AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

 Tashi yayi ya kama hannunta ya ɗagata tsaye, yace

“Muje gida” riƙesa tayi tace
“Kayi fushi ne?” ɗan murmushi yayi ya girgiza mata kai alaman a’a, wajan su Nawaz suka dawo har yanzu suna zaune a bakin ruwa yana rungume da Aziza, Almazeen ya ce
“To romio and Juliet muje gida lokacin sallar magriba yayi” Nawaz yace
“Okay Laila da Majnun” dariya Almazeen yayi dan zuciyarsa fari sol.

Gida Suka tafi, bayan sallar isha'i mom ke gayawa su Nawaz yadda sukayi da Babansu Aziza kuma itama tayi na'am da maganarsa na cewa a dan barsu Azima da Aziza tukunna, su zasu tafi gobe, Almazeen da Nawaz kamar su kurma ihu, Nawaz da gajen hakuri yace

“Har na kwana nawa?” mom tace ungo nan naka????????
“Har na tsawon wata daya,ni kuma nace a barsu suyi wata biyu tunda alfarma suka nema,kuma ai gaskiya ne tinda sun jima basu ne, yanzu kuma zama na dindindin zasuyi daku”
“Haba dan Allah mom, yanzu dake za a yanke wannan shawaran?” cewar mazeen,mom tace bana son rashin kunya, maza ku tashi ku fara shiryawa, a zuciye Nawaz ya fice Almazeen ya bisa a baya.

 Washe gari asubanci sukayi, kaff jama'ar kwana aka fito yi musu sallama, Almazeen ne kawai yayi sallama da Azima inda ya jima yana tsotsar bakinta, Nawaz kuwa ya ƙi kallon Aziza dan yace itama harda haɗin bakinta dama ba son komawa take yi ba.


 Baffa ya haɗawa su Mom kaya sha tara ta arziki yayinda suke zubawa juna godiya cikin mutunci da mutuntawa, haka Baffa ya rungumi su Almazeen da Nawaz, sukayi musabaha da Malam Yunusa da Alhaji Karami, su Inna wuro ma sunyi wa mom da Maman beenah abun arziki, mom tace 

“Dan Allah wata rana ku kawo mana ziyara, da sunyi wata daya kuma mazajensu zasu zo su daukesu”
“In sha Allah” mota suka shiga aka dinga ɗaga musu hannu, da gudu Nawaz ya figi motar Aziza ta fito itama da gudu tana daga masa hannu ya hangeta ta glass din mota amma sai ya kara gudun motar, cikin rashin jin dadi tin daga Azima har Azizan suka juya jiki a sanyaye, a ranar haka suka wuni zuciyarsu babu dadi amma suna zuba hira da wasa da dariya da Hajjarsu,yayinda Yawuro ta fara musu gyara tana tsumasu dan tana so ace kafin nan da wata dayan nan sun sama zam-zam dasu, idan mazajensu suka kusancesu basu ba kara tunanin wata mace.

  @@@@

Sabida gudun da suke yi yasa biyar na yamma suka fice daga jeji suka b’illa titi, yau ma sai da suka kara kwana cikin garin yola kafin da washe gari suka kama hanyar kd, suna isa mom ta kira sultana tace mata sun dawo, wani ihu da murna Sultana tayi a waya mom ta bata labarin abunda ya faru, bata gama ji ba zumudi yasa ta katse wayar ta kalli Khalil dake danna waya tace
“Dear su mom sun dawo” da murna a fuskarsa yace
“Alhamdulillah”
“Dear tashi mu tafi ina son ganin Aziza”
“Oh Allah sultana ki bari su huta sai muje da daddare”
“O’o ni kawai ka tashi mu tafi yanzu sai ka dawo ka daukeni da daddaren” ta fada tana buga kafafunta a kasa” hararanta yayi yace “ai saiki dauko mayafinki” kiss ta sauke masa akumatu tana godiya da gudu ta hau sama dan dauka mayafinta ta sauko a mota ta samesa ya tada suka nufi gidansu.

????????????????

MOMYN AHLAN✍????
GARKUWAR MACIZAI????????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ AZIMA DA AZIZA????✨
    (???? Macizai ne????)

    MALLAKAR.

ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

MARUBUCIYAR.
1- HALITTA DAGA ALLAH NE.
2- GUDU A JEJI.
3- SHUHADA.
4- NIDA ƘANNEN MIJINA.
5- WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200).
6- COLONEL UBAIDULLAH.
7- ITA CE ZUCIYATA(#200).
8- SAMIMA (MACIJIYA CE.
9- GAWURTACCEN SOJA(#300).
10- DA NA SANI NA.
  11- BADAWIYYAH
12- DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)
Now
13- AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)

Follow me on wattpad,@Fateemah’0

   ????????????????????

PAID.
????️=7️⃣1️⃣↪️7️⃣2️⃣???????????????? ALHAMDULILLAH!.

