA MAMAN YUSUF MAI KAYAN MATA???? SAFIYAR YAU KECE KIKA FARA SAKANI DARIYA???? DAN HAKA GA KYAUTAR PAGE HAJIYA JIRGIN DANƘARO????

MAMIE’S CLUB HAKIKA SHARHINKU YA TAFI DA RUHINA, A KODAYAUSHE KUNA NUNA MIN E KU ƊIN YAN AMANA NE NA GASKEN-GASKE, AZIMA DA AZIZA FANS GRP, WLH KARKU YARDA A ZO GARINKU A FI KU RAWA AHA TO????, DAN ARADU YAN MAMIE’S SUN CE BA ZAKU KAMO SU A SHARHI BA,KUMA NA YABA????????, A KAFTA????????‍♀️

ALHAMDULILLAH! ALLAH NA GODE MAKA, YA ALLAH KA KARAWA SHUGABA JA GABA ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM DARAJA! DA IYALAN GIDANSA DA SAHABBANSA DA MAGOYA BAYA HAR IZUWA RANAR SAKAMAKO! HAKIKA AZIMA DA AZIZA YA YI FARIN JINI FIYE DA TUNANINA! ALHAMDULILLAH! MASOYA A CI GABA DA NUNA MIN ƘAUNA TA HANYAR SIYAN BOOK DIN NAN CIKIN FARASHI MAI RAHUSA, ƊARI KACAL????????

FREE..
????️==9️⃣↪️????

Dambe suke yi sosai a tsakaninsu ba ji ba gani, yayinda Azima ta yanki Aziza a gefen wuya,nan ta koma mutun ta faɗi kasa, ita ma Azimar rabi mutum rabi Macijiya ta zama tana kallon Aziza ranta a haɗe idonta ya kara rinewa zuwa blue, a hankali Aziza ta miƙe tsaye tasa hannu ta karkaɗe jikinta ta juya baya,ta sa hannu a gefen wuyanta inda yake zubar da jini ta lumshe ido, kamar ƙiftawar ido da bismillah ta shafe wajan, sannan ta daga hannunta sama ta haɗa wani guguwa mai karfin gaske ta turawa Azima, Azima bata ankara ba taji anyi sama-sama da ita, sai da taje can sama kafin ta faɗo timm! Da kasa nan ta koma mutum, a hankali Aziza ta juyo tana kallonta yau fuskarta babu fara’a, haqiqa dan faɗa su na faɗa amma basu taba dambe ba, bar su a cacan baki.

    Saurin tashi Azima ta yi ta sake komawa macijiya ta yi hajijiya ta tada ƙura ta yi kan Aziza, da sauri Aziza ita ma ta sake zama macijiya suka haɗe aka hau dambe, da jelarta na maciji ta nannaɗe wuyar Azima ta shaƙeta sosai, murkususu Azima ta hau yi tana son kwacewa daga hannun Aziza amma ta kasa, inda karfinta ya fara karewa dan duk muguntarta bata kai Aziza karfin dafi ba.

    Nan numfashinta ya fara yin sama inda a karshen jikinta ya sub’ale ta koma mutum sumammiya, ganin haka yasa Aziza sakinta ta wullata kusa da rafin ita ma ta koma mutum sannan tasa hannu ta dibo ruwa ta watsa mata a fuska, wani wawan ajiyar zuciya Azima ta sauke alaman ta sha wuya, da tari ta farka tana yunkurin tashi ta ce
“Duk abun da zakiyi Aziza kema kin sani ba zaki iya kasheni ba!”

  
   
   Kafadarta Aziza ta kama hawaye cike a idonta ta ce
“Nima bana fatar kasheki! Har na bar duniya bana fata na kashe ko da tururuwa! Azima kisan ya yi yawa! Azima me kikeson zama ne! Ga shi yau kin sani na aikata abunda bana son aikatawa wanda ban ma taba aikatawa ba! meyasa Azima! Me yasa! Me yasa!” Aziza ta karasa tana sakin kuka mai cike da ruɗani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button