BA CIKI BANEHAUSA NOVEL

BA CIKI BANE

Dariya Boka yayi sannan yace
“Hhhhhhh komai zaiyi dai-dai ga wannan” ya d’auko wasu kulli guda hud’u ya mik’awa Hajiya sannan yace
“Wannan zata zuba mishi a abinci yaci wannan kuma zata turare gidan gaba d’aya yana shak’a shikenan wannan kuma duk lokacin da zasu kwanta tare ta shafa a duka jikin ta sai kuma wannan ta zuba mishi a ruwan wanka, idan duk kukayi wannan dai-dai to komai yayi ku tashi Ku tafi sai aiki ya fara aiki sannan Ku dawo ku biya.”

Godiya sukayi mishi sannan yace ko wacce Tayi ashar ta fita haka kuwa sukayi sannan suka fita.

Suna barin wajen Rahma tace
“Haba Momy ya za’ayi na zauna banyi sallah ba har tsawon kwana uku gaskiya bazan iya ba.”

Bige mata baki tayi sannan tace
“Ke rufe mun baki,
Keda kanki kin san ba abinda yakai cikar burin mu, idan kuma sallah ne idan kika nemi yafiya a wajen Allah ai shikenan.”
Ai kuwa ba k’aramin Rahma taji ba.
*(kunji jahilai)*

A hanya Momy duk ta fad’a mata yanda zatayi kuma zata had’a ta da Hanifa taje ta tayata girki da Gyaran gidan nata a haka har suka k’arasa gidan su.

Haka kuwa akayi Hajiya tasa Hanifa taje gidan Rahma ta tayata duk aikin kuma ta tabbatar tayi mata girki mai kyau.

Haka suka kama hanya suka tafi suna tafiya Hanifa tad’au aiki shara tayi sannan tayi moping sannan ta fad’a kitchen abu kamar wasa nan da nan tayi ta gama abinta ta jera su a dining.

Ita kuwa Rahma wanka ta shiga tayi sannan ta zauna ta tsara kwalliya wani atampa ta saka mai Green a jiki yayi mata kyau abinka da farar fata.

Bayan Hanifa taci abinci sannan tace ita zata koma gida magriba tayi.

Tana tafiya Rahma ta d’auko wannan maganin ta zuba a abincin Nawaf sannan ta kunna gaurashi tayi turaren wannan maganin nan a gidan gaba d’aya sannan ta zauna tana jiran shi.

Anayin sallan magriba Nawaf ya dawo gida da yunwar shi dan Yau a office aiki yayi masa yawa ko abinci bai ci ba.

Yana shiga yaji wani irin abu ya turnuk’e shi addu’a ya fara sannan ya samu saukin abin.

Cikin gidan ya k’arasa yaune ya sameta a parlour tana kallon TV shima zama yayi a kusa da ita yace
“Amarya kinyi kyau.”
Wani irin murmushi Rahma Tayi…………..

*Wayyo nikam nace Allah yasa dai kar…….*

 

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????

???????? *BA CIKI NA BANE!*????????

????????????????????????????????

*STORY WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*????✍????

*® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​*

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳ

ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*INA KUKE MASOYAN DUK ABINDA KAYI? GABA D’AYAN KU NAJI K’ORAFIN KU AKAN NACI GABA DA TYPING, TO INSHA ALLAH ZAN FARA MUKU CI GABAN SA WAD’AN DA SUKA KIRANI DA WANDA SUKA MUN MAGANA TA PC DUK NA GODE DA KULAWAR KU SOSAI KUMA INSHA ALLAH NIMA ZAN CI GABA DA KULAWA DA KU WALLAHI INA KAUNAR KU HAR CIKIN RAI NA*❤❤❣❣❣????????????????????????????

*INA KUKE MA ABOTA KARATUN NOVEL TO GA WANI HAD’ADD’EN NOVEL NA UMMY AYSHA MAI SUNA Maraicin so LITTAFI NE ME D’AUKE DA LABARI MAI TSUMA ZUCIYA ZAKUGA YANDA AKE SOYAYYA DA SAURAN SU.*????????????????????????????
*KAR KUBARI A BAKU LABARI!!!!!*

*Page 16~20*

Cikin gida ya k’arasa zaune ya sameta a parlour tana kallon TV shima zama yayi a kusa da ita sannan yace
“Amarya kinyi kyau.”

Murmushin mugun ta tayi sannan tace
“Thank you Hubby.”
Sake matsowa kusa da ita yayi sannan yace
“Gaskiya Yau za’a bani hakk’i na” ya k’arasa maganar yana mai shafa fuskan ta.