Suna isa da gudu tayi cikin gidan tana fadin
“Oyoyo Mom! Oyoyo Anty Aziza!” mom dake zaune a parlour ta ce
“Sai dai ni Amma Aziza kam tana garinsu” turus sultana ta tsaya tace
“Bangane tana garinsu ba mom? Sakinta Yaya yayi?”
“Taya zai saketa? Ba yanzu zasu dawo bane sai sun kwana biyu,mahaifinsu ne ya roƙi alfarma a barsu” cikin rashin jin dadi Sultana ta zauna tace
“Wayyo wlh banji dadi ba mom, to ba komai Allah ya dawo dasu lafiya, inasu Yaya Nawaz da Yaya Almazeen?”
“Muna isowa basu zauna ba asibiti suka wuce”
“Ayya Allah Sarki! Ohh wayyo Mom na bar Khalil a waje ashe” Mom tace
“Shi dai yaso zaman waje ai khalil ba baƙo bane”
“Wlh kuwa mom kyaleta iyayi take ji da shi waya na tsayayi” cewar khalil da yake shigowa ya duƙa ya gaishe da mom ta amsa tana dariya,sultana tace
“Oh wato ma haka zaka ce ko? Ba komai ai”
“To dan Allah mom ki ji ni da ‘ya fa, to me nace?” mom tace
“Ahh kai kam baka ce komai ba” khalil yayi dariya yana fadin
“Inasu Nawaz?”
“Sunje asibiti,ai muna isowa basu zauna ba”
“Ayya Allah Sarki, to bari na wuce mom”
“Ah to ita Sultanan fa?”
“Zan dawo na dauketa da daddare” khalil ya fada yana ficewa, sultana ta miƙe a dogon kujera tana fadin
“Ohh mom korata kikeyi?”
“To nan gidanki ne? Me zaki zauna ki min”
“To yau ma a nan zan kwana”
“ashe da rabon zaki kwana a wajan gate” mom ta fada tana hawa sama, sultana dakin Aziza ta shiga tana tuno abubuwa da dama har bacci ya kwasheta, kamar yadda Khalil ya faɗa bayan isha’i yazo ya dauki sultana, su Nawaz basu dawo ba sai wajan goma, sai da sukayi wanka kafin suka shiga wajan mom a lokacin tana waya a kawo mata ‘yar aiki wacce zata dinga tayata aiki da zama dan ita daya ne, sai da ta gama wayarta ta fuskancesu ta ce
“Sannunku da dawowa fatan komai lafiya?” Almazeen ne yace
“E mom komai lafiya alhamdulillah! Amma muna kewan matayenmu,bamu san halin da suke ciki ba ,su ma basu san wanda muke ciki ba” mom tayi murmushi tace
“Haba dai ai wata biyu kamar kwana biyu ne a wajan ubangiji” sai a sannan Nawaz ya yi magana fuskarsa a haɗe
“Mom wata biyu kuma? Ba wata daya naji kince ba? Baffa ma fa wata daya naji yace” mom tace
“E wata daya ne nice nace suyi wata biyu” tashi Nawaz yayi zai fice mom tace
“Akwai abinci a dinning”
“Bana jin yunwa” yana gama fadi ya fita, Almazeen shi ma tashi yayi mom tace
“Kana nan ne tukunna?”
“A’a mom zan tafi gobe naje na duba asibitina nima, ba zan dawo nan kusa ba sai an kwana biyu idan zamuje kwaso matanmu” mom tace
“Ya kamata a haɗa musu lefe ayi shagalin biki, ya kasance kafin su dawo an tanada musu komai, da kuma gida wajan zama, shin a gidanka na kano Azima zata zauna? Kasan fa yanzu ba kamar da bane, Aziman yanzu ba jin dadin zama zatayi dasu Hajiya Lawiza da yaransu ba, Azima kuma matarka ce amanace a hannunka a san abun yi gaskiya” komawa Almazeen yayi ya zauna yace
“Mom ko da a kano na zauna da Azima wlh su Maman Hanan zasuje su takura mata, inaga gidan dake kasan unguwan nan zanje na taya naji, tunda babu abunda nake yi a kanon idan kuma ta asibitina ne ni zan iya zuwa ina kwana biyu ina dawowa” mom tace
“Hanya zai aureka kenan, to ba matsala Allah ya zaba mana abunda yafi alkairi, ka ga shi abokin naka ba shi da matsala a nan zasu zauna dani” Almzeen yace
“Ai hakan yafi mom shiyasa nima zan dawo cikin masu sona kawai” mom tayi murmushi, sun jima suna tattaunawa har wajan sha biyu kafin ya yiwa mom sai da safe ya tafi, a kwance ya samu Nawaz ya ɗora hannu a fuskarsa alaman tunani, zama shima ya yi, Nawaz yace
“An rabaka da matarka amma me ka zauna mom ke gaya maka? Ai wlh na fahimci mom idam na ci gaba da zama zata iya cewa su yi wata shidda ma” da sauri Almazeen yace
“Kamar kuwa ka sani cewa tayi sai sunyi shekara” wani zabura Nawaz ya yi yace
“She mene?”
“Shekara” Almazeen ya fada yana dariya, tsaki Nawaz ya yi, sai da mazeen ya gama dariyarsa kafin ya basa labarin yadda sukayi da Mom, Allah yasa mu dace, Nawaz ya faɗi tare da shigewa daki ya kwanta, amma kamar jiya ya kasa bacci dan kuwa sun bar wa juna abin tuni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button