Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 16

*????????16*

….”ko mutuwa zakayi bazan barmaka zee baby ba saboda na fika sonta da kaunarta nima itace rayuwa wlh idan narasata mutuwa zanyi dan haka na hadaka da girman Allah karka sake mun wannan maganar hadeem ya rike Mahabeer yana bashi hakuri Ahmed ya dago cike da mamaki yana kallon Mahabeer dafe da kumci ” bro kayi hakuri bansan haka zaka dauki zafiba amma iya gaskiyata na fada ina sonta ya juya ya fice zama Mahabeer yayi dabas yana dafe kansa dan ransa yayi mugun baci “haba Mahabeer kayi hakuri mana banji dadin marin da kamasa ba abokin Dr nefa aya daya suke rabawa cikin zafi Mahabeer yace” an maresa din ni bakaga irin marin da yamunba to wlh idan kaga nabar zee tana tare da wani saide idan mutuwa nayi dan wlh itace rayuwata nima ina mugun son kanwata ” yi hakuri bari tada jijiyar wuya yayanmu niko shawara zan baka wacce zata saka hankalinka ya kwanta? kallonsa yayi ” ina jinka wace shawarace nifa banida shakar zeena tana sona? ” eh duk da haka ita zee din ce zakasa tamasa maganar wlh mutikar yana kaunarta to zaiso duk abinda ta bashi inaso ka fada mata duk yanda kukayi dashi kace mata cikin yan matan gidanku ya zabi gudu mutikar yana sonta zai zaba ” kai haba ina. sai kace muna nema maraba dasu wlh sam ba yardaba Hadeem ba yada bai ba ya shawo kan Mahabeer yaki karshema yace zai sa amatso da auran kusa koko adaurashi ajirayi biki dole ya hakura dan ya dauki zafi sunanan har lokacin zuwa juma’a yayi suka tafi dan shi Hadeem ranar juma’a karfe shadaya yake barin Office sai monday Hadeem abokin mahabeer ne tun suna yara tare sukayi karatunsu bashida babban amini sama dashi basa boyewa juna sirrinsu zumunci suke har iyayansu shine mijin Zainab kanwar su Dr Sardauna sunyi aure shekara daya da ta wuce cikin so da kaunar juna shima nan cikin unguwar kofar marusa lowcos yake saide ba layi daya sukeba Dr Sardauna yana fitowa daga tiyata ya sake duba marasa lafiyan da ya kamata ya duba Ruma duk inda yayi tana binsa da idanu ita da Amina Office d’insa ya koma yayi wanka zuwa juma’a sai uban kamshi yake zuba ya dauki wata darduma mai masifar kyau da ado ya kwashe wayoyinsa ya dauki makullan motarsa ya fito ya murzawa Office dinsa key ya nufo harabar hospital din cikin takunsa na jarumin Namiji maiji da kudi da kuma yarinta ga uwa uba kyau da ilimi gashi da kwarjini

kansa ya daga sama yana kallon yanayin garin hadarine sosai garin yayi duhu parking space ya nufa, motarsa ya bude ya shiga ya mata key da karfi ya fizgeta yayi bakin get aka wangame masa get ya fice saman titi ya harba motar sosai yake gudu dan sam bayansan cida Allah ya jarabesa da tsoron cida da tsawa sama duk jarumtarsa idan yaji cida ko tsawa sai ya firgita tun yana yaro haka Allah yayishi da tsoron tsawa akwai wani lokaci yana karami da wannan bakar zuciyar tashi ko mai ya hadosu da Mahabeer ya fasa masa, kai ranar da hadiri agarin ghaisha ta korosa, waje dan sunsan bayasan tsawa yana daga kofar parlo akayi wata, irin walkiya da tsawa, mai sautin gaske nan take ya fadi sumamme tun daga shi Daddy ya hana tamasa horo da ruwan sama ko a saudia lokacin yana karatu haka Faisal Abbun zainab yake shan fama dashi idan yazo gidan idan ana ruwa ko masallaci baya zuwa itama zee baby haka take mugun tsoron karan ta sama, haka yarika sharara gudu har ya isa babban masallacin kofar soro motocine ko ina burjiki motar Mahabeer ya hango daide can yaje yai parking ya fito ya rufe motar ya, fito yanufi cikin masallacin duk ya fara ciki duk da sauran lokaci,

