AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da yamma ligis wajan irinsu shidda haka Aziza ta shigo yankinta wani murna da annashuwa takeji, yayinda hawaye ya b'alle mata, hakika yanayin al'karyan ya tafi da zuciyar su Nawaz, gari kore shar dashi abun sha'awa ma sha Allah, ga korayen shuke-shuke da 'ya'yan itatuwa, yankin kwana sun ga abunda basu taba gani ba, dan tun farkon shigowar su Nawaz a idon Salti ɗan gidan jauro nan yaje ya baza a gari ya ga wasu sabbin masifa ya shigo musu gari, wasu bayyanannun aljanu,nan yara da manya aka hau bin motar har gaban kofar gidan Baffa, nan aka hau cewa a kofar gidan Magaji masifan ta tsaya, mota na tsayuwa da gudu Aziza ta fito, su ma su mom fitowa sukayi,yayinda Mazeen ya fito da Azima Banju, dasu mom suka rufawa Aziza baya, mutane an cika ana kallon su mom, ko sallama Aziza bata iya yi ba tana shiga ta tsaya turuss tana kallon mahaifiyarta wacce ta rame sosai ta karayin wani fari fal da ita, Hajja na duƙe ta dibi ruwa a kwarya zata zagaya kewaye, su Mom ne suka shigo suma, cikin wani irin kuka da shauki irinta 'ya wanda takeji a kan mahaifiyarta murya na rawa mai fizgar kuka Aziza ta ce
“Hajja!” kwass!! Hajja ta saki kwarya ta juyo da sauri, haba duk daren daɗewa muryar Azizanta ba zai goge a kunnuwanta ba, kallon Aziza Hajja ke yi jikinta na rawa tama kasa magana, da kyar Hajja ta ce
“Dan Allah Aziza yau karki b’ace ki barni, na yarda zan dinga zama da gizon naki dun Allah karki tafi” da gudu Aziza ta shige cikin hajja ta riƙeta gam-gam suna wani irin kuka mai ban tausayi, harta su Mom suma hawaye sukeyi, Malam Yunusa ya kalli Mom ya ce
“Hajiya Kamila(mom)Allah ya saka miki da mafificin alkairi, Nawaz da Al’mazeen Allah ya muku albarka” suka amsa da Amin.
Ɗago Aziza daga jikinta Hajja tayi tana shafa fuskarta, Aziza cikin dashashshiyar muryarta tace
“Hajja nine na dawo, mun dawo” Hajja na shirin magana sai ga Baffa wujigan a muraran, yana can garkin shanakunsa Salti yaje ya samesa yace ai ya ga bataliyan aljanu sun nufi gidansa yanzu haka aljanun suna gidansa, shiyasa Baffa yazo a hargitse, Baffa na shigowa da sauri Aziza ta zo ta ce
“Baffa ni ce Azizanka! Baffa na dawo, kace kar na dawo sai da Azima, Baffa gata nan ga Azima nan” duk irin kunya irinta fulani nan Baffa ya rungume Aziza yasa kuka, an jima ana koke-koke, Sarki Chubaɗo dasu mai unguwa ori dasu Garkuwan yankin kwana, kai duk jama’ar yankin kwana an taro agidan Baffa, sai bayan an gama kuka tukunna aka basu abun zama, Sarki Chubaɗo yace
“Kafin a zauna ya kamata mu fara sallar magriba, hakan kuwa akayi, Aziza ta basu ruwa sukayi Alwala suka nufi masallaci.
A cikin gida ma Hajja ce ta ba wa Mom da Maman Beenah ruwan alwala, taki yarda ta daga kai ta kallesu sabida kunya irinta fulani, Maman Beenah kuwa ba bakinciki kauyen ya mata kyau ya burgeta.
Bayan sun idar da sallar, Hajja na zaune kusa da yaranta nan suka hau gaisawa dasu mom,mom ta kalli Hajja tayi murmushi ta ce
“Kyawu! Kyawun hali! Kunya! Natsuwa! Ashe duk ba a banza Aziza ta dauko ba, ta biyo Mahaifiyarta ne, dadtako halin girma! Jarumta a fuska da kuma jiki ta biyo halin mahaifinta ne! Ina tayaku murna da samun ‘ya kamar Aziza” Al’mazeen da suke shigowa cikin gidan yace
“Kai mom,Aziman fa?”
