AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kai wannan yarinya bata da kunya! Waike bakinki baya shuru ne zan fasa kanki da bindiga fa!” cewar wani daga cikin b’arayin, ogansu yace ku kyaleta mun san irinsu ai, bari mu karbi abunda ya kawo mu daga nan mu rabata da baki har abada muyi mata fyaɗe muyi gaba, wani kallo Azima ta musu tana shirin magana taga an fito da Al’mazeen ana jansa, ranta ne ya b’aci ganin yadda suke fizgar shi kamar kaza.

Gaban ogan aka kawosa ya dago ido yaga ahalin gidansa a zube a kasa an kewayesu da bindiga Azima kuma ana riƙe da ita.

“Dan Allah karku yiwa kowa komai plss” Al’mazeen ya faɗa hankalinsa a tashe

Wani dariyar mugunta ogansu ya sake ya ce
“Abunda ya kawo mu ba mai tsanani bane Kuɗaɗe kawai zaka bamu sannan mu yiwa wannan yarinyar fyaɗe mu kama gabanmu” zare ido Al’mazeen ya yi jin sunce zasu yiwa Azima fyaɗe hakuri ya hau basu amma da shike zuciyarsu ta riga da ta bushe da rashin imani sukace babu abunda ya damesu, Al’mazeen yace
Su fadi kudin da zai fanshi Azima,nan suka masa wani zunzurutun kudi wanda idan ya basu ya kwashe kudin acct dinsa kaff kai har ma da gidan da suke ciki a yanzu, zufa ce ta hau wankewa Al’mazeen jiki yace musu baya da wa innan kuɗaɗen a gida, sannan kudinsa na acct bai kai wannan ba sukace karya yake yi,idan babu kudin a gida to ya musu transfer (kai b’arawo da karfin hali yake wlh).

“Ko da yana da shi ba zai bayar ba!” Azima ta faɗa jikinta na rawa sabida bakinciki izuwa yanzu yaci ace kaff ta sare b’ayin nan amma fitowar Al’mazeen ya dakatar mata da komai.

“Ai kuwa idan bai bayar ba lahira zatayi baƙo, ke kuma zamu yaga-yaga dake! idan kuma kinci musu ya kuma fadin cewa ba shi da kudin da muka tambaya ya gani, dan ko biyar ba zamu rage ba” shuru Al’mazeen ya yi zuwa can suka ce yana bata musu lokaci akwai gidan da zasuje
Almazeen yace
“Wlh kudina na acct bai kai haka ba,kuyi hakuri na baku kuɗin duka amma bai kai yadda kuke bukata ba”

“Amma lallai ka raina mana hankali, a wannan babban gidan naka zakace baka da kudin da muka tambaya ashe kuwa baka son rayiwarka da ta wannan yarinyar!”

"Ku kashesa!" ogan b'arayin ya faɗa, daga Al'mazeen akayi aka saita masa bindiga ganin haka yasa da sauri Azima ta rintse ido hannunta ya kama da wuta ta ciki, saurin saketa wanda suka riketa sukayi sakamakon wani bala'in zafi a tafin hannunsu, rintse ido Al'mazeen yayi yana kalman shahada, ji yayi karan an saki kunnamar bindiga, kafin bullet din ya shigo jikinsa Azima ce ta fara shigewa jikinsa bullet din ya shigeta a baya, saurin buɗe ido Mazeen ya yi ga Azima a jikinsa da Alama bullet din jikinta ya shiga! 

“Azimaaaaa!!” Mazeen ya faɗi hankalinsa tashe da sauri tasa hannu ta shafi fuskarsa nan ya kafe, sannan ta juya ta watsawa su Maman Hanan wani baƙin hayaki nan suma suka kafe sannan ta juyo tana kwashe gashin fuskarta ta nannaɗe ta waro blue eye dinta, dan idan bata ci ubansu ba hankalinta ba zai kwanta ba,bakinciki zai iya sawa ma ta sari kanta ta mutu.

Su kuwa b’arayi tsayuwa kallon bala’i da ikon Allah suka yi, wani gurnani Azima tayi ta juya nan ta zama macijiya.

Karyan iskanci nan suka saka ihu, ta ce
“Kamar yadda baku da imani haka nima ban da shi, nawa kam har ya fi naku! RUWA BIYU! AZIMA! AZIMA BANJU MACIJIYA! NI MACIJIYA CE!” tana faɗi ta hau binsu da sara, sai da ta saresu kaff sannan ta naɗesu kaff dinsu da jelarta ta sulale ta jasu suka bar gidan, b’acewa tayi ta kaisu jeji ta watsar dasu sannan ta koma gidan, nan ta samu mai gadi a sume an harbesa a kafa shima,bata yi ta kansa ba ta koma ciki ta samu har yanzu suna nan a daskare hannu tasa ta shafe jinin dake wajan tass sannan ta watsawa su Maman Hanan wani bakin hayakin nan ta sakesu, Al’mazeen kuwa kara shigewa jikinsa tayi ta shafo fuskarsa nan shima abun ya sakesa a firgici ya riƙo Azima wacce ke sulalewa a jikinsa yayi saurin haɗeta da kirjinsa yana ambatar sunanta, dago kai yayi bai ga kowa ba yaga wayam
To meya samesa sai kace wanda komai na jikinsa ya tsaya na wucin gadi.

