Allon Sihiri 6HAUSA NOVEL

Allon Sihiri 6

Labari ya isowa guyson cewa.
JARUMAR TA MIKE TSAYE DAGA KAN KARAGAR
MULKIN, ta tako kafafunta tazo har daf da
alkasim ta tsugunna fuskarrta na kallon tasa
yadda har suna iya jin numfashin juna sannan ta
dubeshi fuskarta a daure tace wnene kai kuma
me kake takama dashi har da zakayi kokarin
zaluntata ka rabani da abinda na farauto a daji
alhalin hannuna ya riga naka kaiwa kan dabbar?
Sa adda yarima alkasim yaji wannan tambaya sai
yayi murmushi yace bazan baki amsar wannan
tambaya ba sai kin fara gabatar da kanki tukunna
nasan ko ke wacece.
Koda jin haka sai jarumar ta fusata ta mike tsaye
zumbur ta koma da sauri zuwa kan karagarta ta
zauna zamanta keda wuya sai ta yi nuni da
hannunta zuwa kan alkasim take wannan
murtukekiyar macijiya data kanannadeshi ta
sauka daga jikinsa amma sai wadansu sarkokin
karfe suka fito daka cikin bango kimanin guda
dubu suka kanannadeshi har kansa suka janyeshi
zuwa jikin bangon suka shiga matseshi
yarima alkasim bai san sa adda ya fara kurma
ihu da kururuwa ba sakamakon tsananin zafi da
zugin da yake ji
koda ganin haka sai jarumar ta fara kyalkyala
dariyar mugunta tana cikin yin dariyar ne
kwatsam taji alkasim ya daina yin ihu da
kururuwan kuma nan take sarkokin suka karkatse
suka zube kasa gutsungutsun sai gani tayi
Alkasim ya baro jikin bangon ya durfafota yana
tafiya da karfinsa tamkar wani abu bai taba
samunsa ba
Manya gatan wasa kenan sarki Alkasim.
Cikin tsananin kaduwa da mamaki jarumar ta
mike tsaye tana kallonsa kawai alkasim ya iso
har daf da ita yadda suna iya jin numfashin juna
kamar yadda tayi masa dazu ya dubeta cikin
murmushi yace
duk abinda kike takama dashi nima ina da irinsa
ko ma wanda ya fishi akan wane dalili zaki dauki
girman kai a gareni alhalin nine yakamata na
zamo mai girman kai a gareki tun da na kasance
da ga sarkin dake mulkin wannan kasa da kike
cikinta.
Koda jin wannan batu sai jarumar tayi murmushi
sannan tace dama saboda kai nazo wannan kasa
abinda yasa banje fada kai tsaye ba shine ina son
na gabatar da abinda nazo yi a sirrance ya
kasance a tsakaninmu ne kawai mu biyu
sunana LUSLAIYA YA GA SARKIN MAFARAUTA NA
BIRNIN TEHERAN tun ban fi shekara takwas ba a
duniya mahaifina ya bani horon yaki wanda ina
iya fuskantar zaratan mayaka guda dubu sannan
ya bani horon gumurzu da manyan dabbobin daji
baya ga hakan ya bani horon rayuwa a cikin daji
gami da yin gudu na tsawon kwanaki tara ba tare
da tsayawa ba sama da dakika arba in ba
bugu da kari mahaifina ya tsumani a cikin tsumin
tsafi irin wanda samun mai irinsa sai an tona
lokacinda na samu shekaru goma sha takwas ina
samun wannan horo ya zamana cewa na zama
budurwa cikakkiya sai na kawai da dukkan yan
fashin dake cikin dazuzzukan kasarmu ni kadai
hakanne yasa yan fashin suka fusata suka nemo
taimakon yan uwansu dake cikin kasashen ketare
amma duk da hakan sai na zame musu alakakai
na zamo tamkar shaidaniya a cikin bil adama
akwai wata ranar da wadannnan yan fashi suka
ritsani a daji adadinsu yakai miliyan shida amma
ni kadai na kashe mutum miliyan uku da rabi
daga cikinsu sauran suka tsere daga wannan
rana ne na dinga jin kamar babu wani mayaki ko
sadaukin da yafi ni jarumtaka amma sai
mahaifina ya dubeni yace yake yata kada ki
kuskura ki dorawa kanki girman kai bisa wannan
jarumtaka da kika ga kin samu
a halin yanzu ina mai tabbatar miki da cewa
akwai wani dan sarki wanda karfinsa da
jarumtakarsa har da karfin sihirinsa zasu iya
zuwa dai dai da naki koma yafiki
koda jin wannan batu saina kamu da tsananin
mamaki na tuna irin karfiin da nake dashi amma
ace wai har akwai wanda ya kaini koma ya fini
bisa wannan daliline na yanke hukuncin nazo na
hadu dakai domin muyi gasa guda mu banbance
tsakanin aya da tsakuwa gasa ta farko itace
gudun tseren da zamuyi tsawon kwana tara ba
tare da tsayawa ba ta sama da dakika arba in ba
gasa ta biyu itace akwai wani babban gari na
arnan daji dake can kudancinmu na taheran ina
son mu je mu sato gunkin da suke bautawa
domin mu tsokano yaki dasu
wadannan arnan daji suna da mugun yawanda ba
asan iyakar adadinsuba ni dakai dai zamu yakesu
domin mu tantance iyakar jarumtakarmu
gasa ta uku wacce itace ta karshe zamu shiga
daji kowannanmu yayi farautar dabbar da babu
kamarta ya kasheta yazo da gawarta idan har
dabbar da na kashe tafi taka hadari ka tabbata
cewa nafika karfi da jarumtaka kenan
Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan
daga zauran labarai page nake typing
nan take zamu rabu na koma kasata cikin farin
cikin cewa nafi ka komai
yayinda jaruma luslaiiya tazo nan a zancenta sai
hankalin alkasim ya dugunzuma ainun saboda
zuciyarsa ta karaya akan wannan abu guda uku
amma daya tuna cewa shifa mutum ne mai sa a
da nasara bisa duk abinda yasa a gabansa sai
yaji dukkan tsoro ya kau
daga cikin ransa don haka bai san sa adda ya
dubi jaruma luslaiya ba yace na yarda da duk
wannan sharadi na gasar da kika shirya mana
kuma saina tabbatar miki da cewa nafiki karfi da
jarum taka
wow nima Guyson saina tabbatar muku da cewa
jarumi ne ni.
