AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta bangarensu Azima da Aziza yadda mazajen nasu ke ji a kansu haka suma suke ji a kansu.
Da washe gari Almazeen na wanka dan zai tafi kano yau Nawaz na danna system, wayar Almazeen ne yayi kara yayi kara yana dubawa yaga Alisha
“Mayya!” Nawaz ya fadi a fusace yana ci gaba da aikinsa,jin kiran wayar takeyi babu fa shi yasa ya jawo wayar zai daga wata daraba ta faɗo masa, murmushi yayi tunowa da haukan kishin Alisha dan haka Nawaz ya daga kafin Alisha tayi magana yace
“Wai ke baki san yayi aure bane?”
“What!?”
“Yes daidaine abunda kikaji na fadi, yanzu baya yayinki! Idan kuma baki yarda ba zan gwada miki kiji dan ki tabbatar da abunda nake gaya miki sabida….” maganar Nawaz ne ya tsaya sakamakon fitowa da Almazeen yayi, Nawaz yace
“Allah ya taimaki Majnun na Azima! wai ni kam ina Alisha ne Almazeen?” mazeen ya riƙe kai yace
“Wlh nikam na ma mance da ita”
“Kar dai kace min bata san kayi aure ba?”
“Wlh bata sani ba,har shakkar gaya mata nake dan ban san yadda zata dau lamarin ba” Nawaz yace
“To ai ga shi sai ka gaya mata” ya fada yana mikawa Almazeen waya, wani zare ido Almazeen yayi Nawaz kuwa ko a jikinsa, ba yadda ya iya haka ya karbi wayar yana shirin yi mata bayani ta wankesa tass a kan cewa ya ci amanarta kuma babu ita babu shi, tana gama gaya masa ta ajiye wayarta.
"Me kenan kayi haka Nawaz?"
“Me kuwa nayi? Ita fa ta kira! Cika min kunne take,kuma ma ai taimakonka nayi” ya fada yana ci gaba da aikinsa, Allah ya kyauta Almazeen ya fadi Nawaz ya amsa da amin, yana gama shirinsa ya shiga ya yiwa mom sallama a lokacin an kawo mata wata mai aiki, Allah ya tsare ta masa ya amsa amin sannan ya shiga motarsa sai kano.
????????????????????????
Haka suka ci gaba da rayuwarsu amma hankalinsu yana kan matayensu wanda suma kullum acikin tunanin mazajensu suke, ga shi babu netwrk babu waya bare a ji muryan juna ko hankali zai kwanta, a daddafe akayi sati biyu, Almazeen yaji ina sam ya kasa hakuri ya tattaro yazo Kd yacewa mom zasu je dauko matayensu Mom tace aa suyi hakuri dai a cike sati biyun, da kyar sukayi sati uku hakurin Nawaz ya kare ya shirya tafiya ya cewa mom zaije kano, mom ta tambayesa lafiya kuwa yace mata lafiya lau kawai zaije bikin wani abokinsu ne dama kuma yana da tiyatan da zaiyi a can, Allah ya kiyaye hanya a dawo lafiya mom ta masa
Nawaz yana zuwa kano dama tare suka shirya tafiyarsu shida Mazeen nan suka dauki hanyar yola ba tare da sanin mom ba.
Sai da suka kwana da washe gari suka yanki jejin kwana, kasancewar Nawaz ya ƙware a driving musamman ta fannin gudu yasa wajan biyar suna cikin yankin kwana, tun shigowar motarsu yara suka hau bi, a lokacin kuma Azima da Aziza suna kwance a bukka Hajja tana gidan Arɗo, Azima ta tsokani Aziza, Aziza ta hau binta da gudu zata daketa kanta ko dankwali babu, a wannan gudun ne suka fito har waje daidai a kan idon Nawaz da Almazeen, ga shi sun wani kara bulbul dasu sun ciko, wani daci Nawaz ya hadiye yana wurgawa Aziza harara, ganin basu san da zuwan su bane yasa Nawaz danna horn da karfi a firgice suka juyo, ko wacce idonta a cikin na mijinta ya sauka, gaban Aziza ne ya buga ganin hararan da Nawaz ke binta da shi, ita kam shikenan ta shiga uku, ranar da zai tafi ba ayi rabuwar dadi ba, yau kuma ya dawo za a fara rigima,tukunna ma me ya kawosu? Ai ba yau bane ranar da ya kamata ace sunzo daukarsu, Azima ce tayi karfin halin murmushi duk da itama zata iya cewa ba yanzu bane ya kamata ace sun dawo daukarsu ba, Nawaz ne ya hangi wani ɗan fullo rataye da sandarsa a wuyarsa yana tahowa ga Aziza kai ba dankwali tsoro kuma yasa ta kasa gaba ta kasa baya, da sauri Nawaz ya fito a motar yazo ya ja hannun Aziza suka wuce gida, ganin Nawaz ya fita yasa Azima shiga motar da sauri tana yiwa Almazeen oyoyo.
