AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????
Basu suka farka ba sai lokacin sallar azahar, wani ɗauuuu!! Aziza taji a kunnenta da ta farka, zata fadi da saurin Nawaz ya riƙeta, wanda shima yanzu baya jin komai ciwon jikin nasa ya tafi
“Kina lafiya?” Aziza ta gya ɗa kai tana gyara tsayuwarta, zuwa can ta ce
“Azima? yar uwata?” ta faɗa zata fice da sauri Nawaz ya rikota yace suyi sallah kafin su tafi, sallan kuwa suka gabatar shi ya jasu sannan suka fita sukayi gidan da Almzeen da Azima suke, mom ma tana gidan tana kula da Almazeen wanda a zaune ma ya ƙara gabatar da sallah, Azima kuwa tunda ta farka har tayi sallah karo na farko a rayuwarta, bata furta ko da uffan bane kallo kawai take bin mutane da shi abubuwa suna dawo mata kamar a mafarki haka take tariyowa, tana zaune a kan sallayar kaba su Nawaz da Aziza suka shigo da sallama, Aziza tana ganin Azima a kan sallaya tasa kukan farinciki tana fadin
“Azima?” daidai lokacin su Inna wuro da su Yawuro har ma da Hajja dasu Baffa suka shigo, juyowa Azima tayi tana binsu da kallo, ganin Aziza yasa ta ce
“Aziza?” wani kuka Aziza tasa ta ƙaraso da sauri suka rungume juna ƙaƙam
“Me ya faru Aziza?” Azima ta tambaya cikin sheshsheƙar kuka
” zan gaya miki” cewar Arɗo, nan ya hau yiwa Azima bayani dalla-dalla tun fara kisa da yaƙi da komai da barin yankin kwana har izuwa yanzu, wani kwalalo idanu waje Azima tayi ta hau girgiza kai tana fadin
“Ni….ni….ni….ban…..ban….ban…kashe….kowa….ba…..Baffa…….bana….da niyyar kasheka…Hajja ban miki rashin kunya ba…..Aziza…banyi faɗa dake ba…..dan Allah kuyi hakuri….. Ban kashe kowa….ba…” duk Azima ta bi ta ruɗe mom ta jata a jiki ta ringume tace
“Mun sani Azima,mun san cewa jinin Magaji da Jamila ba zata aikata hakan ba, kwantar da hankalinki, ba ki kashe kowa ba,mugun nan azzalumin aljani Banju shine ya kashe” ɗago daga jikin mom tayi tana kan ci gaba da kuka, duk da zafi da ciwo da ƙasanta ke mata ba shi ya hanata tashi da gudu ta shige jikin hajja da kuka ba, itama Hajja kukan takeyi, dagowa tayi ta kalli Baffa ta hau girgiza kai da hannu tana fadin.
????????????????
GARKUWAN MACIZAI????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
(???? Macizai ne????)
MALLAKAR.
ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)
Follow me on wattpad,@Fateemah’0
????????????????????
PAID.
????️=6️⃣5️⃣↪️6️⃣6️⃣
“Aziza?” Azima ta kira sunanta itama murya a sarƙaƙe, Nawaz ne yace kawayen Sultana su fita, da sauri kuwa suka fice,suna fita Al’mazeen ya sawa kofar key, wani kallo Azima ke bin Aziza da shi har ma dasu Mom, Mom ce ta tunkari Azima tana shirin yi mata magana da sauri Aziza ta ce
“A’a Mom!” tsayawa cak mom tayi, Aziza ta mata ido a kan taja baya, Al’mazeen ne ya matso kusa da ita ya ce
“Azima zan iya ce miki wani abu?” shuru Azima tayi kirjinta na bugawa,
“Azima Ina sonki! Kuma na au….” maganar da Al’mazeen bai karasa ba kenan Azima ta saki ihu tana toshe kunne, matsowa kusa da ita Aziza tayi ta duƙa a gabanta tace
“Azima? Ohh ina nufin Banju! Ka sa kunne da kyau, yanzu haka yola zamu tafi, yau sai yankin kwana In sha Allahu! zaku haɗe da Baffana! dama kasan karonku dashi ba dadi” wani dariya Azima ta hauyi marar dadin sauti tace
“Ke a tunaninki zan yarda na koma ne?”
“To taya zaka iya guduwa? Albishirinka! Yanzu haka da aure a kan Azima!” wani zaro ido Banju ya yi yana fadin
Sun ci amanarsa sai ya kashe miji waye mijin, Al’mazeen ya amsa da cewa
“Ni ne mijin!” wani kururuwa Azima ta saka ta miƙe da karfinta da niyyar zama macijiya dan ta saresu da sauri Aziza tasa hannu da wani farin haske ta tokari goshin Azima nan tayi ɗiff!.
