BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 78

78

………Wannan harmutsi da dangin mijin Aysha suka tarar yasa suka dakatar da ɗaukar amarya, acewarsu ai basu san haka uwar amaryar da danginta suke ba. Ƙololuwar tashin hankali Mommy ta sake shiga, har takai ta yanke jiki ta faɗi itama dai sai da aka kaita asibitin. Gwaggo halima dake dariyar mugunta ta tafi gida ranta fes Mommy da Gwaggo a bala’i, sai dai kuma mahaifin Fadwa ya hana mata koda shiga gate, yace Fadwa kaɗai ce ƴarsa, itama zai bata mafakane har tai idda saboda karya salwantar da rayuwarta a cigaba da samun bara gurbi a cikin al’ummar musulmai. Amma ta sani bazata taɓa jin daɗi ko ɗigon farin ciki a gidansa ba. Rikicewa Gwaggo Halima tayi, kamar yanda Fadwa dake kuka rirus dama dan da ƙyar Gwaggo Halima ta jawota suka tahonan saboda ido rufe take neman Shareff amma taƙi ganinsa. Masu aiki yasa suka shigo da ita, Gwaggo Halima kuma ya tabbatarma masu gadi ko hanunta ya taɓa masa gate abakin aikinsu. A karan farko itama ta fara kuka, dan a zatonta koda yay sakin guda biyu zai haƙura ya barta ta cigaba da zama cikin ƴaƴanta har a sasanta. Sanin da yay mata zata iya ƙin nufar gida ya sakashi turata a mota da kansa yaja motar ya maidata gidan su Daddy da tuni ƴan biki sun fara watsewa, ba kowa na ɓangaren Mommy. Na ɓangaren Mom kuwa da dangin su Daddy zama daram wasuma shirin tafiya dinner ɗin Khaleel da amaryarsa suke. Dan su Hajiyar Sudan sun shiryama wannan biki kwarai da gaske….

       Komai ya hargitse, komai ya rikice. Burin Gwaggo na watsa biki wani yankinsa ya tabbata. Domin kuwa akan bigire na duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka ake. Ita dake amsa matsayin suna uwar daba tana can asibiti ƙafa a ragargaje batama san inda kanta yake ba likitoci sun rufu akanta. Manyan dodannin fadarta su Mommy sun masifar tsanarta fiye da rayukansu a yanzu. Dan kuwa Mommyn da kowa kema kallo matsayin ƴarta da zata iya zama magajiya a gareta na kwance bisa gadon asibiti jininta yay ƙololuwar hawa har yana son zarce abinda ba’a fata. Tana da saki guda biyu a kanta, igiya daya ce kacal ta rage mata a yanzu, kuma Daddy ya tabbatar musu daga asibiti su wuce da ita karta sake dawo masa gida. A daren daga gidan angon Aysha takardar saki ta iso a cewar iyayen ango ɗansu bazai rayu da ƴar mace ba. Wannan al’amari yayi matuƙar ƙona zuciyar su Daddy har Abie na tabbatarwa sai ya kaisu kotu, da ƙyar su Abba suka lallashesa. Gwaggo halima data ɗauki Gwaggo tamkar uwarta mahaifiya a yanzu babu wanda tafi tsana a duniya sama da Gwaggo, a sanadinta ɗiyarta mafi soyuwa a gareta ta rasa ciki ta rasa aurenta, ita a karan kanta ta rabu da ƴan uwanta shekara aru-aru a dalilin huɗuba ko muce tarbiyyar Gwaggo. Ta rasa igiyoyin aurenta da ƴaƴanta a cikin abinda bai gaza awa shidda da barinta gidan mijinta cike da fatin ciki ba.
     Yayinda Aysha itama ke can tana rusar kuka tamkar ranta zai fita, dan kuwa ta tabbatar alhakin mahaifiyarta da kakartane ke bibiyar ƙaddararta, a ranar da aka ɗaura mata aure a ranar miji ya saketa ko gidansa ba’a kaita ba. mijin data ɓata tsahon shekaru tana mutuwar so da ƙauna.
         Haka zalika Fadwa celeb…. Wadda ke ganin ko ta tashi a rayuwar da ita a karan kanta bata taɓa gundurartaba balle kallonta a juye. Shareff shine dukkanin farin cikin duniyarta, da sonsa ta rayu da shi ta horu, a rana ɗaya dalilin makircin ƙawayen data ɗauka babu yasu a duniyarta da cigabanta ta rasashi. Auren mahaifiyarta da aka ƙulla tsahon shekara talatin yau ya girgiza shima a dalilin wadda suke kallo gunkiyarsu da bayan horon tarbiyya ga uwarsu suma akan zaren tarbiyyar tata suka horu…..
      Shareff da komai ya ƙwace masa a wannan gaɓar tunaninsa yama rasa ina zai kama ko samun mafaka, sai dai ya jure, ya danne wajen tattare hankalinsa kan matarsa da jikinta yay ruɗewar da daren sai da Dr Jamal yazo ya sanya mata ruwa….,  ya kuma saka Fharhan a daren kaima su Sima, Siyyah, Amal, Bibah ƴan sanda suka cafkesu, tare da doctor ɗin dayay aikin.
    Abba, Daddy, Abie, aunty Mimi. Mamakin Gwaggo da ɗunbin al’ajabinta ya hana zukatansu bugawar gaggawa a ƙirazansu. Sun rasa wane aji  na duniya ya kamata sunan Gwaggo ya fita, dan a iya hasashensu sun gagara kama minene dalilinta na duk aikata waɗannan abubuwan?. Kenan akwai abubuwan da suka shuɗe da yawa a baya dake buƙatar nazari mai faɗi da neman ba’asin dalilin aikatashi ko ganinsa a aikace. Sunyi ta mazan bin su Baba Ibrahim asibiti, inda har dare ya raba suka dawo gida babu wani bayani akan jikin Gwaggon likitoci dai sun rufu a kanta sunata faman kaikawo….

