FARHATAL-QALB 22
PG:22
=====
Waheedah bata ce wa Marka kanzil ba ta koma daki abunta
“Ki tashi kici Umma.”
“Dibi kici Waheedah. Ki raba mu ku da su Yayan ki da Najan Isubu. Don sai yanzu ta tafi gidah yo wanka. Zata dawo “
“Allah sarki aunty Naja. Allah yabar zumunci.”
Nan da nan kuwa ta fara dibarwa Umman tasu nata. Sannan ta raba musu nasu.
“Umma ki tashi ki ci “
“Banajin yunwa ..”
“Dan Allah Umma “
Umma Hadiza ta daure ta tashi daga kwanciyar da take. Taja plate din gabanta tana ci tana hadawa da kunun. Hakama Waheedah da kunnuwanta sai motsawa suke don dadi.
“Gaskia abincin nan yay dadi “
“Ai Hajia ta iya girkuna.”
“Sunada kirki Ummaa. Ban baki labari ba. Da naje fa hanani shiga masu gidan su kayi daga farko “
“To pha SubhanAllah… Baki ce musu ni mahaifiyar ki bace?”
“Kwata kwata sun hanani. Saboda wai baqin da za suyi. Ina zuwa kuma bakin na zuwa su ma. A wasu manyan motoci.”
“Lalle bakin na karramawa ne. To waya shiga da ke kenan?”
“Wata Nadra .”
“Okay Nadra . Yar Haj Hameedan ce ai.”
“Eh na sa ni., Wai itace ma ta aikota wajen ko kinzo sun hana ki shiga. Tana zuwa ta ganni sai tai musu bayani suka kyaleni na shiga.”
“Allah sarki “
“Gaskia sunada kirki Umma. Baki ga yadda suka mun ba gaba dayan su. Kamar irin tun da can dinnan sun sanni.”
“Allah sarki su Hajiya. Akwai karamci
“Wadda tazo din ina kyautata zatom mahaifiyar mai gidan ce. Wata dattjuwa wai Ummimi “
“Tabbas naji sunan nan Hajia na fada.”
“Eh tazo da maaikatan ta da wata budurwa . Tace mun sunanta Ahlam.”
“Allah sarki. Allah ya saka musu da alkhairi.”
“Wallahi sun burgeni sosai wallahi.. Ba ruwan dukkan su. Har sashen dayar matar mu kaje.”
“To pha meya kai ku?”
“Anan tsohuwar ta sauka. Don naga Maa ma na tambayarta abincin da zaa dafa mata.”
“Allah sarki baiwar Allah.”
“Yauwa ni na manta ma ban gaya miki ba.”
“Meya faru.?”
“Tace wai na dinga kiran ta da Maa”
“Allah sarki Haj Hameedah … “
Waheedah ta gama bata labarin komai tsaf. Sannan ta kuskure bakinta ta mayar da hijabinta ta koma gidan aikin Umman su na The Adams family.
Tana zuwa ta shige ciki ba tare da masu gadi sun sake hanata ba
“Kin dawo Waheedah.?”
“Eh na dawo Maa “
“Masha Allah. To ya jikin Hadizan?”
“Ah da sauki . Na baro ta ma tana cin abincin. An gama sa mata ruwa.”
“Oh Allah sarki Hadiza , Har da karin ruwa.?”
“Eh.”
“To Allah bata lapia. Yasa kaffarane Amin.”
“Amin , Bari na dauraye kayan “
“Tom Waheedah.”
Nan da nan ta hada ruwan kumfa ta wanke kananan kayan ciki da safuna (socks) na Moha .
Ta dauraye ta shanye. Ta goggoge ko ina tamkar yadda suka koya mata. Sannan ta wanke mopping sticks din da dusters.
“Ah sannu Waheedah. Kina da saurin aiki irin na Hadiza. Masha Allah.”
Dan murmushi Waheedah ta yi. Tana mai lankwasa yatsun hannuwan ta .
“Allah miki albarka.”
“Aamin Maa.”
“Zauna ki huta. Ga abinci nan ki ci kafin a kammala na rana.”
“Wallahi na koshi Maa. Ai na ci na wajen Umma. “
“To kya sake ci anjima.”
“Tohm..”