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Zaune take gaban wani malam boko jibgege bakikirin dashi kallo daya zaka masa, kasan imani bai ishe saba ” kafi madubi ya zakamun haka kace baza’a taba saka masa, ranaba batare da yarinyataba zaka wargaza soyayyarsa wacan yarinyar amma abun sai kuratowa yakeyi babu wani Abu da ya sauya yarinyata tana fama da sonsa amma har yanzu bata san nufu naba maganar khadija ma da Abdulmutallab babu wani canji har yanzu darajarta tana nan kamar. da kace zan malakesa amma shiru babu wani sauyi duk inada kimata agunsa amma ai nagaya maka so nakeyi ya dawo tafin hannuna shida wannan dan iskan d’an NASA mai girman kan tsiya khalisat ta juyashi kamar waina atanda kecewa kafi madubi yayi da dariya wata irin muryasa maras dadi yace” zo kiga ikon Allah banace kibani lokaciba amma kin fiye gagawa ni idan nace zanma aiki to ka jira ko nan da shekarane zai ci saide idan mutum bashida rabone kawai ya kalli Asiya ko ba haka bane?? ” hakane Nice kat kuwa tunda na raba mijina da ahalinsa wani katon madubi ya janyo bayan wata kujera yayi surutansa da sada barunsa ya ajiye gabanta ya kira sutanta da karfi” Mariya Mariya Mariya har sau ukku tana amsawa afirgice dan saida dakin ya amsa ” matso kigani matsawa tayi gaban kafi madubi idanu ta zaro gabanta na faduwa jikinta na kerrrma zufa na keto mata cike da mamaki take nuna madubin tabbas Sardauna ne duk sam fuskarsa taki fitowa sai katuntakarsa amma mashakurah gatanan sai khalisat sai wata itama ba’a ganinta sosai amma taganeta tayi tunanin me yasayota cikin sabgarsu tunda batakawo sunanta ba” kafi madubi kana nufin gurina zai cika khalisat zata auri Faisal ta mallakeshi mu yashe dukiyarsa kamar yada nake burin yashe mahaifinsa kuma da gaske wannan abun ya faru da matarsa da zai aura auran zai dawo ka’ diyata idan asiri ya tonu Alhmdllh nagode Allah naji dadi yauwa sai wata yar banzar yarinya koren makkah ta taba kamani ina waya taso tonamun asiri nakiraka na gayama to dan Allah ayi kokarin matar da ita maganar bincike ya fara ” nifa Al’amarin yarinyar bana ganin kominta wlh bana gani kamar yada kinga fuskar Faisal bata fita amma dubar ya nuna shine ko dan yanayin kakuntakarsa dan haka kibarta nasamata shashatau bazata iya fadiba amma bana ganinta sam zan gindaya miki sharuda mutikar kinyisu to ki zuba idanu kiga ikon Allah yanzu kije bayan kwana goma shadaya ki dawo kafin lokacin na hada magungunan cikin farin cikin tamasa godiya jikinta na rawa ta bude bakin jaka ta sallamesa suka tashi suka tafi lokacin da suka fito daga dajin har an fara ruwa,

*********

Bayan sallah juma’a Dr Sardauna suka nufo gida shida Mahabeer kowa amotarsa, garin yayi bakikirin an fara ruwa gidu yayi sosai yana isowa gida ya jima yana honr kafin mai gadi yaji ya bude masa ya waiwaya bai ga mahabeer ba parking space ya shige yayi parking jiran Mahabeer yayi ya shigo su tafi part d’insu shiru bai zoba tsaki yaja ya bude motar ya fito ganin part din Daddah kusace jiyake kafin yaje tasu cida za’ayi wuff ya shige part d’in Daddah parlon ba kowa tunawa yayi suma masallaci suke zuwa maybe basu zoba Azimi mai aiki tana zirganiya dan bata gama girkiba ” inna ina su Daddah?? ” ai basu isoba sai ni daya kai ya kada ya nufi bedroom Daddah wacce dama mafi akasari idan ana ruwa can yake buya can kurya ya shige ya cire takalminsa ya Haura saman gadon mai girman gaske baya wani ganin gaban gadon saboda duhun gadon akwai rumfa shiyasa, ba haske wayoyinsa ko suna mota kwanciya yayi ya done kunnesa ya tura hannusa daya cikin gashinsa yana fatse ruwan da ya fara jika masa gashi kamshi yakeji mai mutikar dadi na ziyartar hancinsa duk atsorace yake ya kudundune guri guda ruwa akeyi sosai kamar da bakin kwarya zee baby cikin bacci takejin kamshinsa na ziyartata sai kara bude hanci takeyi tana nemo kamshi wata irin tsawa aka saki habawa ba Sardauna ba zee baby da take barci sai gata zaune tana kwarara ihu daide lokacin Dr Sardauna shima ya kwarara ihu jin mutum kusansa ya lalubo ya rumgumeta da karfi ya kwantar da ita yaja musu bargo dan har yanzu tsawar akeyi cikin rawar murya tace ” yaya mahabeer boyeni wlh tsoro nakeji wayyo Allah kara shigar da ita jikinsa yayi ya rufesu itama kara makaleshi tayi jikinta na rawa ta fara kuka muryar Mahabeer ya mata magana” my zee babyna yi shiru wlh nima banason tsawa karkiyi kuka kinji ya fada ashagwab’e” to ka toshemun kunne na kara rumgumeta yayi gam yana shafar lalaunsan gashin kanta jitayi kamar yau mahabeer ya kara girma kamshinsa irin na Dr Sardauna baki ta bude zatayi magana aka sake tsawa ihu sukayi atare suka rukumkume junan su itama hannuta ta dora fuskarsa tana shafawa ” yayana meyasa mukejin tsoro atare muyi maganin tsoron ka likemun kunnena nima na like maka kunneka

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button