    WASHE GARI.

           Sai a yau asabar zuri’ar MD Shareff suka sami ganin Gwaggo, sun fara shiga ɗakin da aka kwantar da Mommy itama bisa matsawar Abie suka dubata, inda acan suka sami Shareff da Maheer tare da ita. Basu jimaba suka fito, Mommy da abubuwa da yawa ke cin ranta musamman sakinta da Daddy yayi ta taso ta biyosu, duk yanda su Shareff sukaso dakatar da ita taƙi yarda da hakan. Hankalinsu ya tashi da ganin jikin Gwaggo, dan ƙafarta tayi wani irin mahaukacin kumbura daya ninka jikinta biyu, gashi an yanketa daga gwiwa zuwa ƙasa dan can ɗin yayi ragargajewar da bazai ƙara aiki ba. Sai kananun ciwuka da ba’a rasa ba. Da ƙyar take iya amsa musu, sai dai abin mamaki idonta a soye babu ko alamar hawaye. Bayan sun jajanta da ɗaukar kusan mintuna goma sha biyar a ɗakin sukai haramar tafiya. Muryarta a ɗashe, amma hakan bai hanata fita da kaushi ba ta dakatar da su…
      “Na rikeku na muku gata fiye da uwar data haifeku, amma a dalilin kanƙanin abu kuke nuna alamun juyamin baya Muhammadu. Bazan hanaku ba, sai dai ku sani bazan yafe muku wahalar dana sha a kanku ba”.
      “Bakece zaki ƙi yafe mana ba, mune bazamu taɓa yafe miki ba Hindatu…”
    Muryar Gwaggo Halima ta ratsa kunnuwansu a bazata. Su dukansu suka juya suna kallonta da mamaki, dan kuwa babu lallashin da basu mata ba danta biyosu tace bazata ba. Ta cigaba da takowa firingau-firingau dan a kwana ɗaya duk ta sususce ta fita a hayyacinta tamkar ba halima ƴar gata ba. Ta ƙaraso gaban Gwaggo tana mai share hawayenta. “Hindatu kamar yanda na faɗa mune bazamu yafe mikiba annamimiya azzaluma. Musamman ni nan Halima. Hakama iyayenmu dake kwance a cikin kabari, da sunada damar da zasuyi magana sautin yaje cikin kunnuwanki da sun nanata miki kalmar ALLAH ya isa fiye da sau dubu. Kinga wannan ƙafar taki da aka yanke, ba itace kaɗai ƙarshen azabar da zakisha a duniya ba. Yanzu kika fara gani, bayan ɗanɗanar ɗacin rashin haihuwa na shekaru sama da sittin da kikai a duniya, yanzu zaki cigaba da fuskantar raɗaɗin azaba ne mai muni tsinanniyar tsohuwa mai zubin ƴan wuta…….”
     “Ke ce dai mai zubin ƴan wuta…”
Cewar Mommy a hasale. Dariya Gwaggo Halima ta sanya. “Ke kumafa? Maza je kiji da kanki shasha kawai. Hawan jini da zawarci ma sun ishi rayuwarki ƴar wahala, sannan kema a gurinta baki tsira ba”.
