AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

 "ALLAH KENAN MAI YIN YADDA YA SO, HAKURINKA BAYA FADI KASA BANZA! ALLAH YA TAKAITA MANA WAHALA" cewar Mom tana jinjina kai, zama sukayi nan Mom ta hau warwarewa Al'mazeen komai bata kara ba bata rage ba, Al'mazeen ya zare ido yace

“Kenan mom AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE? SANNAN YAN BIYU NE? mom ta gya ɗa kai,
“Kenan Azima ba Azima bace Banju ne?” mom ta ƙara jinjina kai
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!” mom ta kara da cewa
“Wannan shine dalilin da yasa auren Nawaz da Aziza ya tashi babu shiri dan yin jahadi ya taimaki Aziza” jinjina kai Al’mazeen yayi ya ce
“Idan har Aminina zaiyi wannan aikin ladan ba tare da ya faɗa soyayya ba ina ga ni da na fara son Azima? Sannan ta taimakeni da badin sanadinta ba da yanzu b’arayi sun kasheni!” nan ya bai wa mom labari mom ta hau salati tana sanar da ubangiji, sannan ya kara da cewa
“Ta taimakeni! Ta ceci rayuwata yayinda ta saka nata a hatsari! mom ina son Azima! Ina so kuma jibi nima a ɗaura min aure da ita amma karta sani, kamar yadda Banju shaiɗanin aljani ne zai iya kashemu idan har yasan da hakan, sannan ya kamata a gayawa Aziza kar ta dawo gidan nan dan karsu haɗu da Azima har sai bayan an daura aure” Mom tace
“Hakan ma wata shawara ce mai kyau,idan yaso aka daura auren da washe gari ranar sai mu shirya tafiya yola,ko kuma da an daura kawai mu wuce tinda Aziza tace cikin daci suke, sai ku shirya mota mai ƙarƙo da zai iya kaimu zamu tafi da Malam Yunusa da ƙanin mahaifinku da kuma Hajiya Lawiza ko kuma Hajiya luba”
“E hakan ma yayi mom” cewar nawaz, na suka gama tsara abunda zasuyi.

   An gama yiwa Aziza lalle tana zaune,ita kuwa Sultana ana wanke mata nata, gajiya da zaman Aziza tayi ta ɗan jinginu tana lumshe ido, tana lumshe ido wa zata gani? Azima ta hanga wani ajiyar zuciya ta sauke da jan numfashi ta buɗe ido tace

AZIMAA!?” sultana tace
“Azima kuma? Ina kika ganta?”
“Wlh na ganta Anty Sulty ina rintse ido na ganta,ina zuwa bari na sake dubawa” rintse ido tayi ta shafo tafin hannunta nan ta hangi Azima kwance a gadon sultana, a hankali ta buɗe ido tace
“Azima a gida kuma a dakinki a gadonki?” sultana zatayi magana wayarta ya yi kara, tana dubawa ta ga mom saurin dauka tayi tasa a kunne tayi sallama mom tace saurareni da kyau Sultana” nan mom tayiwa sultana bayanin komai sannan tace
Idan sun gama su biya gidan kawarta Hajiya Biba su ajiye Aziza sannan su su dawo, yanzu sultana ki yiwa Aziza bayanin komai yadda na miki, mom na gama fadi ta ajiye waya,sultana ido bude ta kai bakinta saitin kunnen Aziza tayi mata bayani dalla-dalla,itama Azizan ido a waje ta kalli Sultana, sultana ta jinjina mata kai.

 Basu gama ba sai gaf magriba dan haka ko da suka tashi suka biya suka ajiye Aziza a gidan Hajiya Biba su kuma suka wuce gida.


Ko da suka isa Sultana bata nunawa Azima komai ba tayi maraba da ita ta hau janta a jiki.


Nan sanarwan aure ya koma na mutum uku.

Da washe gari walima Mom ta ba wa Azima haɗaddiyar dogon riga wanda yasha stone, a jiya ne ma da dare tasa aka nemo mata kasancewar ba ayi shiri da ita ba, bata tayi ta saka Azima ta karba ta mata godiya, kasancewar a gidan za ayi walimar a tare kusa da juna Mom ta zaunar da sultana da Azima,itama Aziza ana can anayin nata a gidan kawar mom, sadda aka fara wa’azi dodon kunnenta kamar zai tarwatse ji take har fatarta ƙuna yakeyi dan da karfi Malama Rasheedat Hassan Usman ke fadin Allah yace Annabi Yace.

