AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️
Hakika su Mom sun sha mamakin ganin mutane him a wannan alkarya, mutanen yankuna sun zo daga yankuna daban-daban, jama’a an cika ana kallo, Aziza na zaune kusa da mom, Nawaz yana gefen hannun hagunta, ya ce
“Mom wlh naso ace sultana tana nan da ta ga abunda take kalla a zahiri a tv” mom tayi murmushi.
A hankali Baffa ya fito yana riƙe da zureren takwabinsa wanda ya kashe Banju da shi a karon farko amma wannan karon bai yi amfani da zaren sakar dana ba, dan ko ya koma jejin lore ba ba shi za ayi ba,amma duk da haka yau sai ya kashe Banju da yardan Allah.
Kunce Banju Baffa ya yi, Banju yana ganin takwabin hannun Baffa ya ce
“Magaji! ka ajiye takwabin nan ba da shi zamu gwabza ba” murmushi Baffa ya yi ya kalli Nawaz ya miƙa masa takwabin, zuwa Nawaz ya yi ya karba yana riƙewa sai da yaji damtsen hannunsa ya girgiza, kara sarawa Baffa Nawaz ya yi sannan ya koma ya zauna.
Banju ya kalli Baffa ya ce
“Ba kai ka yarda da kanka ba?to inaso ne mu gwabza da karfin-karfi,ni aljani ne faɗa da aljani kuma ba dadi” jan kafa baya Baffa ya yi ya ware hannunsa ya ce
“Bar ganin ka ƙereni a tsayi da girman jiki! a haka na daureka na kasheka a farko, ni mutum ne amma ba irin wanda kake tunani ba na san kasan da haka” Baffa na fadi ya hau tada guguwa, ganin haka yasa Banju wani juyi ya koma wani shirgegen Maciji???? blue mai matukar kauri da girma, wayyo karka so ka ga yadda wasu daga cikin masu kallo aka watse daga ciki kuwa har da mom, dan tace wlh wannan kallo ba da ita ba.
Kokarin sara Banju ya hau kai wa Baffa Baffa na b'acewa a cikin iska, yayinda masu kallo aka kara ja baya ana darewa ana basu fili dan yau abun babba ne, an gwabza sosai tsakanin Baffa da Banju, da ya ga tabbas ba fa zai samu galaba a kan Baffa ba nan ya yanki wajan jama'a yana shirin ya kai musu sara dan kuwa ya tabbatar da Magaji zai kashesa! to dan haka a cikin wa innan dibbannin alumman gwara ya shafe ko da rabi ne, nan ya yi kansu gadan-gadan ganin haka yasa Nawaz fizgar hannun Aziza suka sa gudu tare da mutane, ganin yadda Banju ya yi kan alumma yasa Baffa haɗa hayaki ya kwashe mutanen ya zubar dasu gefe, jelarsa Banju yasa zai kwashi wasu kafin ya kwashe Baffa ya kuma kwashesu, ganin haka yasa ya buɗe bakinsa zaiyi musu b'arin ambaliyar wuta cikin hanzari Baffa yayi wani tsalle ya tashi sama, dan kuwa idan Banju yayi b'arin wutar nan za a mutu dayawa, kafin Banju yayi tuni Baffa ya haye saman kansa tare da zaro wani wuƙa ya dab'awa Banju a tsakiyar kai, cak Banju ya tsaya, a hankali ya fara sulalewa yana zama mutum har ya zama mutum gabadaya, yana gama zama mutum Baffa na zaune a saman wuyarsa da karamin wukar da ya dab'a masa, tsalle Baffa ya yi ya sauka daga wuyar Banju ya dirƙo akan kafafunsa ya juya baya ya maida hannunwansa ya rungume a bayansa.
Da kyar Banju ya ce
“Wuƙar Dafi!” Banju na faɗi wukar ta narke a cikin kan Banju ta b’ace bat, dan kuwa ba wuƙa bace kamar sauran wuƙaƙe, Baffa ne ya haɗa da hannunsa dan zuwan wannan rana, sharabbbb!! Banju ya zube a kasa, nan take ya kama da wuta har sai da yaci ya ƙone ƙurmuss!! Hamdala da Wani ihu da guɗa da al’umma suka saka suna fadin
“Magaji! Magaji! Magaji!” suna daga hannu, wani hawaye ne ya tsiraro daga idon Baffa, da gudu Aziza ta tashi ta zo ta rungume mahaifinta tasa kuka, shima Baffa tamkar an cire masa wuƙa a maƙoro haka yakeji, Nawaz ne ya taso ya zo shima Baffa ha rungumesa, sannan ya karbi wuƙar ya damƙawa Aziza a hannunta yace a mallamaka mata dan tare sukayi yaƙin, nan aka kara sa ihu ana kabbara kafin kace me an daga baffa sama ana ambatar sunansa, sarki chubaɗo mai unguwan yankin kwana ori da kowa na yanki kwana murna sukeyi harda hawayen farinciki, sauran yankuna kuwa ji sukeyi ina ma ace Magaji a yankinsu yake, ko ba komai zasu samu karramawa da girmamawa da daukaka daga sauran manyan yankuna, haka aka dinga miƙawa Baffa hannu ana jinjinawa jarumtarsa.