    “Hahaha garama ni, kuma koba komai zuwa yanzu na tabbatar miki Shareff jinina ne tunda gaki a zawarci ƴarki a zawarci. Kuma yanda ya saki Fadwa itama Anaam sai ya saketa dan bazai zauna da zuri’ar waɗanda basu san hallaciba. Ƴar dukiyar da akaga ya tara akemawa to babu mai cinta har kai uban nasa”.
          A karan farko Daddy ya ɗago yana kallon Mommy, amma sai kafin yace wani abu Abba ya cafe murya a kausashe.
     “Mu bamu kasance marasa halacciba Nafisa. Wannan tsohuwar dake da kika rayu a gidanmu matsayin agola kune marasa halacci, kuma dukiya da kike takama Shareff ya tara bara na buɗe muku zancen yau, kaso biyu bisa ukun abinda kuke ganin Shareff ya tara na Usman ne…….”
     “Please Yaya Abubakar ba wannan gaɓar mukeba…”
   Abie yay niyyar katse Abba. Amma sai Abban ya fisge jikinsa. “Barni Usman, gara wannan mahaukaciyar tasan ANNABI ya faku. Duk da ƙulle-ƙulle datai domin ganin ta raba tsakaninku da Usman hakan bai hana ka cigaba da tallafa rayuwarsa ba, har take iƙirari da fariyyar dukiyar ɗanta. ki shiga hankalinki kuma kisan mikikeyi, daga ke har uwar taki, sakamako kuma yanzu kuka fara girba, dan wlhy Gwaggo alhakin iyayenmu kaɗai bazai barki sake jin daɗi ko farin cikin rayuwa ba. Tur da masu irin halinki na annamimanci da hana zaman lafiya a cikin zuri’a. ALLAH zai saka mana matuƙar sakayya a ranar da gaɓoɓi zasuyi magana madadin bakuna”.
      Tuni Mommy da kanta ke bada wani yuuuu na haurawar jininta sama ta dafe gadon da Gwaggo ke kwance. Kallon Shareff take cike da son ƙarin bayani. Lips ɗinta na rawa. Kansa ya jinjina mata tun kafin tace komai. “Mommy abinda Abba ya faɗa shine gaskiyar magana. Dukiyar Abie ce ni nawa basu wice kudin siyan ruwa ba a cikin taron biki”.
      Wata irin ƙara Mommy ta saki da faduwa ƙasa daɓar, Gwaggo ma tuni gadon da take a kai ya fara jijjigar shiga a tashin hankali. A halin da take ciki da dukkan ƙarfin halin nata Shareff ɗin shine kawai gadararta a yanzu, dan ko maganar aikin da ake faɗar za’ai mata na ƙafarta ta gama sawa a ranta ko kowa ya gujeta suna da Shareff ai. Ashe-ashe abinda sukema gadarar ma ba nasu bane. Da tasan haka bazata taɓa yarda taima su Abba hakaba. Da ta cigaba da musu fuskarta ta tun ƙuruciya. Amma yanzu ta tabbatar bakin alƙalami ya rigada ya bushe kuma….
     Cikin ƙanƙanin lokaci duk sukai waje, hatta Shareff da Maheer ji sukai bazasu iya zama ba, dan dama tsananin kunyar su Daddy sukeji saboda abin kunyar da kakarsu ta jima tana tafkawa da mahaifiyarsu duk da kuwa akwai Gwaggo Halima tare da su……

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button