Yanzu idan na lashe wannan gasa menene
sakamakona?
Koda jin wannan tambaya sai mamaki ya kama
luslaiya tace inda dai ace kai ba dan sarki bane
toda saina baka dukiyar da har ka mutu kai da
danginka ba zaka yi talauci ba
amma ai mahaifinka yafi mahaifina dukiya yanzu
ban san dame zan iya biyanka ba
koda jin wannan batu sai alkasim yayi murmushi
yace ai kuwa kece kike da abin da zaki iya biyana
yake jarumar jarumai kuma tauraruwar taurari ba
komai nake so a wajanki ba face soyayyarki da
aurenki idan har na lashe wannan gasa akanki to
na siyi soyayyata kenan kuma babu abinda zai
hana aurenmu
koda jin wannan batu sai jaruma luslaiya taji
zuciyarta tayi baki kirin kuma nan take taji ta
tsani yarima alkasim fiye da komai a duniya
saboda tunanin cewa ya na so yayi mata dole ta
soshi kuma ta aureshi
cikin tsananin fushi ta dubeshi tace nayi maka
alkawari zaka sha bakar wahala da baka taba sha
ba a rayuwarka a cikin wannan gasa wacce zata
kaika ga rasa lafiyarka ko rayuwarka gaba daya
kuma ina tabbatar maka da cewa baka da
jarumtakar da zata iya burgeni har zuciyata ta
kamu da sonka don haka duk yadda zanyi naga
ka fadi wannan gasa sai nayi ya kasance ne ne
na lashe gasar
ka sani cewa babu hada kai a cikin wannan gasa
ni dakai sai dai kowa tasa ta fishsheshi kuma
kowannanmu zai iya shiryawa dan uwansa tarkon
mugunta domin ya hallaka
iana son mu zamo tamkar abokan gaba masu
farautar rayukan juna
lokacin da sarki alkasim yazo dai dai nan a
labarin da yake baiwa yarima kamsus sai yaga
idanun yarima sun ciko da kwalla kuma
hankalinsa ya dugunzuma ainun ya tari
numfashinsa yaana mai cewa daka ta yakai
abbana yanzu kana bani labarin wata jaruma a
matsayin itace mahaifiyata to ita kuma junaina
wadda na taso nake ganinta a matsayin uwata
wacece ita??
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
sarki Alkasim yayi shiru kamar ba zaice komai ba
daga can ya dago kai ya dubeshi cikin rawar
murya yace yakai dana kayi hakuri zakaji
amsawar wannan tambaya da kayi min a karshen
wannan labari da nake baka kafin mu isa birnin
masarul anjana
Tabbas zaka tantance a tsakanin mahaifiyarka
junaina da kuma mahaifiyarka jaruma luslaiya
zaka san matsayin kowacce a wajenka
koda sarki alkasim yazo nan a zancensa sai
zuciyarsa ta karaya ya fashe da matsanancin
kuka al amarin da ya dugunzuma hankalin yarima
kamsus kenan ya shiga rarrashin sarki a lokacin
da yaji ya kamu da tsananin tausayin mahaifin
nasa sarki Alkasim
da kyar ya shawo kansa ya daina kukan sannan
yarima kamsus ya dubeshi cikin zakuwa yace na
rokeka dakaci gaba da bani wannan labari domin
naji yadda karshen gasarku da jaruma luslaiya
zata kasance sannan kuna na gane banbancin
dake tsakanin luslaiya da mahaifiyata junaina
Al amin Ahmed Dan misau
Guyson sunana kenan
daga zauran labarai nake magana
tayaya zan karbi luslaiya a matsayin uwa ta
alhalin ban san wata uwa ba face junaina
gama fadin haka keda wuya sai hawaye ya
kwararo bisa kumatun yarima kamsus take shima
sarki alkasim yaji ya kamu da matukar
tausayinsa don haka sai ya rungumeshi akan
kirjinsa sannan yaci gaba da bashi labari yana
mai cewa…..
