FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 21

PG:21_

======
     
Waheedah dai taja tunga a tsaye ta zubawa sarautar Allah idanu. Idanunta nata wulqitawa tana mai karade gidan da kallo. Ai gaba daya yadda Umman su ke tsara haduwar gidan. Sai taga a zahiri ma yafu kawatuwa sosai.

Ga bishiyu da suka ingattu da albarkacin ganyayyaki sunata kadawa. Wata iriyar iska mai ratsa jiki ce ke busawa ahankali

Ya yinda Ahlaam da Nadra ke gaisawa sun manne da juna suna farin ciki. Can sai lokacin da wata mata ta fara zuro kafafinta dake sanye cikin takalma masu laushi da kyawu.

Can sai ga sandar da take dogarawa nanma ta zuro ta kasa. Kafin direban ya sake wangale kofar motar. Dattjuwar ta fito cikin riga da zani na atamfa. Ya yinda mayafin ma atamfar ce tayi mayafin da shi.

Wuyan ta me dauke da wuri. Haka ma dankwalin kanta irin masu santsinnanne. Sai hannunta da yasha lalle samfurin dungulmi.

Fuskarta kuma da baqin gilashi. Wanda tun wani aiki da akai mata a idanun take saka baqin gilashin. Sakamakon hasken rana da qura kan iya dawo mata da aikin danye.

“Ummimi…!!!” Nadra ta fada da sauri. Tana mai rungumar kakarta su.

Wata dattjuwa yar kyakkyawa, Bata cika tsawo ba. Kuma sam batada jiki. Kyakkyawa ce. Kana kallonta kasan ta hada jini da fulani..

Yayin da wata mata a gefen ta ke riqe da jakar ta. Nadra ta tafi d sauri ta rungume ta tana farin ciki

“Sannun ku da zuwa Ummimi..”

“Sannu ka dai Nadra.”

Ta sake rissinawa tana gayshe ta. Sannan ta miqe. Ummimin na ta sanya mata albarka.

Suka rankaya baki daya suka yi sashen Hajia Aisha. Uwargidah kuma mata ta farko ga farfesa Adams.

Waheedah na biye dasu a baya , Tafiya kawai take salolo. Zuciar ta nata rada mata kan tabbas Nadra ta manta da ita.

Ai kuwa Bata karasa tunanin ba ta tsinkayo muryar Nadra. Suna tafe itada Ahlam.

“Na’am… “

“Afuwan na bar ki. Wajen su kakar mu naje. “

“Bakomi yar uwa.”

“Sunana Nadra. Ke fa?”

“Wa…. Hee…dah” Ta fada a rarrabe.

“Sunan larabawa kuma yan gayu ba. Well ni kuma sunana Ahlam . Nadra da ni first cousins ne.”

“Ah masha Allah …” Cewar Waheedah.

A tsakiyar su suka sakata. Suna tafiya a jere. Waheedah sai raba idanu take. Tana mamakin saurin sabo irin na su. Uwa uba kuma basa kyankyami na ganin ita din ba wata bace. Ba tsarar gogawar su ba ce .

Sashen Barr. Aisha suka shiga. Da sauri ta taho cikin farin ciki da girmamawa wa ta tarbe su. Ta rungume Ummimi bakinta tamkar zai wage .

Ta rissina har kasa ta gaishe da ita cikin girmamawawa. Ummimi ta amsa da fara’a. Ta zauna akan kujera mai cin mutum uku .

Nan da nan su Ahlam suma suka shiga gayshe da Barr. Aisha. Ta amsa tana kiran sunayen su. Waheedah ma ta gayshe ta .

“Ke kuma ya sunan ki?”

“Sunana Waheedah “

“Masha Allah … “

Ma’aikata ne suka shiga kawo abubuwan motsa baki. Da lemuka da ruwan roba kala kala.

Su kayita tururuwar shigowa suna gayshe da ummimin. Cikin haka Haj Hameedah ta shiga sashen itama. Sanye cikin laffaya baqa mai kwalliyar pink

Ta tsugunna har kasa ta gayshe da ummimin. Ummimi ta amsa da fara’a lullube a fuskarta

Ta juya ta gayshe da Barr Aisha. Itama ta gayshe da ita. Kafin su Ahlam su gayshe da ita.

A kallo na farko Waheedah ta gano itace mahaifiyar Nadra. Saboda tsananin yadda suke kama.

“Maa ga Waheedan.”

Suka hada idanu da ita. Ta saki tattausar murmushi .

“Sannu Waheedah. Ina Hadizan, Fatan dai komai lapia?”