“Har da itama mana”
“To kishi kakeyi dan an yabi Aziza?” cewar Nawaz yana hararan Mazeen, murmushi su Arɗo sukayi sannan aka zauna aka hau gabatarwa da juna kai, mom ce tayi musu bayanin komai har izuwa auren da su Azima da Aziza suke da shi a yanzu, sannan ta gabatar da Nawaz a matsayin mijin Aziza ta gabatar da Al-mazeen a matsayin mijin Azima, ta ɗan bada tahirin kansu a gajarce, dago ido baffa yayi ya kalli Al’mazeen ya Kalli Nawaz kawai sai ya fashe da kuka, Baffa Mandi ya hau bubbuga kafadun Baffa yana fadin
“Alhamdulillah! Hakika Allah baya bacci,kuma yana tare da masu hakuri da masu jahadi da sadaukarwa, hakika kayi jahadi wa yankuna da dama, kayi sadaukarwa wa yankinka da komai naka, sannan kazo ka kara bi da hakuri da juriya, taya Allah zai barka a haka Magaji? yanzu dubi ka ga mijin da Allah ya bai wa Azima da Aziza, da munata tunani da kokonta wa zai auri Azima da Aziza dan ya kawo mana karshen Banju, sai ga shi Allah ya turo mana mutane daga wasu duniya daban”
Sarki Chubaɗo ya ce
“Tabbas kuwa Magaji,kai ba mutum bane kamar kowa bane, hakika muna yiwa Allah godiya daku sirakananmu, mun gode da wannan jahadi Allah ya baku lada” aka amsa da amin, nan Sarki Chubado da mai unguwa ori suka bada umarni a shiryawa manyan baƙi kuma sirakanan Magaji Bawa Shugaban garkuwan kwana abinci mai rai da lafiya, nan aka kawo wa su Mom hadaddiyar kindirmo yasha damu, Inna wuro ta ce
“Wata kila ba zaku iya cin abincin mu ba” Mom tace
“Ai idan muka sha wannan furan wlh alhamdulillah sai kuma gobe” Al’mazeen ya ce
“Ana ta magana amma banji anyi maganar matata ba?” Baffa ne ya sunkuyar da kai Hajja kuwa rufe fuska tayi, Arɗo ne yayi murmushi ya ce
“Ohh Allah Kaɗo babu kunya, yanzu kai a gabanmu kake maganar matarka?”
Almazeen ya sosa keya ya ce
“To ai kaka gani nayi to bari dai nayi shuru” aka sa dariya, Baffa yace
“Kayi hakuri ɗan nan, sakin matarka ba tare da kayan aiki ba babban hatsari ne ga mutanen yankin nan gabadaya, ka jira har zuwa gobe idan na daure shi tukunna, ai yanzu ba matarka bace katon aljani ne mugu” shuru Almazeen yayi yana kallon Azima wacce ta koma gunki, a hankali Aziza ta miƙe zata shiga bukkarsu, jiri ne ya kwasheta nan ta fadi, kafin kowa yayi kanta Nawaz ya fara dagota, Hajja kuwa ganin su Mom sun rufu a kan Aziza yasa ita taji kunya ta koma gefe tana leken fuskar Aziza, Baffa ne ya kama hannunta ya ce
“Ya salam! Aziza an huda jikinki ko?” gya ɗa kai Aziza tayi tana jan numfashi, Baffa yace
“Dole sai an nemo furen huriri”
“Me hakan yake nufi Baffa?” cewar Almazeen
“Ai kasan ita ba asalin mutum bace,maciji kuma baya son tab’o”
“Amma an harbi Azima bai bata illa har haka ba?”
“E sabida ita Aziza Banju ya rigada da ya maidata macijiya shine dalili, ga shi yanzu dare yayi ina zan samu furen huriri?” tashi Baffa ya yi ya fita zaije jejin kwana ko Allah zai sa ya samu, yana fitowa da Inno Fandi ya hadu ta mika masa furen huriri tace
“Ina matukar farin ciki da Allah ya dawo da Azima da Aziza lafiya, sai kuma shirin kashe Banju a gobe ko?” Baffa ya sosa kai yace
“Humm Fandi, abun kunya nake jin kunya” Inno Fandi ta gano abunda yake nufi dan haka ta hau masa dariya, dan kunyar kuwa na kusantar Azima da Al’mazeen zaiyi ne,tunda dole sai Almazeen ya kusanci Azima kafin Banju ya fita a jikinta a kashesa.
Da sauri Baffa ya koma ciki, Ardo yace
“Magaji ina da kaje?”
“Da wai zanje jejin kwana ne nemo furen huriri to sai Fandi ta kawo mini” jin sunan Inno Fandi yasa Aziza fara murmushi.
Jiƙa mata furen huririn akayi,tana sha ta ware.
Su mom sun saki jiki da mutanen yankin kwana sai hira sukeyi kamar an jima da sanin juna.
Sai da dare ya tsaga Ardo yace su mom suje su kwanta su huta, su mom gidan Arɗo aka kaisu aka gyara musu wajan kwanciya, su Nawaz kuwa gidan Sarki Chubaɗo aka kaisu.
A ranar Aziza da Hajja basuyi bacci ba kwana zaune sukayi suna kuka suna hira, Azima na kafe a gefe, sai da akayi asuba tukunna Aziza ta fara jin bacci Baffa kuma ya ce mata ta fito zai daure Banju sai ta sakesa, Aziza ta miƙe tana hamma dan bacci takeji.