Can wajajen 12 da rabi Moha ya dawo daga makaranta.
Da gudu ya rungume mahaifiyar ta su yana tsalle.
“My little sun shine.”
“Maaaa.”
“A zubo abinci.”
“Wannan wacece?” Ya tambaya yana nuna yatsansa akan Waheedah .
“Sunan ta Yaya Waheedah ….. “
“Yaya Waneeda.”
“No Yaya wa… Hee… Dah.”
“Okay Yaya Waheedah.”
“Ya sunan ka?” Waheedah ta tanbaye shi tana murmushi.
“Sunana Moha. “
“Sunan sa Muhammad. Muna kiran sa da Moha.”
“Allah sarki . Ajin ka nawa?”
“Maa what’s Aji in english.?”
“Class/grade”
“Oh! I’m in grade one . “
“Masha Allah …”
“Ke fa?”
“Ni ss2 zan shiga.”
“Okay .. “
Haj Hameedah ta miqe ta nufi babban kitchen din sashenta inda maaikatan ke girki. Ta dudduba kan abubuwan ta koma dayan kitchen din dake parlorn inda take gashi.
Waheedah ta miqe tabi bayanta .
“Maa akwai abunda zaa tayaki?”
“Babu komai Waheedah. Dama gashi ne nake yi anan din. Can babban kitchen din maaikata na abinci. “
“Okay. Sannu da kokari.”
Haj Hameedah ta zura safar girki tana dudduba kayan hadin jikin naman kajin.
“Wannan gashi ne.?”
“Eh nayi marinating ne da kayan hadi. Se gasawa kawai.”
Waheedah ta kada kai .
“Kin iya girkuna?”
Ta dan yi murmushi kafin ta ce,
“Bakomai ba. Na de fi iya wasu abubuwan . “
“Ah inde kin iya girki ai da sauki. Allah ya temaka. Kai temake ni. Kinsan na manta da tafarnuwa “
“Wai.”
“Yi sauri ki dubamun cikin freezer dinnan daga kasa zaki ga tafarnuwar a wani canister.”
“Tohm”
Nan da nan Waheedah ta duba ta dakko ta miqa mata. Tafarnuwar a dake take. Haj Hameedah ta diba ta zuba acikin gashin tana cakudawa .
Waheedah ta dauki wasu canisters din na spices tana dubawa. Sai kamshin abincin larabawa suke . Haj Hameedah ta janyo abun grilling din tana dudduba shi. Kafin ta sauke kallonta akan Waheedah. Cikin murmushi tace da ita,
“spices/seasonings ne na larabawa ..” Ta shiga daukar kowanne dai dai tana gaya mata sunayen su,
“Wannan Sadaf mint leaves ne, Wannan, Natural sidr leave sai, Pure black seed ( Black cumin seed), Ga Nutmeg, sai cardamom, Wannan sumac, Sai hulba , Fenugreek ,Allspice
Cloves, Ginger…”
“Masha Allah…..Gaskia suna da kamshi Maa.”
“Sai ma a abinci…”
“Gaskia daga jin kamshin su ma ” Ta dauki duster ta shiga goge kitchen cabinets din. Duk kuwa da ba datti suka yi ba .
×××××
A gajiye yake likis saboda gaba daya jiya bai yi wani baccin kirki ba kuma tun kafin asubah bai sake runtsawa ba ya fita. Dawowar sa kenan cargos din kayan su sun sauka a site yaje ya dubo.
Sanye yake cikin manyan kaya. Riga da wando na shadda. Rigar iya gwiwa sai wando. Kalar dark blue. Hular kalar kayan sa ta zanna bukar na hannun sa. Yayinda half covered shoe dinsa da agogon hannun sa kalar aikin kayan sa ne.
Sai kamshin turaren Calvin Klein ne da Rasasi suke tashi a jikin sa.
Yana sallama tun daga bakin kofar kitchen ya samu zuciyar sa da sauya bugu . Bugun mai duka da sauri sauri.
Kamshin turaren da bazai taba mantawa ba ya shiga yawo sosai a kofofin hancin sa.
Ya lumshe idanu ya bude. Ahankali ya saka hannu ya tura kofar kitchen din ya shiga…….
❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????