Da kyar suka saffe sukayi sallar magriba, wasu yankuna wa inda basu da nisa sai sun koma yankinsu wasu gobe zasu koma.
Ranar yankin kwana wasai, duk majalisa kuwa hiran Magaji Bawa ake yi da yaransa Azima da Aziza, Jauro kuwa dan kunya da tsangwaman da ake masa yasa ya kasa fitowa.
Washe gari bayan manyan yankuna sun karrama Baffa nan suka gaya masa ai a yankuna yanzu babban yanki shine yankin kwana, bayan an gama komai suka yi masu sallama, godiya sosai jama'ar kwana sukayi ma wa inda suka samu damar halartan wannan gayyata ta fafatawa.
Bayan kwana uku da faruwar hakan komai ya zama daidai alhamdulillah Ma sha Allah.
Yanzu Baffa ya maida hankalinsa a wajan yiwa Almazeen magani, sai da Almazeen ya shafe sati curr kafin ya farfaɗo ya dawo hayyacinsa, a wannan lokacin su mom sunyi sabo da mutanen kauyen kwana fiye da tunanin mai tunani.
Washe garin ranar da al'mazeen ya farka nan sarki chubaɗo ya tara su yace yana da magana, bayan kowa ya haɗu nan yake shaida bukatarsa na son sauƙa a kan kujerar mulkin yankin kwana, sannan ya bayyana Baffa a matsayin wanda zai mulke yankin kwana, girgiza kai Baffa ya hau yi kafin yace a'a tuni alumma sukace sunji sun gani, babu yadda Baffa ya iya dan kuwa bai so ba amma kowa ya nuna yana son Baffa ya mulke yankin kwana, haka sarki chubaɗo yasa aka rubuta sakon gayyata inda yankuna suka ce zasu zo, dan za ayi bikin da ba a taba yi ba na al'adun fulani.
????????????????????
Kamar yadda aka tanada haka kuwa ta kasance wajan karfe goma na safe aka fara bikin naɗa Baffa sarautar kwana, inda manyan yankuna da ƙananun yankuna duk sun zo, anyi walima Baffa ya samu alkairi ba ma iyakar shi daya ba harda jama’ar yankinsa, yankin kwana Allah ya ɗagata sama.
Wajan irinsu biyu haka aka kammala taro lafiya, an yanka su shanaye dasu kaji da zabbi an sha kindirmo, kai taro dai tayi saidai muce Allah ya taya Baffa Magaji Bawa Arɗo riƙo.
Da yamma Azima da Aziza suna zaune a bukkarsu, hajja kuma suna bukkarta dasu mom, bayan Aziza ta gama koyawa Azima karatu ta kalleta ta ce
“Aziza dama ina son na tambayeki” gyara zama Aziza tayi tace
“To inajin yar uwata” maganganun da Al’mazeen ya gaya mata a kunne ne take son Aziza ta fassara mata, dan ta kwashe maganganun tsaf a cikin kanta, dan haka ta gayawa Aziza tace ta fassara mata, dariya Aziza ta hau yi har tana riƙe ciki ta ce
“Inyee! Kin faɗa soyayya ne?” haɗa rai Azima tayi tace ban son wulakanci idan ba zaki gaya min ba sai naje na tambayi mijinki Hamma Nawaz ko naje na tambayi mom”
“Allah ya baki hakuri maida wuƙar” nan ta fassara mata abunda kalmomin ke nufi, wani murmushi Azima tayi tana rufe fuskarta da tafin hannunta, Aziza zatayi magana sukaji sallamarsu Nawaz sai da gabanta ya faɗi, su dai basu fito ba sunajin maganarsu dai a tsakar gida, Almazeen ne ya ce
“Mom ya kamata mu koma gida, dan muje mu dubasu mu ga lafiyarsu, barin ma mu da muke da asibiti” mom ta ce
“Nima na fara wannan tunani zuwa anjima zamuyi magana da Baban su Azizan” wani zaro ido Azima da Aziza sukayi bama su kadai ba harda Hajja, dan tasan za a kwashesu a tafi dasu ne tunda yara da mazajensu, kuka ta fara haɗiyewa, Almazeen ya kuma cewa
“Mom ina yaran naki suke? Ya kamata dai yau su zo su kai mu yawo mu ga gari” mom ta ce
“Hakane, Azima! Aziza!” a sanyaye suka amsa da na’am, barin ma Aziza damuwarta yafi bayyana ƙarara a fuskarta, a tare suka fito suka duƙa, mom tace
“Ku dauko mayafi kuzo ku kai mazajenku yawon ganin gari” amsawa suka yi da to suka dau mayafin dama dogon abaya ce iri daya a jikinsu, mayafinsa suka dauka suka rufa kansu da shi, a kofar gida suka samu Almazeen da Nawaz sannan suka hau tafiya babu mai cewa qala, duk inda suka wuce sai an bisu da kallon burgewa ganin yadda suke tafiya tamkar wasu taurari masu haska sararin samaniya.
