AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

 Kamar yadda yace a daren yau ya rafketa, taci bakar wuya a hannunsa dan kuwa bai tausaya mata ba, a ranar shima ya fanshe wahalarsa, sannan ya gaya mata irin buhun kaunar da yake mata.

????????????????

  Ma sha Allah haka rayuwarsu ta fara a kasar america, suna da sati biyu a kasar suka nema musu skull suka ci gaba da yi har da Azima wacce ita ɗorawa kawai tayi.


  Soyayya sukeyi mai tsafta mai cike da so da tattali, suna da wata hudu, a tare Azima da Aziza suka fara laulayin ciki, murna a wajansu Almazeen da Nawaz abun ba a cewa komai, kuma basu gayawa mom ba, a wannan wata hudun ne suka samu hutun wata daya suka ce zasu zo su gida nigeria akwai aikin da zasuyi, amma basu taho dasu Azima da Aziza ba sabida skull a can suka barsu.


 Sai da suka zo sukayi wata dayan nan kafin suka koma suka ci gaba da rainon ciki a tare, ko da wani lokaci suna tare da mom a waya da kuma sultana, yanzu damuwarsu ɗaya shine sunyi kewar Yankin kwana da Baffansu da Hajjarsu.


  Mom bata san cewa suna da ciki ba har sai da cikin ya shiga watan haihuwarsa tukunna ranar suna video call mom ta ga yara da ciki nan ta rufe su Nawaz da faɗa ta musu kaca-kaca kuma tace maza su dawo dasu su haihu a gida, da washe gari kuwa suka sauka a airport din abuja a ranar suka wuto kaduna, bayan dawowarsu da sati biyu Aziza ce ta fara nakuɗa inda akayi da ita ALWAZ HOSPITAL su Nawaz basu dawo ba suna can, amma jin labarin matarsa na nakuda yace ya bawa kwararrun likitocin asibitinsa umarni dasu tsaya a kan matarsa.

Bayan wahalhalun nakuɗa Aziza ta haifo yarta kyakkyawar gaske, murna a wajan mom sai son barka haka akayiwa baby hoto aka turawa babanta,Nawaz kamar ya b'ace ya gansa kusa da matarsa da yarsa, shi kuwa Almazeen yana adduar Allah shi ma ya sauke ta shi matar lafiya, Aziza ta haihu da kwana uku itama Azima nata haihuwar yace ga shi nan tafe, haka itama tasha wahala ta haifi yarta mace kyakkyawa, mom kamar tasa kanta a cikin fridge dan murna.

 Nan iyayen yara sukace a hada suna ayisa rana daya, mom tace to kawai ayi sunar ranar jumma'a.


 Ana gobe suna kawai sai ga Al'umma yankin kwana a kaduna, tsananin murna su Azima da Aziza kamar zasuyi hauka, haka suka rungume Hajja gagam a jikinsu, washe gari suna yarinyar Almazeen taci sunan mahafiyarsa Ɗahira amma za a dinga kiranta da AYRAH yarinyar Aziza kuwa sunan mom aka saka mata za a dinga ce mata AYZAH anyi suna lafiya an watsa lafiya sai dai fatan Allah ya raya mana Ayrah da Ayzah, duk yadda ubanninsu suka so zuwa Allah baiyi ba sai nan da wata daya, kafin lokacin yara ai sunyi wayo dama yaran yanzu da wayonsu ake haihuwarsu.


  Satinsu Hajja biyu nan ma da kyar mom ta sakasu sukayi sannan suka musu sallama suka koma.


  Haka Azima da Aziza suka ci gaba da rainon yaransu masu kyau dasu kamar iyayensu.


   Wata daya na cika su Nawaz suka dawo, ranar dasuka ga yaran basu iya bacci ba, dan murna.


 Haka suka ci gaba da rainon yaransu, sai da Ayrah sukayi wata uku kafin Allah ya sauki sultana ta samu ɗa namiji ranar suna aka saka masa suna Walid.


 Sai da su Ayrah da Ayzah suka yi wayo sosai kafin suka shirya tafiya yankin kwana harda sultana zasu tafi

@@@@@@

  Sadda suka isa yola sam ranar basu kama hotel ba, ga mamakin Azima da Aziza yankin da ake yanka a shiga jeji ya koma titi ɗoɗar, mamakinsu bai gama karewa ba sai da suka ga cikin yankinsu ya koma birni ga wutar nepa ga asibiti ga makaranta, wanda yasan yankin kwana a da yazo yace yanzu shine wannan za ace karya ne.


Basu gama sarewa ba sai da suka ga mota ya parker a wani hamshakin gida, ashe wai gidan Baffa ne, kamar an kashe fanka haka su Azima da Aziza suka fito a mota, Sultana kuwa sai dariya takeyi tana fadin

“Ohh wlh da ace banzo ba kafin ayi wannan aikin ai da na bata” da mamaki Aziza tace “dama kin zo Anty Sulty?”
“Eh mana munzo har dasu mom lokacin kuna america dasu Hajja sukazo sukayi kwana biyu a lokacin da za a cire kwalta” Nawaz yace to jawabi zaku shigo ko zaku tsaya surutu” ya fada yana daukar yarsa suka shige, da gudu Azima da Aziza suka rungume Hajja, bayan an gaisa Baffa ya shigo Azima da Aziza suna hada baki wajan tambayar Baffa wannan abun arziki, nan Baffa yake gaya musu ai Mazeen da Nawaz ne sukazo suka maida garin ya zama birni yanzu haka wasu yankuna suna zuwa yankin kwana kallo, duk ta sanadin Magaji Bawa da yaransa Azima da Aziza,harta jauro ya zubar da hassadarsa arziki yake ci, nan Baffa ya dinga gaya musu abun arziki dasu Mazeen da Nawaz sukayi, hakika sunyi farinciki sunyi murna inda son mazajen nasu ke kara ninkuwa a zuciyarsu, sun zama tamkar wasu super’star a yankinsu na kwana.

@@@@@@

 Sai dare can su Nawaz suka dawo suka cewa su Azima da Aziza su zo su tafi gidansu.

Ashe sun gina gida a garin madaidaci idan sunzo hutu nan zasu dinga zama dan zasu dinga zuwa yanzu a kai a kai lokaci zuwa lokaci.

  Cikin kuka ko wacce ta rungume mijinta tana gaya masa tsananin so da kaunar da take masa, kamar yadda suma mazajen ta bangarensu hakan yake, daga nan ko wanne ya dauki matarsa da 'yarsa sukayi daki.


  ????????????????

TAMMAT BI HAMDULILLAH

ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALLAH NA GODE MAKA DA KA BANI IKON RUBUTA WANNAN LITTAFI ALLAH NA GODE MAKA DA KA BANI IKON GAMATA lafiya, YA ALLAH ABUNDA NA RUBUTA DAIDAI ALLAH KA BAMU LADANTA,KUSKURENA ALLAH YA YAFE MIN.

INA TAYA YAN UWANA MUSULMAI MURNAN SHIGANMU WANNAN WATA MAI ALBARKA, ALLAH YA YAFE MANA YA AMSHI IBADUNMU, ALLAH YASA A MUYI LAFIA MU GAMA LAFIYA, DAN ISAR ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

SAI KUNJINI A SABON LITTAFINA BAYAN SALLAH DA SATI DAYA IDAN RAI YA KAIMU IN SHA ALLAH, SUNAN LITTAFIN AHLAN AKAN FARASHIN DARI BIYU.

BISSALAM.

MOMYN AHLAN
GARKUWAR MACIZAI????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button