yana rungumeta ya saki ni’imartacciyar ajiyar zuciya
“I miss u!” yaji ta fadi, saurin sakinta yayi yace
“Wow! Aziza ta koya miki kenan!” gya ɗa kai tayi tana murmushi tace
“Yanzu nima inajin yaren sosai”
“To yayi kyau, ina Baffanmu da Hajjarmu?”
“Baffa yana fada,Hajja kuma taje gidan Arɗo, amma na tabbata yanzu labari yaje garesu kunzo yanzu zaka ga hajja har ma da Baffan”
“To kafin su zo ,mu sha soyayya a mota tinda Nawaz ya ja Aziza ciki” ya fada yana shirin kama bakinta tace
“Amma naga kamar da fushi ya jamin yar uwata,kuma wlh laifi nane, dan tana kwance na tsokaneta” jinjina kai Almazeen yayi yace
“Nima naji haushin wannan tsalle-tsallen naku, kawai murna da farincikin ganinki ne ya danne fushina, amma shi baya iya control ɗin fushinsa sam, dan Allah karki sake” a sanyaye Azima tace
“To kayi hakuri Hamma Mazeen”
“Ai ya wuce” ya faɗa yana shafota.
Suna shiga cikin gidan, bukkarsu ya wuce da ita, suna shiga ciki ya saki hannunta a masifance yace
“Ashe baki da hankali? Miye haka? Au ashe da bamu nan abunda kukayi kenan? Guje-guje? Wannan ai kauyenci ne! Da Aurenmu a kanku amma kuke guje-guje ga karti na wucewa, ke da shike kece isassa kai ba dankwali ko? Ya miki kyau ki shirya gobe zamu tafi” zaro ido Aziza tayi kwalla na cika a idonta kafin tayi magana yace
“Okay wato baki son tafiya sabida can babu maza da guje-guje ko?” yana cikin faɗa da masifa ta rungumesa ta ce
“Sorry!” tana fadi kuwa yayi shuru da fadan nasa, yayi missing dinta dan haka yasa hannu ya rungumeta yace
“Karki sake, hakan da na gani ya taba min zuciya”
“In sha Allah, kayi hakuri” zaiyi magana suka ji sallamarsu Hajja dasu Almazeen da Azima dasu inna wuro, fitowa Nawaz da Aziza sukayi inna wuro tace
“Ohh Allah wato kai har ka wuce daki da ita? Wai wai wai kar ayi abun kunya bari Magaji yazo a baku matayenku” Nawaz da Almazeen sukayi murmushi nan aka hau gaisawa, Hajja tana tambaya ya mom, suka amsa da tana lafiya tama ce a gaishesu (kaji su Almazeen da Nawaz da karya mom da bata san sunzo ba).
Bayan sun gama gaisawa da matan suka wuce wajan Baffa a fada, nan aka hau gaisawa suka shaidawa Baffa sunzo daukar matansu ne zasu tafi gobe,Baffa Mandi da Ardo da sarkin yankin kwana mai murabus chubado suka hau dariya, ardo yace a basu matansu kawai su tafi, nan suka ce su gobe suke son komawa Baffa yace ba damuwa Allah ya kaimu.
Ko da suka zo hira Nawaz da Aziza basu yi wani dogon hira ba ya jaddada mata akan su shirya da wuri, su Almazeen ne da Azima aka sha luv shima ya gaya mata su shirya da wuri.