Shagwa6e fuska tayi sannan tace
“Haba Hubby kasan dai banida lafiya ko?”
“Sorry sweetheart wallahi ina cikin wani hali da bazaki gane ba please ki taimaka mun.” Ya k’arasa maganar cikin wani yanayi.
“To yanzu Ka tashi muje muci abinci ko?” Ta tambaye shi.
Da sauri ya mik’e yana cewa
“Ai kuwa kamar kinsan yunwa nake ji over.”
Itama mik’ewa tayi ta rik’e hannun shi sannan tace
“To muje na had’a maka abincin da kafi so.”

Haka suka rik’e hannun junan su suna tafiya.

Shi dai Nawaf baisan meye ya tada mishi sha’awar Rahma ba kuma gashi ta wani irin sonta ya kama shi.

Dining suka nufa abinci ta zuba mishi a plate sannan ta ajeye mishi a gaban sa sannan tace
“Hubby ga abinci kaci kafin ka gama bari na had’a maka ruwan wanka.”tana gama fad’an haka ta mik’e ta nufi d’akin sa zuciyar ta cike da farin ciki.

Shi kuwa Nawaf mamakin kansa yake dan baisan baisan me yake damun sa ba.

Tana shiga ta nufi toilet ta had’a mishi ruwan wanka sannan ta zuba wannan kullin maganin da Boka ya bata.

Dawowa tayi ta same shi yana zaune sai faman kwasar abinci yake yana sosa kunne da alamu dai abincin ya mishi dad’i sosai.

Zuwa tayi ta zauna a d’aya daga cikin kujerun sannan tace
“Hubby yadai ko magana babu?”

Murmushi yayi mata sannan yace
“Wallahi Sweetheart abincin yayi dad’i sosai ban ta6a cin abinci mai dad’in wannan ba” ya k’arasa maganar yana kai wani loman bakin sa.

Kallon ta yayi yace
“Ke bazaki ci abincin bane.”
Yamutsa fuska tayi sannan tace
“Wallahi bana sha’awar wannan abincin idan Ka gama Ka kaini restaurant naci abinda nake so.”

Murmushi yayi yace
“Angama Hajiya amman sai na gama cin nawa dan kuwa bazan iya bari ba.”

Haka suka zauna Nawaf ya kwashe abincin nan tas sannan yayi wanka suka fita.

Wani had’add’en restaurant ya kaita sai da taci abinda take so sannan ya d’auke ta ya kaita supermarket yayi mata shopping kaya kala-kala mai yawa sosai sannan suka koma gida.

Direct d’akin Rahma suka wuce dan shi da abinda yake damun Sa.

Suna zuwa suka canza kayan jikin su sannan suka haye gado.

Wasa yake da ita sosai sai da ya tabbatar tana buk’atar sa sannan ya fara k’ok’arin abinda yake ransa.

Da sauri ta mik’e ta nufi toilet dan aikata abinda Boka ya bata.

Wani magani na gani tana sawa a gaban ta tana gamawa ta dawo ta kwanta.

Yana matsowa kusa da ita yaji wani abi yana zagaye shi.

Addu’a ya fara sosai dan ko wacce tazo mishi yi yake.

Yana cikin wannan addu’a barci ya d’auke sa mai nauyin gaske.

Rahma da take kwance tana jiran Nawaf sai gani Tayi ya kwanta yana barci.

Da sauri ta mik’e ta k’arasa inda yake kwancen tana dukan sa tana cewa
“Hubby please Ka tashi mana kai fa nake jira.”

Ganin barcin gaske yake ne yasata cewa da karfi
“Wallahi baka isa ba katashi wallahi sai kayi abinda Ka fara baka isa ba” sai kuma ta fashe da kuka.

Haka ta kwana ko barcin kirki batayi ba.

Sai da asuba Nawaf ya tashi da sauri ya mik’e ganin sa a d’akin Rahma ba kaya.

Da karfi ya furta “subhallahi!
Me ya kawo ni d’akin nan!”
Kayan sa ya d’auka ya saka sannan ya zauna a bakin gadon sai a lokacin ya tuna abinda ya faru jiya daddare, dafe kan shi yayi dan wanin ciwo yake mishi, addu’a ya kama ai kuwa nan da nan yaji ya dawo dai-dai.

Tashi yayi yaje d’akin sa yayi alwala sannan ya tafi masallaci shine bai dawo ba sai da gari ya waye.

*PLS KUYI HAKURI DA WANNAN BA YAWA*

 

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????

???????? *BA CIKINA BANE!*????????

????????????????????????????????

*​STORY WRITTEN BY​*
*​MOMYN MUSADDIQ​*????✍????

*DEDICATED TO MY FANS*

*MASOYA KUYI HAK’URI KUYI HAK’URI NASAN NAYI LAIFI BUT AKWAI DALILI BIKI MUKAYI RANAN BIKIN KUMA MAHAIFIYAR AMARYAR TA RASU SO ABIN SAI A HANKALI KUMA MAK’WAFCIN MU SHIMA YA RASU SHIYASA KO ONLINE BANA HAWA INA FATAN ZAKU MUN AFUWA*????????????????????????????????????????❣❣❣❣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button