Labarai
HOTUNA: Kiristoci sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da kisan Deborah

Wasu Kiristoci sun fito kan tituna suna zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da kisan da aka yi wa wata dalibar Sokoto, Deborah Yakubu, bisa zargin batanci ga fiyayyen halitta.
A baya dai kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi kira ga Kiristoci da su yi zanga-zanga a ranar Lahadin yau dan kisan Deborah.
A ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu ne wasu fusatattun mutane suka jefe ta da duwatsu tare da kona gawar ta a harabar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari bisa zargin ta da aikata mummunan kalamia ga fiyayyen halitta.
Hotunan zanga-zangar da aka yi a jihar Oyo da Badore Ajah a Legas
[ad_2]