Asubanci suka ku ma yi inda jama'a aka fito rakasu, hajja kam taki fitowa rakasu, Azima da Aziza kuka kamar ransu zai fita,itama Hajja kukan takeyi, su Inna wuro ne suka yi musu nasiha akan su bi Allah da Manzon Allah sannan su bi mazajensu,yi nayi bari na bari shine aure, da haka suka shiga mota ana daga musu hannu nan Nawaz yaja motar da gudu suka hau tafiya, a hanya Almazeen ne ya rarrashi Azimansa, Aziza kuwa da tayi kukanta da kanta ta bawa kanta hakuri tayi shuru.
Sai shidda suka fice a jeji, kamar yadda suka saba hotel suka kama, ko a daki Nawaz baccinsa yayi, Azizan ma haka, Almazeen kuwa yaso kashe arnan sama Azima ta hau masa kuka dole ya kyaleta ya lallatsata kawai ya barta, ko da mom sukayi waya da Nawaz da daddare a lokacin suna yola take ce masa ta kirasa bai shiga ba yace mata ai sun shiga tiyata ne gobe ma suna nan dawowa, Allah ya dawo dasu lafiya mom tace.
Da safe sai wajan takwas kafin suka sake kama hanya a wannan lokacin anyi canji Almazeen ne ke driving Nawaz na zaune a gefe Azima da Aziza suna zaune a bayan mota, jifa-jifa suna ɗan taba hira.
Sai wajan hudu suka shigo garin gwamna, basu zarce ko ina ba sai gida, da sallama suka shiga a lokacin mom na magana da sabuwar mai aikinta Lami taji sallamarsu Nawaz, amsawa tayi tana juyowa sai ganinsu Azima da Aziza tayi, da mugun mamaki mom ke kallonsu kafin tace
“Dama dauko su Aziza kukaje yi ne?” Almazeen ya hau sosa kai, Nawaz yace
“E wlh mom, cewa akayi Aziza nata kuka tana so ta dawo ta ganni tayi kewarki,ko zakice ba haka bane?” ya fada yana kallon Aziza wacce tayi narai-narai da ido tace
“Wlh mom ba haka bane”
“Ohh nayi karya kenan?”
“Ni dai ban ce ba, amma wlh ni banyi kuka ba ko Azima?” Azima ta kunshe dariya tace
“Ni dai ban sani ba” mom tace kyalesu na san ba zaki ce ba, to sannunku da kokari ance ku bar yara suyi wata kunje kun kwasosu ai shikenan, Azima Aziza ku hau sama dakin sultana na da, suka amsa da to sannan suka hau sama, mom tace
“Maganar lefensu dama jibi ne za a kawo,shagalin bikin fa?”
“Mom dan Allah a bar wani maganar shagali” cewar Nawaz,mom tasan halinsa duk wa innan abubuwan bai damesa ba, mom tace gobe kasa a kwashe kayan part dinka a kawo sabbi dan dama munyi wannan maganar dasu Baffan Aziza da yan uwanta kafin mu dawo, na gaya musu mu yaran kawai mukeso, amma dik da haka mahaifinsu ya bada garken shanu biyu na Azima da kuma Aziza yace dai ba dadi ace yara ba a ga kayan da yan uwansu suka musu ba, bare kuma ace akwai uwa da uba, na karba ne dan ya fimu gaskiya, dan haka Almazeen ya maganar gidan naka?”
“Eh mom an gama magana gobe ma za a iya zuwa ayi jere dan haka zamuyi other tare da Nawaz”
“Eh hakan ma yayi, ai da wasu daga yan uwansu sunzo sun ga inda yaransu zasu zauna, ko da yake ba damuwa zasu zo wata rana” nan su mom suka gama tattaunawa, bayan sallar magriba Aziza ta cewa mom zataje gidan anty sultana, mom tace je ki tambayi mijinki, dabadin tana son zuwa gidan Sultanan ba da ta hakura, amma haka tayi jahadi taje part dinsa tace masa zataje gidan sultana, ga mamakinta yace mata ta shirya ya kaita, da murna kuwa suka shirya harda Azima, a tare suka je yiwa mom cewa sun tafi,mom tace
“Azima kin gayawa Almazeen cewa zakije?”
