Labaran Kannywood

Wa Yafi Kudi Tsakanin Nafisa Abdullahi Da Naziru Sarkin Waka?

A yau zamu duba rayuwar wasu Jaruman Kannywood, inda zamu kwatanta mawaki Naziru Sarkin Waka da Jaruma Nafisa Abdullahi don sanin, shin wa yafi kudi a tsakanin su.

 

Kowa yasan cewa harkar Kannywood harkace wadda ake samun kuɗi sosai da ita, domin kuwa munga yadda sana’ar ta rufa wa jaruman da suka ɗauke ta sana’a asiri, hakan yasa har wasu daga al’ummar gari suke sha’awar wannan harka, saboda ganin irin alfanun da ake samu a wannan harka.

 

To yanzu zamuyi bayani tsakanin Naziru Sarkin Waka da Nafisa Abdullahi, inda zamubi jaruman daya bayan daya muyi bayani akan su, bari mu fara da Nafisa Abdullahi.

 

NAFISA ABDULLAHI

Nafisat Abdullahi

Nafisa Abdullahi tsohuwar jarumace wadda anyi yayin ta sosai kuma ta taka leda a sanda take lokaci har zuwa yanzu, sannan jarumar ta samu makudan kudade a wannan masana’anta ta Kannywood, hanyoyin da take samun kuɗi sun haɗa da:

 

Yin fim shi kansa, kamar yadda take fitowa a matsayin jaruma a fim a biya ta.

Yin tallace tallace na kamfani, Nafisa Abdullahi ta kasance jaruma wadda take yin talla na kamfanunuwa da dama daga cikin su akwai babban kamfanin nan na Pepsi da wasu kamfanin da dama.

Kasuwanci: ba iya fim da talla kawai jarumar keyi ba harda kasuwanci, domin kuma itace mamallakiyar kamfanin NafCloset kamfanine na siyar da kayan sawa da takalma da jakun kuna na mata, da kuma kayan kwalliya da sauran su.

Darajar Nafisa Abdullahi tana kaiwa,

 

Net Worth $500k

 

Naziru Sarkin Waka

Naziru Sarkin Waka

Nazir M Ahmad mawaki ne a masana’antar Kannywood jaruma a wani bangaren, mawaki ne wanda akayi yayinda kuma ake yayin sa a harzu haka, kuma yana taka leda a matsayin jarumi a fim din LABARINA, Kuma yana daya daga cikin jaruman da keda maƙudan kudade a masana’antar, Sarkin Waka yana samun kuɗi ne ya hanyoyi kamar haka.

 

Waka: hanya ta farko da Sarkin Waka yake samun kuɗi ita ce waka, domin kuwa Sarkin Wakar ya kasance yana yiwa Sarakuna da yan siyasa waka, sannan kuma yanayin wakokin finafinan a wasu lokuta, wannan ita ce babbar hanyar da Sarkin Wakar yake samun kuɗi.

Fim: Kamar yanda muke gani Sarkin Wakar ya fara fitowa a fim duk da ba shine lokacin sa na farko ba, kuma dashi ake shirya shirin LABARINA, tabbas Sarkin waka yana samun kuɗi ta hanyar fim.

Dina: Naziru ya kasance ana gayyatar sa dina ko fati idan ana daurin aure, yanayin waka kuma a biya shi.

Akwai wasu hanyoyi da dama wanda Sarkin Wakar yake samun kuɗi bayan wadannan.

Darajar Naziru Sarkin Waka tana kaiwa,

 

Net Worth $650k

 

Ku kalli wannan video don samun ƙarin bayani.

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button