Duk wanda yazo ya tambaya wannan itace amaryan Nawaz din sai mom tace a'a ta Al'mazeen ce, lokacin dasu Maman Hanan suka iso kamar su mutu da bakin ciki dan tun a jiya labari ya iskesu nan suka dinga tsinewa Almazeen da Azima, har suna cewa dama ya sane ya ƙi fada musu zaiyi aure.


Anyi walima lafiya aka watse lafiya.


 Da washe gari karfe sha ɗaya za a daura aure kasancewar su Nawaz zasu kama hanyar yola ne da an daura aure.


 Tun wayewar gari Azima ta kasa zama ta kasa tsayuwa ta rasa dalili, a gidan Hajiya Biba kuwa itama Aziza ta matsu suyi ido huɗu da Azima.


   Ma sha Allah sha ɗaya nayi dai-dai aka shaida daurin auren Khalil Alhaji Yaro da Amaryarsa Sultana Alhaji Sardauna, sai kuma na NAWAZ ALHAJI SARDAUNA DA AMARYARSA AZIZA MAGAJI BAWA, SANNAN AKA DAURA NA AL'MAZEEN ALHAJI SAHABI DA AMARYARSA AZIMA MAGAJI BAWA! ana daura aure Azima na zaune a daki da su Sultana da kawayen sultana nan ta riƙe kirjinta ta hau tari, ana gama daura aure Nawaz da Al'mazeen da wasu abokai sukayi gidan Hajiya Biba dan dauko Aziza, da lullubi aka fito da ita kanta na juyawa kasancewar mahaɗi daya suke da Azima wacce take mayuwacin hali a gida su Sultana sun rufo a kanta.


 Da kyar Aziza ke fizgar numfashi ta gaida su Al'mazeen suka amsa ,hankalin Nawaz na kanta yana lura da halin da take ciki.

Suna isowa gida guɗa ya hau tashi ana ga angwaye ga angwaye, Mom tace su hauro sama, Aziza ta taka step jiri ya kwasheta zata fadi da sauri Nawaz ya tallabota nan jama’a aka sa ihu ana musu tafi, shi dai matarsa kawai ya kama suka hau sama, hannun kofar Aziza ta murɗa fuskarta a murtuke, tana tura kofar a lokacin Azima na duƙe sultana na bubbuga bayanta.

“AZIMA!” Aziza ta kira sunanta murya a daskare, wani wawan dagowa Azima tayi caraf idonta ya sauka cikin na Aziza wacce Nawaz ke rike da kafaɗunta.

  ????????????????

MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

WA INDA BASU BIYA BA SUN BIBIYI PAGES BA, CMLPT DCMNT #300 NE, NOR #100.

