AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AZIMA DA AZIZA COMPLETE HAUSA NOVEL

    Wazirin ja’i ya ce
“Ai ranka ya daɗe abunda muka jima muna nema ne, shine suka sakar mana shi yanzu,tun yaushe muke neman nasara a kan yankin kwana amma mun kasa samu sabida Magaji Bawa” wazirin fulanin ja’i ya karasa maganarsa yana murmushi, wakilin fulanin ja’i ya kuma cewa
“Ranka ya daɗe kar mu b’ata lokaci kawai mu amsa da cewa e mun amince da bukatarsu” girgiza kai garkuwan fulanin ja’i ya hau yi ya ce
“Shekara da shekaru ake ɗibi ba daɗi tsakanin yankinmu da yankin kwana, rana daya tak su aiko mana da sako su ce sun janye anya babu lauje cikin naɗi? A gaskiya ni ban yarda da yankin kwana ba, sai dai wani shirin kawai suke yi ta yadda zasu shafemu!” garkuwan fulanin ja’i ya karasa maganarsa yana haɗa rai sosai, sarki Jawo ya ce
“Bana tunanin haka! Idan ma kuma hakane karka manta muna da fidda kunyar gasa a yankin nan wato INNU MACIJI wanda a halin yanzu shi suke bukatar taimakonsa,Innu Maciji dai duk faɗin yankuna sun san shahararsa! Tunda shi ya lashe kambu na daya a gasar fidda gwajin macizai! Innu Maciji bai ci sunansa a banza ba! Tunda har aljanun maciji da mayu yana yaƙi dasu kuma ya ci nasara, dan haka idan muka tura Innu Maciji dan zuwa taimakawa yankin kwana kamar yadda suka bukata yaje ya dawo ya kake tunanin martaban da yankin ja’i zai samu tare da karramawa daga sauran yankuna?”

    Ajiyar zuciya Garkuwan fulanin ja’i ya sauke tare da kallon Sarki Jawo ya ce
“Ranka ya daɗe bana so mu manta da abu daya, a lokacin da aka raba kambu Magaji Bawa ya jima da sauke duk wata gab’ob’in baiwa da yake da shi, na san idan har zaka manta da tarihin Magaji Bawa da Tsohon sarkin ja’i ya baka ba zaka manta da sunansa da ya shahara a sauran yankuna ba, GWARZON DAFIN MACIZAI!! ka tuna?” Garkuwan fulanin ja’i na furta wannan kalma sai da mutanen da suke wajan suka firgita, Wakilin Fulanin Ja’i ya ce
“A gaskiya na so na yarda da maganarka Garkuwan ja’i! Me yasa Magaji ba zai yi wani abu a kai ba da zasu dinga bukatar taimakon yankuna! A da shi Magaji a ina ne bai yi taimako ba, gaskiya maganarka abun dubawa ce” Maga Isar da sako ya ce
“Amma shekaru ashirin Magaji Bawa ya ce ya daina duk wani abu na yaƙe-yaƙe da yake yi, bayan ya sauka ne shine aka naɗa Firi jarumin yankin kwana ko ba haka bane? Ni a tunanina da ace Magaji Bawa zai iya wani abu a kai da ba za a zo neman taimakon Innu Maciji ba har su russunawa yankin nan”

     “Amma dai kun san da cewa duk wata shahara da Innu Maciji zai yi ba zai taba kamo ko da tsilen takalmin Magaji Bawa ba ko?”

        Maga Isar da sako ya ce
“Ni dai bana tunanin haka gaskiya, da ace zai iya da ba zasu zo nan ba” Sarki Jawo ya ce “tabbas haka ne maganarka Maga Isar da sako, yanzu abunda za ayi,aje a cewa mai unguwa Sodangi akwai magana ta gaggawa, a biya a kira Innu Maciji, a rubutawa yankin kwana da cewa su tsumayemu zuwa gobe idan muka gama shawara da tattaunawa zamu tura musu da sako idan ma mun amince ko akasin haka” Sarkin fulanin Ja’i yana gama magana ya miƙe tsaye ya bar wajan.

     ????????????????

YANKIN KWANA

Maga Isar da sakon yankin kwana ne ya gama karanta wasikar da yankin ja’i suka aiko musu da shi, sarki chubaɗo ya ce
“Ba komai yau da gobe duk daya ne a wajan Allah, Allah ya nuna mana” mai Unguwa Ori ya ce
“Amma Allah ya kara maka yawan rai, anya yankin ja’i zasu yarda su taimakemu kuwa? Gani nake kamar su na neman hanyar da zasu wofantar da bukatarmu ne, tunda mun sanar dasu yankin jimo sun rasa jarman macizai, da mun sani da bamu rubuta musu da cewa an kashe jarman macizai ba” Arɗo ya girgiza kai ya ce
“Maganar duniya bata b’uya, gwanda dai da muka gaya musu gaskiya zai fi, balle kuma abu babba irin haka ya faru ace manyan yankuna basu sani bane? Ai hakan ma ba mai yuwa ba ce, dan naji ance yankin gangare da yankin jauro da yankin ulela da yankin nasare duk sunje yiwa yankin jimo ta’aziyyar jarman macizai”

      Sarki Chubaɗo ya ce
“Mu jira har zuwa goben muji sakamakon abinda zasu ce” Arɗo ya yi murmushin karfin hali ya ce
“Bana tunanin yankin ja’i zasu wofantar da bukatarmu! Abunda muka jima da sanina suna neman yankin kwana ta duƙa musu, sai ga shi laluri tasa duk taurin kan da fulani ke da shi mun russuna musu da muka ji uwar bari, dan muna da bukatar mu san waye ba mutum ba a yankin nan! WAYE MACIJI! a yankin nan! Dole azo ayi gwaji dan a fidda zargin juna a zukata, gwanda a nuna mana inda matsalar take mu kuma mu san ta inda zamu shawota”
Aka amsa da haka ne,nan dai suka gama tattaunawa suka ajiye maganar tasu akan su saurari yankin ja’i.