Su Maman Hanan kuwa masu fitsari a jiki da masu kashi duk sunyi, Hadiza kuwa cewa tayi wlh yau gidansu zata tafi dan daren nan babu abunda ta gani sai bala’i ido da ido, Al’mazeen na daukar Azima suka fito gabadaya nan ya iske mai gadi a kwance shima da harbi a kafa, kwashesu yayi duk ya kaisu asibiti a lokacin da ya fito ana kiran sallan assalatu.

  Bayan sun isa asibitinsa duk yan gidan aka hau basu taimakon gaggawa shi kuwa ya wuce cikin emergency da Azima, shi da kansa ya hau mata aikin cire mata bullet din da ya shiga bayanta,duk abunda yakeyi tanajinsa sarai har ya gama yi mata komai, allura ya dauko zai mata tayi saurin riƙe hannunsa tana girgiza masa kai, da sauri ya hau kiran sunanta,murya can kasa tace

“Hamma karka a yi mini allura zai cutar dani, jikina bana allura bane karka mini dan Allah” hawaye Al’mazeen ya goge yana gya ɗa kai alaman ba zai mata ba, duba agogo ya yi ya ga bakwai dan haka ya wuce masallaci dake cikin asibitin ya yi sallah sannan ya koma ya duba lafiyar kowa ya ga kowa lafiya harta mai gadi an cire masa bullet yana zaune, sai a lokacin yaji ya samu natsuwa ya kira jami’an tsaro ya shaida musu duk abunda ya faru, bayan ya gama musu bayani ya tuno da ashe ya bar wayarsa a gida dan da wayar asibiti ya kira jami’an tsaron kasancewar akwai wa inda ya sani a ciki, wayar wata nurse ya karba ya saka lambar Nawaz ya hau kira, sai da ya masa kira uku kafin nawaz ya daga Al’mazeen ya ce
“Dude ni ne”
“Kai Dude jiya muna magana kace zaka kirani baka kirani ba ni kuwa nata kiranka baka daga ba,ina fata dai komai lafiya?”
“E to da sauki dai” nan Al’mazeen ya ba wa Nawaz labarin abunda ya faru, hankali tashe Nawaz yace gashi nan tahowa Kano, Al’mazeen ya ce
“Noo! Wlh karka zo don’t worry we are safe now alhamdulillah! and Karka gayawa Mom am sure hankalinta zai tashi but still zan taho jibin In sha Allah dan na saka jami’an tsaro a lamarin,pls karka damu ina lafiya”
“Pls take care of urself” daga haka sukayi sallama.

  Sai wajan karfe hudu kafin suka gama watsatstsakewa sannan suka ɗunguma sukayi gida har lokacin yan sanda suna zagaye da gidan,nan maƙota aka hau yiwa su Al'mazeen jaje ana yin Allah ya kiyaye gaba, nan police suka ba wa Al'mazeen rahoton sun san b'arayin sun jima suna aikata b'arna amma yanzu sun nemesu sun rasa amma zasu ci gaba zurfafa bincike, godiya Mazeen ya musu sannan yace yana da bukatar matakan tsaro a gidansa, nan D.P.O. ya shaida masa babu komai, sannan ya kamo Azima wacce ke zaune a mota ya fito da ita suka shiga ciki, dakinta ya kaita ya kwantar da ita ya kalleta yace

“Meyasa kika tare min harbi?”
“Nima ban san meyasa nayi hakan ba, amma naji a jikina ba zan iya bari a harbeka ka mutu ba” shuru Mazeen ya yi sannan ya tashi ya fita.

  Sai dare tukunna su Maman Hanan da Maman beenah suka hau neman su Sumy da Sady, ko da aka kira wayarsu cewa sukayi sun jima a katsina, nan aka basu labarin abunda ya faru Sady tace

Ashe da rabon ba zamu ga masifa biyu ba,munga daya kun ga daya,maganar auren Almazeen kuwa sun yafe Allah zai bamu wani kar muzo mu bamuci kudi ba mu mutu a banza sai anjima anty suka kashe wayarsu.

    Bayan kwana biyu Azima ta warware sai shirin tafiya kaduna akeyi gobe, har yanzu kuma ba a samu wani rahoto ba dangane da b'arayin, su Almazeen zasu tafi gobe shida Azima, su Hajiya Lawiza kuma sai ana gobe daurin aure zasu je.



   Da washe gari kamar yadda Mazeen ya cewa Azima ta shirya akan lokaci hakan ce kuwa ta kasance karfe takwas suka kama hanyar kaduna, gaban Azima sai bugawa yakeyi.