Bayan sun kewaya dasu, Azima ta kalli Aziza tace
“Ukhty muje rafin jimulo” a sanyaye Aziza ta amsa da to, dan tun lokacin da taji anyi maganar tafiya jikinta yayi sanyi dan idan tace tana son komawa tayi babban karya, suna isa rafin wani iska mai dadi da yake kaɗawa ga ruwa farin sol abun burgewa ga ganyaye kore shar kwance a wajan,
“Wowww!” Nawaz da Almazeen suka furta, Azima tana satar kallon Almazeen, hannunta ya kama suka zagaya ta gefen rafin dan yana da bukatar suyi luv, dik da mugun kunyarsa takeji, suna barin wajan Nawaz ya maida idonsa kan Aziza wacce duk ta taburce kamar ma kuka take son yi, dan ita har yanzu bata taba ji Nawaz yace yana sonta ba, dan haka itama ba zata buɗe zuciyarta ba balle ta cutu, hannunta ya kama tayi saurin daga ido ta kallesa, janta yayi ya haɗata da bishiya murya a can kasa ya ce
“What’s the matter?” girgiza kai tayi sai kuma hawaye suka biyo baya, hannu yasa ya goge mata yace
“Ba ki so ki koma ne ko?” shuru tayi, wani murmushi yaƙen takaici ya yi yana sakinta ya juya baya ya ce
“Na faɗi daidai shiyasa kika ƙi cewa komai?, karki damu duk yadda kike so kiyi, bcox u are free now” ya faɗa kamar a ɗan zafafe, rungumesa ta baya Aziza tayi tasa kukanta mai sauti, rintse ido ya yi ya ce
“Kamar dai na taba gaya miki bana son kuka ko? To sakeni!” sake riƙesa tayi, hannunta yaja suka isa bakin ruwan ya zauna ya zira kafafunsa a ciki, itama zaman tayi kusa da shi ta kamo hannunsa ta kifa kanta a kafadarsa, bata san lokacin da ta furta masa cewa
“Hamma Nawaz, ka taba ji kana sona? Ko kawai tausayina kakeji?” ajiyar zuciya ya sauke ya juyo ya fuskanceta yace
“Idan har zaki iya karanta abunda yake cikin idona, sannan ki auna bugun zuciyata” ya fada yana ɗora hannunta a saiti zuciyarsa dake bugawa da sauri
“Zaki iya ba wa kanki amsa, idan hakan bai samu ba, ki bari idan muka koma kd zaki tabbatar” daga haka bai sake cewa da ita komai ba banda rungumeta da yayi.
????????????????
Almazeen suna zagayawa baya da Azima ya rungumeta sosai a jikinsa, rufe fuskarta tayi da kirjinsa tana murmushi tanajin wani bakon yanayi a tare da ita, sakinta Mazeen ya yi ya rungumeta ta baya ya ce
“Na gama haukacewa na susuce a kan son….” shuru yayi ganin tana ta wani aikin rufe fuska, bakinsa yasa a saitin kunnenta yace
“Wai ni wannan kunyar na miye ne? tinda na farka ake guduna, ko dan sabida daren….” bai karasa ba ta jiyo ta sauri ta rike bakinsa tana shigewa jikinsa, murmushi yayi yace to faɗamin
“Ana sona?” ɗago kai tayi tasa idonta a na shi ta ce
“Idan ban furta hakan ba na zama butulu! wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin tawa, miye ribata idan ban so shi ba, ance tukaicin so kauna, sabida haka ina kaunarka Hamma Mazeen” wani runguma Mazeen yayiwa Azima cike da so, kafin ya haɗe bakinsa da nata ya hau bata hot kiss, Azima tayi alkawari ba zata taba juyawa Mazeen baya ba kamar yadda shi ma bai juya mata ba a lokacin da take abun gudu a wajan mutane, shiyasa ko da yake romantic dinta bata yi yunkurin dakatar da shi ba, tsayuwa ce ta gagaresu suka zube kasa, murzanta yake yi cikin salo da shaukin kauna, Azima ganin hankalinsa ya fara gushewa ne ya sakata zare jikinta daga na shi,yayi saurin riƙota ta ce
“Don Allah Hamma, ka duba inda muke,kuma ma ai” sai kuma tayi shuru, saurin saita natsuwarsa Almazeen ya yi, amma gaskiya ba zasu kara sati a garin nan ba zasu koma dan ya samu yaji dadin bai ji ba a daren farko dan wuya kawai yaci.