“Na kafar da ita zamu iya tafiya” Aziza ta faɗa jiri take ji amma ta rasa yadda zata yi, Mom tace
“Nawaz Al’mazeen ku kama matayenku ku saka su a mota, bari na yiwa Umma magana (Umma yaya ce ga Mom wanda itace zata tsaya a karasa biki a kai sultana dakinta) har zasu fita sultana ta fashe da kuka tace
“Aziza! Za ki dawo? Kiyi min alkawari zaki dawo?” itama Azizan kuka tasa suka rungumi juna, Nawaz zai ja Aziza mom ta daga masa hannu alamun ya barsu, dagowa Aziza tayi tace
“Ban san me zance miki ba Antyna….”
“Shiiiii! Yanzu kece Antyna tunda da auren Yayana a kanki” murmushi Aziza tayi hawaye na zuba a idonta tace
“Ba a canzawa tuwo suna, ke ɗin antyna ce wacce nake ji da ita sosai, da fari zan fara neman gafararki! aurenki guda amma ta sanadina da yar uwata ba a miki shi yadda ya kamata ba, kiyi hakuri ki yafe mana, ga shi zamu kara tafiya da mom,mu kuwa me zamu ce muku? Sai dai mu muku fatan Allah ya muku sutura ranar lahira, dan kuwa kunyi mana a duniya”
Sake rungumeta Sultana tayi ta ce
“Ni kam alhamdulillah! Naji dadin aurena,dan kuwa an daura tare da Yayuna, sannan karki damu da batun tafiya da Mom, Umma tamkar mom take har ma taso tafi mom, lafiya za a kaini gidana,ni dai fatana dan Allah kiyi hakuri ki dawo a kan lokaci,kinji?” share hawaye Aziza tayi ba tare da tayi magana ba dan bata sa a ranta zata dawo ba, Nawaz ne ya kama hannun Aziza ya jata ya rabasu da sultana suna kuka suna komai, mom ce ta rufe musu fuska kowa ya kama matarsa a haka suka sauko jama’a sai guɗa ke tashi, da manyan motoci biyu zasu tafi wanda zai juri wahala da afkawa jeji mai gudu, mom da Hajiya Luba Maman Beenah kenan ba dan taso ba haka aka sa ta shiga mota,Maman Hanan kuwa cewa tayi wlh ba zata je ba, da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami da Malam Yunusa abokin Mahaifin su Nawaz.
Al'mazeen da Azima suna zaune a bayan mota Nawaz da Aziza suna zaune a gaba,mota daya suke su hudu Nawaz ke driving, Azima tamkar gunki haka ta koma, lokaci zuwa lokaci Al'mazeen zai waiga ya kalleta, sunyi nisa Al'mazeen yace
“Aziza? Hope dai Azima lafiya take?”
Gya ɗa kai Aziza tayi a sanyaye tace
“Lafiya take Hamma Mazeen, kawai na kafar mata da dafi ne idan ba haka ba sunanku gawa dan Banju zai kasheku! Ni ba zata iya kasheni ba, kuma kafin ace nayi kokarin yin wani abu dan dakatar da ita zata iya kashe ko da mutum daya ne ba zan so hakan ba, zamanta a haka shine mafi alkairi har mu isa” jinjina kai Almazeen yayi yana kara maida idonsa kan Azima.
Basu isa yola ba sai yamma lilis, dan haka Aziza tace ba zai yu su afka jeji ba su bari su sake yin asubanci gobe, dan haka suka kama hotel inda zasu kwana.
A gida kuwa karfe biyu Umma tayi oya-oya aka dauki amarya sultana aka kaita danƙareren gidanta da Khalil dinta ya gina aka ajiyeta, Umma ce tayi mata komai tamkar Mom tana nan, Umma ce ta wakilci mom a komai aka sallami baki da wasu daga cikin yan uwa.
Sadda aka ajiye sultana a gidanta za a watse a barta tasha kuka, duk hankalinta da adduarta Allah yasa Aziza ta dawo.
Kamar yadda suka ce da washe gari asubanci sukayi, sallar asuba kawai suka yi suka yanki cikin jeji inda zai sadasu da ƙauyen yankin kwana, Aziza ke nuna musu hanya, Nawaz ya kalleta yace
“Zamu iya isa a yau?” tace
“Hamma Nawaz yadda wannan mota ke gudu kamar a iska inaji nan da yamma zamu isa”
“Kai har yamma?” Nawaz ya tambaya a gajiye dan tsakani da Allah ya gaji, yadda ya zare ido ya ba wa Aziza dariya dan haka tayi murmushi, suna tafiya Nawaz ya cewa Mazeen ya musu video recording ɗin hanyar, Mazeen ya ciro waya ya hau musu video ɗin.
????????????????
Yau tinda Hajja ta farka gabanta ke faduwa, ga shi jiya tayi mafarkin Azima da Aziza sun dawo, duk da mafarkin ba sabon abu bane a wajanta.