“Alhamdulillah…. Eh batada lapia ne.”

“SubhanAllah! Meya same ta?”

“Zazzabi take da amai.”

“Wayyo. Allah bata lapia yasa kaffarane. “

“Aamin Yaa rabbi.”

“Ummimi me zaa dafa muku?”

“Ko meye ma Hameedah.”

“Toh . Bari na je.”

“Sannu da kokari.”

Fita hajiya Hameedan tayi. Nadra da Waheedah suka bi bayanta.

A kan hanyar su ta komawa sashenta ta sake cewa da Waheedah,

“Amma an kaita asibiti ko?”

“Na baro su dai me kyamis ze duba ta”

“To Allah bada lapia. Tun safe nake jiranta. Naji shiru. Na dauka ma ko tazo masu gidah basu bari ta shigo ba saboda baqin da za’ayi. Nasa Nadra taje ta dubo. Allah sarki hadiza ashe batada lapia “

“Eh …”

“Tohm shigo ciki.”

Waheedah ta shiga cikin parlorn tana raba idanu. Lalle dukiya tayi kuka. Idanunta suka sauka akan wata jirgegiyar tv da sauran kayan kallo

“Zauna mana Waheedah.”

Waheedan ta dan tsakure akasan kujera kafin tace,

“Ance a nunnunamun abubuwan da zan yi kafin Umman ta mu ta samu sauki “

“To Waheedah ba matsala . Zo ki ga “

Haj Hameedan tayi gaba. Yayin da waheedan ke biye da ita. Ta nunnuna mata komai da yadda zatai amfani da su.

“Kinga abincin ta ma…” Ta nuna mata wata food flask katuwa. Kamshi sai tashi yake daga cikin ta.

“Allah sarki …..”

“Zaki iya kai mata ki dawo?”

“Toh ko zan kammala aiyukan?”

“A’a kai mata dai. Akwai kunu ma gashi can tunda zafin su ta samu ta ci.”

“Tohm..”

“Yauwa Waheedah “

A cikin wani kwando ta jera mata kayan abincin kai kace wata babbar bakuwa zaa kai wa.

“Rike dakyau.”

“Angode Allah ya saka da alkhairi Hajia…”

“Aamin Waheedah, Ki cemun Maa haka su Nadra ke kirana kinji ko?”

“Tohm …Maa”

“Yauwa Waheedah. “

Daukar kwandon tayi cikin nutsuwa ta fita zuwa gate din. Ta ajiye a kasa ta bude gate din sannan ta dauka ta fice.

Kamshin soyayyan nama da na tafarnuwa na ta dukan hancin ta a haka ta karasa gidah

Bakinta dauke da sallama ta shiga cikin gidan.., Marka na zaune akan turmi tana tsintar shinkafa. Ta hararo kwandon dake hannun Waheedah tana tabe baki.

Waheedan ta shige da kwandon cikin dakin su. Umma Hadiza na kwance akan katifa. Yayin da dayan hannunta kuma daure yake da abun karin ruwa. Har ya kare wanda aka saka matan kafin me kyamis din ya koma anjima.

“Sannu Umma…”

“Yauwa Waheedah. Ya kika dawo?”

“Ca tai nayi sauri na kawo miki abinci. Nace ta bari ma na kammala aikin tace a’ah ..”

“Allah sarki Hajia … Mungode Allah ya saka da alkhairi.”

“Aamin Yaa rabbi. Ki tashi ki sha kunun da abincin.”

“Dakko kofi da kwano ki zubawa Marka “

Waheedah ta turo baki gaba.

“Umma da dai kin fara ci.”

“Je ki dakko na ce .”

“Toh.”

Da sauri ta dakko kwano da kofi wankakku ta ajiye.

“Zuba mata kunun ki zuba mata abincin a plate.”

“Tohm.”

Ta zuba kunun a kofi dake tashin kamshin gyada da kayan kamshi. Ta bude food flask din.

Kwai ne da dankali da soyayyan nama a gefe.

Ta zuba komai a farantin zata miqe Umma Hadiza ta ce,

“Kara mata waheedah..”

Waheedah ta sake karawa. Ta nunawa Umma Hadizan sannan tace yayi.

Ta fita ta kai wa Marka

“Gashi inji Umma. Daga gidan aikinta aka bata”

Marka ta yamutsa fuska hadi da wulqita idanu ta hango lafceciyar wainar kwai da dankali da nama. Ga kunu kuma.

“Sai da aka ci aka cinye.? Kalli dan abunda aka sammun. Aikin kawai ” Ta wafta jikinta har yana rawa……

❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button