.
LOKACIN DA NAJI ABINDA LUSLAIYA ta fadi
cewar a cikin wannan gasa zamu zamo tamkar
abokan gaba kuma zamu rinka shiryawa juna
tarkon muguntar da zan iya hallaka sai hankalina
ya tashi saboda dalilai guda biyu.
Dalili na farko shine na kamu da tsananin sonta
dalilina biyu kuwa bazan iya shirya mata
mugunta da zata hallaka ba nan take zuciyata ta
gamsu cewar lallai zan sha bakar wahala a cikin
wannan gasa musamman da na tuna cewa inda
zamu je mu gabatar da wannan gasa acanne
nahiyar su jaruma luslaiya don haka ban san
sirrikan dazuzzukan dake can ba.
Yayin da luslaiya taga na sunkuyar da kaina kasa
ina tunani da nazari saita kyalkyale da dariyar
mugunta sannan ta hade fuska tace yaro bai san
wuta ba saiya taka ta yanzu saika tashi ka koma
gida ka sanar da iyayenka duk abinda ya faru a
tsakaninmu domin kayi musu sallama ka dawo
mu tafi ka sani cewa tun daga nan gasar mu
zata fara don haka kayi amfani da damarka ta
kowa a gidansa sarkine
duk yadda zakayi ka tabbatar kaga bayana kafin
mu bar nahiyarku
dajin wannan batu sai yarima Alkasim yayi
murmushi ya mike tsaye ya juya mata baya har
yayi taku uku gaba zai yi tafiyarsa sai ta kira
sunansa ya waigo ya dubeta cikin mamaki
ita kuma sai tace da sassafe zaka fito gobe ka
sameni anan wurin idan ka baata min lokacin
zanyi tafiyata sai kayi da gaske zaka riskeni
alkasim yayi murmushi yace babu matsala zanzo
akan lokaci
yana gama fadin hakan sai ya juya yayi tafiyarsa
har yarima alkasim ya isa gida jikinsa a sanyaye
yake kuma hankalinsa a tashe yake domin
guiwarsa tayi sanyi ainun bisa wannan
gagarumar gasa dake gabansa
da isar yarima Alkasim a lokacin da magariba ta
gabato sai ya nufi kai
Tsaye bisa mamaki sai ya hango kofar dakinsa a
bude al amarin da yayi matukar bashi mamaki
kenan domin babu wanda yake da ikon shiga
dakinsa ba tare da izininsa ba face mutum biyu
daga sarki sai mahaifiyarsa
a fusace yarima Alkasim ya kunna kai da sauri
cikin turakar tasa da nufin yaci mutuncin wanda
ya bude ya shiga koda yayi arba da wanda ke
zaune a cikin dakin sai zuciyarsa ta buga da karfi
ba wani bane ba face mahaifiyarsa tana zaune
bisa shimfidarsa kanta a sunkuye hawaye na diga
daga idanunta cikin firgici ya karasa gareta da
sauri ya durkusa a gabanta
ya rike hannayanta biyu yana dubanta cikin
tsananin damuwa yace yake ummina ina dalilin
zubar wannan hawaye daga cikin idanunki sa
adda taji wannan tambaya sai tasa hannunta na
dama ta share hawayan nata sannan ta janyo
yarima izuwa jikinta ta rungumeshi akan kirjinta
tace
ya kai dana yau shekara talatin da kadan kenan
ina tare dakai bamu taba rabuwa ba amma yau
sarki ya tabbatar min da cewa a wannan karon
zaka nisanta dani kuma zaka yi wata tafiya mai
hadari wacce zama ka iya rasa rayuwarka
koda jin haka sai yarima alkasim yayi murmushi
cikin nutsuwa yace haba yake ummina akan wane
dalili zaki damu kanki alhalin kin san duk ahalin
gidan nan yana da sa a da nasara bisa duk
abinda yasa a gabansa ke da bakinki kin sha bani
labarin irin
gwagwarmayar da sarki yayi a rayuwarsa tamkar
ba zai tsira da rayuwarsa ba
wai shin ma me yasa kika shigo cikin turakata
kika zauna kina ta kuka? Shin yanzu kina nufin ki
ce dake za ayi wannan muguwar tafiya ne?
Nayi murna da ganinki a yanzu domin dama
akwai wani abu daya shige min duhu ina son kiyi
min cikakken bayani kada ki boye min komai
taji zuciyarta ta buga da karfi tsoro ya shigeta ta
fara zargin anya kuwa sarki bai sanar dani sirrin
da suka boye ba tsawon shekaru cikin karfin hali
na budi baki nace
yake umma ina sonki sanar dani matsayina
kafin yarima alkasim ya karasa fadin abin dake
bakinsa sai yaji motsi a bayansa don haka sai ya
waigo da sauri
sarkine tsaye a bayansa fuskarsa a murtuke yana
mai kada kansa wato yana yi masa nuni da kada
ya fada mata abindake bakinsa….

1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button