Itama Aziza yau da bugun zuciya ta farka dan bata san da maganar aurenta da Nawaz ba duk wannan hidima sai a daren jiya, tun tara suka tafi gidan gyaran jiki da lalle dan idan basuyi yau ba gobe Sultana tace ba fita zatayi ba,kuma mom tace dole ayi walima a goben tunda jibi ne daurin aure jumma'a kenan.



     Goma da rabi Al'mazeen suka iso, a lokacin gidan ya fara cika da mutane yan biki, yana shiga ciki ya yi parking din motarsa bugun zuciyar Azima ya tsananta,kallonta ya yi ya ce

“Menene?” girgiza masa kai tayi alaman babu komai
“To fito” suna fitowa Nawaz shima na fitowa daga part dinsa zai shiga wajan mom ta kirasa ya hangi amininsa, da sauri yazo suka rungumi juna ya kara yi masa jaje, bai ma lura da Azima dake maqale kanta na mugun juyawa ba ga jiri ga zufa, har sun fara tafiya Al’mazeen ya waigo ya ce
“Azima?” da sauri Nawaz ya juyo ya kalleta tana sanye da black shadow a idonta, fuskar a bude amma tayi rolling din veil mai rufe rabin fuska,ƙura mata ido Nawaz yayi, ya kalli Al’mazeen yace
“Who is she?”
“I will tell u later, now let’s go inside, Azima muje ko?” jinjina kai tayi tana gaishe da Nawaz ya amsa ba yabo ba fallasa suka shiga, suna shiga aka hau yiwa Nawaz tsiya ango ango aure ba shiri a lokaci guda mun zata sai mun buga mata gangan gauro ashe yanzu kuwa wa Almazeenu zamu buga mawa, cewar tsofaffi, su dai dariya sukayi suna hawa sama Azima na kan binsu a baya, dakin mom suka shiga da sallama mom ta amsa tana yiwa Almazeen oyoyo gaisheta yayi ta amsa cikin kulawa tana fadin
“Ka ga ikon Allah ko? Abokinka zaiyi aure ,da ina shirin takura muku ashe Allah ya riga da yayi ikonsa, yanzu ma kai zan takura ma wa, naso ace a tare zakuyi aure wlh!”

“Mom ba komai ai,komai lokaci ne nima ranata tana zuwa in sha Allah”

“Amma dai ba da wannan Alishan ba ko?” Nawaz ya fada yana hararan Mazeen
“To wai ina ruwanka?mom ki masa magana”
“E kuma gaskiya ne ina ruwanka kai zaka zauna masa da ita ne” mom ta fada tana daga kai ta kalli Azima dake tsaye a bakin kofa kanta a duke jikinta na rawa
“Wacece kuma?”
“Amm umm e mom tare muka zo da ita, inasu Sultana?”

“Ayya sannu da zuwa ɗiyata” Mom ta fada tana kurawa Azima ido ganin wani sirhitaccen kamanni da takeyi da Aziza, duƙawa har kasa Azima tayi ta ce
“Ina kwana mom? Mun sameku lafiya?” hakan da tayi ba karamin dadi Almazeen yaji ba, Mom ji tayi muryan ma irin na Aziza amma sai dai Aziza ta fita sanyin murya sosai,
“Alhamdulillah! Ga shi kin zo su Sultana sun tafi gidan lalle da gyaran jiki, amma zo na nuna miki dakin sultana sai ki zauna ki jira su, ko kina so a kaiki gidan lallen kema a miki?”
“A’a ban taba yi ba ma a rayuwata, zan jira su ɗin kawai” mom tayi murmushi ta kama hannun Azima caraf idonta ya sauka akan zoben hannun Azima iri daya sak da na Aziza,kuma Aziza tace sadda aka haifesu kakansu Arɗo shi ya ba wa Hajjarsu ta saka mu shi a hannu, daurewa Mom tayi ta ce ya sunanki?
“AZIMA!”
“Ma sha Allah Azima suna mai dadi, Azima wa?”
“AZIMA BANJU!!” ba iyakar Mom ba harta Nawaz wanda yake kokonta sai da ya waigo a firgice, da kyar Mom ta iya riƙe kanta tana murmushin yaƙe ta rungumo Azima ta kaita dakin sultana sannan ta koma daki ta samu Almazeen na tambayar Nawaz meke damunsa, Mom Na shigowa Nawaz ya mike yana fadin
“Wlh ita ce mom, yar uwar Aziza ce, Allah Alhamdulillahi³!” Mom da Nawaz suke faɗi, Al’mazeen da kansa ya shiga duhu yace
“Dan Allah Mom ku min bayani ku fiddani a duhu, dama Aziza tana da yar uwa ne?” mom tace
“Dole zamu maka bayani amma kafin nan a ina kasan Azima ina ka sameta?” bai boye musu ba aiki takeyi agidansa a cam ma ya sameta dan tun bayanan su Maman Hanan suka gaya masa an dauke sabuwar mai aiki, har izuwa sadda ya dawo da shakuwar da ta shiga tsakaninsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button