       Bayan an watse a fadar Sarki Chubaɗo Arɗo da Baffa ne suke tafiya a hankali su na magana kasa-kasa,Arɗo ya ce
“Magaji, fatan kana sa a ido sosai a kan su AZIMA DA AZIZA?”

      “E Arɗo ina iyakar bakin kokarina wajan saka musu ido, ita Azima baka iya gane gabanta,gwanda Aziza, gasu dai a tare aka haifesu amma halayyarsu ta sha bamban, a kwana biyun nan basu kula juna, Jumala sai korafi take yi a kan nayi musu magana ko me ya haɗa su, amma ban dauki hakan da mahimmanci ba sabida ba shi ya kamata na kula ba, kare rayukan yankin nan shine abu mafi mahimmanci” Arɗo ya gya ɗa kai ya ce
“Tabbas hakane, ba mamaki sun ɗan yi faɗa ne tinda ana samun irin haka” Baffa yace
“Eh nima haka nake tunani Azima bata da dadi ko kadan, Arɗo barin wuce gida”
“To a gaida Jumala da Azima da Aziza”
“Zasu ji” Baffa ya fada tare da yiwa Arɗo sallama.

     ????????????????

Tun safe Aziza ke rafin jimulo tana wanke kayan Hajja da na Baffa, Azima kuwa dan Aziza na rafin jimulo yasa ita bata je ba tana gida, abinci Hajja ta ɗora amma Azima ta hana abincin dahuwa, har la’asar tana zaune a kan tabarma kaba tana saƙe wani igiyoyi, Hajja ta kalleta ta ce
“Wai ni kam Azima wannan saƙe-saƙen da kikeyi na miye ne? Tun safe kike zaune a wajan ba sallar azahar bare la’asar ki tashi kiyi sallah” ba tare da ta dago ta kalli Hajja ba ta ce
“BANA SALLAH!” ????
Baki sake Hajja ta kalli Azima ta ce
“Kina fashin sallah ne?” kafin Azima ta bada amsa Aziza ta yi sallama da kaya a hannunta ta shige bukkan Hajja ta ajjiyesu sannan ta fito ta duƙa ta ce
“Sannu da gida Hajja”
“Yawwa sannu Azizatuna, kin dawo?”
“E Hajja na dawo”
“Ayya Aziza maimakon idan kin wanke kayan ki dawo gida idan ya bushe anjima a kwaso shine kika zauna har yamma a rafi ba tare da kin dawo gida ba? Ga shi haka kika fita ba ki ci komai ba” murmushi Aziza ta yi a ranta ta ce
“Idan na so zan iya wanke kayan nan na busar da shi a lokaci guda sabida karfin dafin da nake da shi,amma bana son hakan nafi son na samu ladar iyayena” a fili kuma ta ce
“Wlh ba komai Hajja bana jin yunwa ai”
“Allah ya miki albarka Aziza ke da yar uwarki, kinyi sallah ne?”
“Amin, E Hajja nayi sallolina a rafin jimulo ban bari lokaci ya shige ba” Hajja ta kalli Azima ta ce
“Azima kince baki sallah kina fashi ne?” da blus eyes dinta ta dago ta kalli Hajja ta ce
“Ni sallah ne kwata-kwata bana yinsa a rayuwata!” dam!dam!dam! Ƙirjin Hajja ya bada ta b’ata shuru tana bin Azima da kallo, da kyar ta buɗe baki zata yi magana amma Azima bata jira hakan ta faru ba dan kamar ƙiftawar ido ta tashi tare da tattare dogon igiyar da ta saƙa ta shige bukka, Aziza ganin yadda hankalin Hajja ya tashi da maganar da Azima ta faɗa ya sakata faɗin
“Karya take yi Hajja, kin san halinta bata damuwa da maganar da zata faɗi zai yi maka dadi ko akasin haka faɗi kawai take yi” sai a lokafin Hajja ta sauke ajiyar zuciya, Aziza ta ƙwaƙulo murmushi dan sallah kam Azima baya yi, ta ce
“Hajja ba a gama abinci ba?”
“Wollah Aziza ban san wani irin abinci yau nake dafawa ba, tin rana na ɗora kafin ayi azahar amma har yanzu ta ƙi nuna” shuru Aziza ta yi tana kallon tukunyar kasan na wani sakanni kafin ta ce
“To Hajja je ki ciki ki huta yanzu zan karasa”
“A’a Aziza yanzu fa kika dawo daga….”
“Ohh dan Allah Hajja ki je ki huta” murmushi Hajja tayi tana shigewa bukka, Aziza ta buɗe abinci ta ga rashin dahuwarsa yana da nasaba da sa hannu da Azima ta yi, rintse ido ta yi ta buɗe nan idonta ya koma fari sosai ta zaro harshenta ta hura wani hayaki a cikin tukunyan, nan kalar abincin ya canza alaman ya dahu, sannan ta rufe tana miƙewa tsaye ya yi dai-dai da shigowar Baffa da kuma fitowar Hajja daga bukka, sannu da dawowa suka masa, Baffa ya amsa yana zama a inda Azima ta tashi, kallon baƙin igiyar da Azima ta yi saƙa da shi ya gani guntun, dauka ya yi a fili ya ce
“Zaran saƙar dana? me yake yi a gidan nan? Wa ya kawo?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button