PAID.
????️=6️⃣7️⃣↪️6️⃣8️⃣

Murtuƙe fuska Banju ya yi ya ce
“Magaji! ba dawowa nayi ba”
“Na sani Banju! ba dawowa kayi ba,jarumar ‘yata ce ta dawo da kai”
“Kaii Magaji! Kunceni! Idan ba haka ba yankin kwana ta koma toka! Dan kasan wanene Banju! Bana da imani! Kasan karonmu da kai!” murmushi Baffa yayi yace
“Amma ni Magaji Bawa! ban gudu ba hakane Banju?” haɗe rai Banju yayi baffa ya ci gaba da fadin
“A yanzu ko Magajiyata Aziza tsaf zan iya sakata kasheka! amma halin da ka sakani yasa nake son kasheka da hannuna! ka fara ƙirga numfashinka daga yanzu zuwa gobe” dariya Banju ya yi yace
“Ashe kuwa idan zaka kasheni zaka haɗa da ‘yarka, karka manta gangar jiki daya muke da ita” Baffa shima murmushi ya yi ya ce
“Duk makahon da kaji yace ayi wasan jifa yasan ya taka dutse bare mai ido kuma kai ma kasan bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane, a wannan tafiyar kaine makahon inaji ka manta da cewa yanzu haka Azima na da aure ko? mijinta shine zai fiddaka daga jikinta ni kuma na kawo karshenka ta yadda ba zaka kuma dawowa ba, kisan farko da na kasheka ban so ba, amma a yanzu ne zan kau da ka” wani ihu Banju ya yi yana son tsincewa, Baffa yace
“Aziza!” juyowa tayi ta kalli Baffa, Baffa ya mata alama da ido, ta gya ɗa masa kai sannan tayi gaban Banju tana shirin sake kafar da shi, da karfi ya furta mata “BAHULAAAAA!!” a kunne yana son tada Bahula dake jikin Aziza, wani ja da baya Aziza tayi ta dafe saitin zuciyarta da kanta, ganin haka yasa Baffa jan Aziza da sauri ya watsa mata wani farin hoda nan Aziza ta sulale zata faɗi Nawaz bai yi kasa a guiwa ba ya tare matarsa, da yatsa daya Baffa ya do ki goshin Banju, kamar anyi ruwa an dauke haka Banju ya tsaya cak, Mom cikin tashin hankali ta kama hannun Aziza wacce take kwance a jikin Nawaz ta ce
“Dan Allah Baban Aziza kayi wani abu, Aziza ta sha wuya wlh! Duk wani masifa kanta yake afkawa dan Allah tunda ga Azima a cire mata Banju ko Aziza ta huta, me yasa baka kashesa yanzu ba?” cikin kunya Baffa yace sabida har yanzu yana jikin Azima, idan na kashe Banju a yanzu Azima ma ta tafi!” nan Mom ta gane abunda Baffa ke nufi, ta kalli Hajja wacce ke tsaye a gefe tayi lullubi tana duƙe da kai, Mom ta ce
“Nawaz shiga da Aziza cikin gida, Maman Aziza? Dan Allah ki daina ɗaurewa kina wannan kunyar taki, ki saki jiki ki rungumi yarki, an wuce wannan zamanin kunyar, yarki ce fa? Karki cutar da kanki kina son jin dumin yarki amma ki ta rabewa, dan Allah bana son haka, ai gwara ki ja ta a jiki kafin na dauketa” rasssss!! gaban Hajja ya faɗi jin mom tace zata dauke Aziza, amma bata iya furta ko da uhum bane tabi bayan Nawaz da ya shige da Aziza, mom ta ce
“Baban Aziza zamu yi magana” Baffa ya ce
“To madalla bismillah” gefe suka koma suka kebe, mom ta ce
“A ba wa Almazeen matarsa yau suyi mu’amala ta aure dan a kawo karshen wannan masifan, karka ce zaka biyewa kunya, wajan ceton rai babu zan can kunya, a nema masa inda za a kai masa matarsa, a gobe ka kashe Banju,idan kuma hakan ba zai yu ba to a bamu su mu koma birni idan yaso komai ya daidaita a can Banjun ya fita sai a kashesa a can birni sai mu tafi tare da ku, amma ya ka ce?”girgiza kai Baffa ya yi cikin sauri ya ce
“Maganar a bar yankin nan a shiga gari akwai matsala, ba zan boye miki ba, Almazeenu zai fuskanci kalubale wajan kusantar Azima, Banju ya wuce duk tunaninki , kuma bayan ya kusanceta zaiyi ciwo, ba lallai bane ku a cikin gari kuna da maganguna irin tamu ta gargajiya, ga misali a kan Aziza haka tayi ta faman ciwo sai da ku ka zo kafin ta samu furen huriri ta warke, a nan aka fara yaƙin a nan kuma nake so a ƙarasata,bana so a kai muku masifa kuna zaman lafiya, burin Banju kenan ya sake barin yankin nan,ni kuwa ba zan bar haka ta faru ba ta yardan Allah, dazu bayan munyi sallar asuba maganar da Baffa Mandi da Arɗo suka min kenan a ba wa Almazeenu Azima yau, akwai wani gida da Arɗo yasa aka zagaye a can kusa da wajan gari, amma akwai tsirarakun fulani a wajan kawai dai gidan ne shi daya, yanzu haka zamu tafi da shi Almazeenu din, kafin nan zan ba shi wasu magunguna da rubutu su sha shi da Nawazu din, dan shi ma yana da bukatar haka tunda miji ne ga Aziza” Mom ta ce
“To ba damuwa hakan ma yayi Allah ya iya mana” Baffa ya amsa da amin, mom ta kira Nawaz da Almazeen tace musu su bi Baffa, Malam Yunusa kuma da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami suna tare dasu sarki chubado da mai unguwa ori sai hira sukeyi ana shan damemmen fura da nono, gwanin sha’awa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button