Kayan yaki Baffa ya tanada, sai wajan takwas jama'ar yankin kwana suka hallara, Baffa ya kalli Aziza ya mata ido alaman ta saki Azima, gya ɗa kai Aziza tayi tasa hannun ta dafe goshin Azima wani haske na shiga goshin Azima, wani ajiyar zuciya Azima ta sauke, nan ta dawo hayyacinta, idanunsu ne ya sarƙe da na Baffa
“MAGAJI BAWA!!?”
“na’am BANJU! maraba da dawowa Yankin kwana!”
????????????????????
MOMYN AHLAN✍????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
(???? Macizai ne????)
MALLAKAR.
ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)
Follow me on wattpad,@Fateemah’0
????????????????????
PAID.
????️=6️⃣9️⃣↪️7️⃣0️⃣
“Wlh Baffana bani bace! Wlh ban yi yunkurin kasheka ba!” gya ɗa kai Baffa ya yi yana shafa kan Azima ya ce
“Na sani Azima” riƙe Baffa tayi gam tana kan ci gaba kuka, nan al’umman yankin kwana suka hau hamdala ana taya juna murna, wa inda sukayi wauta da farko ta hanyar dukan Aziza suka hau ba wa Baffa hakuri yace shi kam ya wuce a wajansa, nan aka zauna ana ci gaba da jajinta lamarin, lokaci zuwa lokaci Azima tana ɗaga ido ta kalli Almazeen wanda yake lullubi idonsa a lumshe bai san hayaniyar da ake yi ba.
Maga isar da sako ne ya shigo da sallama yace Sarakunan Yankuna da Muƙarrabansu sun fara isowa da wani lokaci za a fara fafatawa?" Baffa ya ce
“A shirye nake, amma a bar fafatawar sai anyi sallar la’asar da yamma kenan, a ƙara shiryawa mutanen yankuna wajan zama mai kyau da abun motsa baki dan kar su gajiya, sannan a dama musu nono mai kyau a tabbatar an basu isasshe ba ƙasasshe ba” Maga Isar da saƙo ya amsa da to, sannan Baffa yace
“Mu tafin ku dan a kara shiri” dukkansu suka fice aka bar Nawaz da Azima da Aziza, Azima idonta na kan Almazeen wanda lokaci daya taji zuciyarta ta harba da shi, a yanzu yana cikin wannan halin ne sabida ita, wani kuka Azima ta kara sakawa tana rufe fuskarta da sauri Aziza tasa hannu ta riƙo hannunta tana fadin
“Haba Azima miye haka? Godiya zakiyi wa Allah dasu Mom da Hamma Mazeen” cikin kuka har tana sheshsheƙa ta dago idonta wanda yanzu ya koma daidai amma dik da haka basu da baƙin ido ta kalli Aziza tana girgiza kai ta daga hannuwanta hawaye na zuba ta ce
“Aziza! Ni! Wai ni da kaina na ke son kashe mahaifin da ya haifeni! Wai ni da kaina na rayuwa bana bautar wanda ya halicceni! Wai ni da kaina mutane suka shiga masifa da tashin hankali! wai ni da kaina na maida yar uwata ta biyuna macijiya! Wai ni da kaina….!” kuka yaci karfinta da sauri Aziza ta rungumeta tana bubbuga bayanta itama tana kuka
“Taya zan manta da wannan abun a rayuwata! Kenan mu haka kaddararmu take!” ɗago fuskarta Aziza tayi tace
“Karki yi sab’o, ki godewa Allah, sannan duk abunda kika lissafa ai bake kikayi ba Banju ne ya yi, dan haka ki bar fadin haka Sis” cikin kukan tausayi da Azima ta kasa tsayarwa tace
“Amma da jikin wa!? Da fuskar wa?”
“Koma da miye ne komai zan zama tahiri, ki ta nanata kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yafi wannan sambatun da kikeyi dan bana so,kina ji na ko?” Azima ta gya ɗa kai hawaye na kan sauka tana kallon Almazeen wanda Nawaz ke riƙe da hannunsa yana ji kamar yasa kuka dan tausayinsa, zuwa can da suka gama kukan Nawaz ya kalli Aziza ya ce
“Tashi mu tafi watakila yanzu kam ana can filin yaki, zo muje karo na farko a rayiwata naga yadda ake faɗa tsakanin mutum da aljan” tashi Aziza tayi ta kalli Azima tace
“Ki kula da kanki da kuma Hamma Mazeen uhum?” Azima ta gya ɗa kai, Nawaz da Aziza suka fita, suna fita Azima ta miƙe a hankali ta karasa jikin gadon ta kwanta a kusa da Almazeen har yanzu jikinsa da zafi sosai, tana kwantawa ta kama hannunsa tana kallon kyakkyawar fuskarsa ta ɗora hannunsa a fuskarta ta lumshe ido.