“A’a mom, to karki fita a gidan nan har sai kin gaya masa”
“Mom baya nan” Azima ta fada kamar zatayi kuka
A waya mom ta kira Almazeen ta gaya masa azima zasuje gidan sultana yace ba komai sai sun dawo, a tare suka fito suka shiga mota dan Nawaz na mota,gidan sultana ya kaisu, da sallama suka shiga sultana na saka turaren wuta ganin Aziza yasa ta saki ihu tana rungumeta cike da kewar juna, haka ma ta rungume Azima,nan suka baje a parlour suna hira sultana ta kawo musu ruwa da lemo nan aka hau labari, har sai da Nawaz yazo daukarsu karfe tara kamar karsu rabu, nan Nawaz suka gaisa da khalil sannan ya cewa su Aziza su shiga su tafi gida.
@@@@@@@@
Kamar yadda suka tsara da washe gari aka zo aka canza kayan parlour da daki aka saka sabbi,mom ce ta tambayesu ra’ayin kala, Aziza tace pick Azima tace purple, kai mom tayi kokari sai son barka Ma sha Allah, a ranar da yamma ta kira kawayenta aka zo aka raka Azima gidanta da babu nisa sosai a nan kd dan Mazeen yace ba zai kai Azima can kano ba, bayan an dawo daga rakiyar Azima mom da kanta ta dauki Aziza ta kaita part din Nawaz,kamar yadda tayiwa Azima Nasiha haka ta yiwa Aziza, daga nan ta tashi taje tayi kwanciyarta, mom na fita Aziza ta sulale kafin Nawaz yazo ta koma dakinta na da tare da Lami suka kwana, haka Nawaz yayi neman duniya bai ga Aziza ba.
@@@@@@
AL-MAZEEN kuwa yau yake ango dan dadin da baiji ba ranar yau ya shata a wajan Azima dan kuwa ta shayar dashi ni'ima, bai sarara mata ba ko kaɗan ita kam ta miƙa wuya tabi dama kuma sun sha gyara, da washe gari ma haka ta ga tattalin soyayya da kauna.
Aziza kuwa wasan boya suka fara da Nawaz a gidan, haka zai wuni bai ganta ba a kwana bai ganta ba, har aka kwashe sati daya yana neman hanyar da zai damƙeta zata gane bata da wayo dan ya ga alama ta rainasa.
@@@@@@
Yana kwance waya ta shigo masa yana dubawa ya ga daga outside ne, dagawa yayi nan aka shaida masa ana nemansu a america akwai wani course din da zasu sakeyi na shekara daya, wani tunani ne ya faɗo masa nan yace ya amince zasu zo, Almazeen ya kira ya shaida masa halin da ake ciki, Almazeen ma amincewa yayi, sannan Nawaz yaje ya samu mom da maganar sannan ya gaya mata zasu tafi da matansu, mom tace babu damuwa sai suyi musu passport yaushe ne tafiyar! Nawaz yace nan da sati daya amma ranar labara zasu tafi abuja a can za ayi musu komai, Allah ya kaimu mom tace.
Labari ne ya iske su Azima da Aziza zasu tafi america, wai! kirjin Aziza kamar zai faɗo kasa dan firgici, Azima kam an zama yar hannu.
Sai ranar da zasu tafi abuja Nawaz ya sa Aziza a idonsa, suna hada ido kwafa ya mata, mom ta rakosu har bakin mota tana musu adduar Allah ya tsare.
Awa biyu da rabi ya kaisu Abuja a ranar aka yiwa su Azima da Aziza komai kasancewar da kudi a kasa, da washe gari kuma suka ɗaga kasar waje.
@@@@
Sun isa lafiya inda sukayi waya da mom suka ce mata sun isa lafiya, gidan da suka sauka yanzu mai part biyu ne dan haka Almazeen ya ja matarsa suka nufi part daya, Nawaz ma hannun Aziza yaja suka nufi dayan, suna shiga bedroom ya tureta a gado ya bita ya danne yace
“Kin rainani ko? Yau zamu raba raini, ki tashi ki watsa ruwa yau zaki bani hakkina!” ido waje Aziza ke kallon Nawaz shi kuwa ya ki yarda ma su haɗa ido.